Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

BAIWA MATA TALLAFI A JIGAWA: Da Muguwar Rawa Gwamma Ƙin Tashi, Shawara ga Gwamna Namadi

Daga: Ahmed Ilallah

Kamar yanda labari ya bayyana a zaman Majalissar Zartarwar Jihar Jigawa na farko, a kwai sanarwar ƙudurin wannan gwamnati na bayar da tallafi ga mata dubu daya (1000) don rage raɗaɗin talauci da matsin rayuwar da yake damun wannan ƙasa.

Abin hanzari ba gudu ba, game da wannan lamari shine, ya kamata mu faɗa wa kanmu gaskiya, duk wani ala’amari da ya shafi al’ummah masu ɗunbun yawa shirya shi ake yi, tsakurar kaɗan daga ciki yamutsa hazo ne, amma in har aka gaza samun kyakkyawan tsari  na aiwatarwa, to fa za a gwammaci kiɗa da karatu. Wannan aniya ce mai kyau, amma cike da ƙalubale. Jihar Jigawa da ta ke da ƙiyasin sama da mutane miliyan shida (6 million), wanda kaso arbai’in da tara na yawan mutanenta mata ne (49% are Female), kuma akasari suna zaune ne a karkara, a cikin wannan kaso sama da kashi tamanin (80%) na waɗannan matan suna fama da talauci mummuna.

Ƙarfin Talauci A Jigawa (Tunatarwa)

Tun kafin zuwan cire tallafin man-fetur, daman can talauci a Jigawa yana da ƙarfi. A cikin bayanan ƙiddigar talauci a Nijeriya, Jihar Jigawa tana daga cikin Jihohi guda shida (6), masu ƙarfin talauci, har ma ana tantamar, cewa ko ita ce tafi ma sauran. A wannan yanayi fa mata ne suka fi galabaita, sanadiyar wannan talaucin.

Jihohin Jigawa, Sokoto, Bayelsa, Kebbi, Gombe da Yobe ne suka fi kowacce jiha talauci a Najeriya kamar yanda ƙididdigar talauci ta Nigeria Multidimensional Poverty Index 2022 ta nuna. A cikin waɗannan jihohi kuma ba a da tabbacin wacce ce ta fi wacce talaucin – ba abin mamaki ba ne Jigawa ta kasance ta fi.

Daɗi da ƙari a kan ƙarfin talauci a Jigawa har ila yau, lissafin ƙiddigar talaucin ya nuna cewa a mazaɓun ‘Ƴan Majalissar Dattijai na Nijeriya (Senatorial Districts) guda goma da suka fi saura ƙarfin talauci a Najeriya, guda biyu sun fito ne da ga Jihar Jigawa waɗanda suka haɗa da Mazaɓar Sanatan Jigawa ta Arewa maso Yamma da Mazaɓar Sanatan Jigawa ta Arewa maso Gabas. A waɗannan mazaɓu guda biyu, ƙididdigar ta nuna cewa, yaran da ke cikinsu ƴan ƙasa da shekaru 5 kaso 91% zuwa 99% nasu suna cikin matsanancin talauci. Wannan kuma kai tsaye na nuni da yanayin da matan yankin suke ciki ne.

Wannan fa kaɗan ne daga yanayin da al’ummar Jigawa musamman ma mata suke ciki, gashi kuma cire tallafin man-fetur ya ƙara gishiri a kan ciwon.

Mata 1000 Da Gudunmawar Mata A Jigawa

Warewa mata 1000 kacal don ba su tallafi, ba ƙaramar ƙura zai tayar ba, a fahimtar gwamantin nan, sannan ka iya yamutsa hazo a tsakanin miliyoyin matan da suke ƙaunar wannan gwamnati.

A nazarin da nayi a kan “MATA DA SIYASA A JIGAWA”. Na sa ido da jagorantar wani aiki a lokacin da Jamai’iyar APC ta ke sabunta rijistar mambobinta, a cikin mazaɓun kansiloli ɗari biyu da tamanin da bakwai (287 Political Wards), babu mazaɓar da mata sama da ɗari tara (900) ba su yanki katin zama ƴan jama’iyar APC ba.

Har ila yau, a cikin ƙananan hukumomin Jigawa ashirin da bakwai (27), na halarci yaƙin neman zaɓe tare da Maigirma Gwamna a ƙananan hukumomi ashirin da biyar (25), kowa ya san a duk inda a ka gewaya a waɗannan ƙananan hukumomi, dubban mata suke fitowa don taya yaƙin neman zaɓen.

A nawa hangen kusan dukkanin waɗannan matan, babu wanda ba ta cikin masu buƙatar a taimaka musu.

Shawara A Kan Mata Dubu

Ina bawa wannan gwamnati mai girma da Maigirma Gwamna, a kan sake duba a kan wannan ƙudiri, saboda muhimmancinsa da kuma dacewarsa a wannan lokacin da a ke ciki.Ya kamata gwamnati ta yi komai a shirye, domin a kowace ƙaramar hukuma ma, a ƙalla ya kamata a ce an taimakawa mata sama da dubu ɗaya, ganin yawan su a yau ya kai miliyoyi, ga kuma gudunmawar da suke bawa wannan gwamnati, da ma burinsu a kan wannan gwamnati.

Duk abin da ba za a ƙare shi da kyau ba, ya kamata a sake duba shi kafin aiwatar da shi, mulkin siyasa a keyi, fahimta ba ɗaya ba ce, zato ma haka ba ɗaya ba ne. Yana da kyau duk wani tsari da zai shigo cikin al’umma ya zamanto mai kyakkyawar tsari da zai samu gamsuwa ga dukkanin mutane. Bahaushe dai ya ce, da muguwar rawa gwamma ƙin tashi.

alhajilallah@gmail.com

Malam Umar Namadi, Gwamnan Jihar Jigawa