Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Babu Abin Alkhairin Da Tinubu Zai Iya Yi Kafin 2027 – Salihu Lukman

Tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Salihu Lukman, ya bayyana cewa ya daina sa ran Shugaba Bola Tinubu zai kawo wani canji mai ma’ana a Najeriya kafin shekarar 2027.

Lukman ya bayyana haka ne yayin wata hira a shirin Inside Sources da Laolu Akande ke gabatarwa a Channels TV, inda ya ce yadda Tinubu ke tafiyar da Najeriya ya sha bamban da irin yadda ya mulki Legas daga 1999 zuwa 2007.

Ya ce duk wanda ke sa ran wani babban sauyi kafin 2027 yana mafarki ne kawai, kuma idan har aka samu to ya zama babban abun mamaki.

Lukman ya kara da cewa ya daina goyon bayan Tinubu tun watan Yulin bara, bayan da ya fahimci cewa shugaban ya keɓe kansa daga jama’a har ma da ƴan jam’iyyar sa.

Ya ce tsammanin da ya yi cewa Tinubu zai gyara kurakuran Buhari ya gagara, maimakon haka yana ganin yadda abubuwa ke tafiya yanzu, yana jin Buhari alheri ga Najeriya.

A cewarsa, ana aikin kafa wata sabuwar haɗin gwiwar siyasa mai ƙarfi wanda zata tabbatar da cewa irin gazawar da aka yi a APC ba za ta sake faruwa ba.

Lukman ya roki Allah ya ba su ƙarfi da ƙarfin hali su tashi tsaye domin gyara Najeriya a lokacin rayuwarsu.