
Sarkin Ningi, Alhaji Haruna Yunusa Danyaya III, ya ƙaddamar da dashen bishiyoyi miliyan ɗaya a Jimi, Ningi, Bauchi.
An yi aikin ne tare da Green Legacy Foundation ƙarƙashin jagorancin Magajin Garin Kano, inda aka raba shuke-shuke ga al’umma.
Sarkin ya ce wannan “babban mataki ne na tarihi wajen yaƙar matsalar hamadar Sahara,” yana gode wa masu ɗaukar nauyin shirin.
Ya umarci hakimai, dagatai da masu unguwanni su kula da shuke-shuken “don su tsira su zama gado ga ƴaƴanmu,” in ji shi.
Shugaban ƙaramar hukumar Ningi, Nasiru Zakarai, ya ce gwamnati za ta “kare muhalli daga sare daji da samar da gawayi.”
Wakilin Masarautar Kano, Dr Aminu Wada Fanda, ya bayyana cewa an yi irin wannan aiki a ƙananan hukumomi 18 na Kano, yana mai cewa “mu na tsayawa tsayin daka kan yaƙi da hamada.”
Shugaban Warji, Aminu Barmini, ya buƙaci a biya masu aikin sa kai kan kula da bishiyoyin, yayin da Alhaji Muhammad Kilishi Musa ya gode wa masarautu kan jagorancin da suke.