Rundunar ƴansanda a Jihar Bauchi ta tabbatar da tsare wasu jami’anta guda uku da ake zargi da hannu a mutuwar wani wanda ake zargi, Abubakar Auwal, wanda ya rasu a hannun ƴansanda a hedikwatar rundunar yankin Jega.
Auwal, wanda aka kama bisa zargin satar tayoyin babbar mota, ya rasu ne a safiyar ranar 16 ga watan Afrilu, bayan da ya faɗi a cikin cell na ƴansanda, kamar yadda kakakin rundunar, SP Nafiu Abubakar, ya bayyana.
An garzaya da shi asibitin gwamnati da ke Jega, inda aka tabbatar da rasuwarsa da misalin ƙarfe 10 na dare.
WANI LABARIN: Wasu Jigajigan PDP Na Zargin Atiku Da Dagula Lamuran Jam’iyyar
Rundunar ta ce Kwamishinan ƴansanda na jihar, Bello Sani, ya umurci sashin binciken manyan laifuka na jihar (CID) da su gudanar da bincike mai zurfi kan lamarin.
“Binciken farko ya nuna cewa wasu jami’ai uku na da alaƙa da mutuwar, kuma tuni aka tsare su, yayin da DPO na yankin ya samu takardar tuhuma tare da sauya masa wurin aiki,” in ji sanarwar.
Rundunar ba ta bayyana sunayen jami’an da ake zargi ba, amma ta ce ana ci gaba da bincike.
Rundunar ƴansandan ta jaddada cewa tana da niyyar ci gaba da gudanar da aikinta bisa ƙa’idoji da mutunta haƙƙin ɗan’adam.