Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Buhari Ya Dawo Abuja Bayan Kwashe Kwanaki 8 A Saudiyya

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dawo Abuja bayan ziyarar kwanaki 8 a kasar Saudiyya, inda ya kuma gabatar da aikin Umara.

Shugaban na Najeriya ya bar Filin Jirgin King Abdulaziz da ke Jiddah a kasar Saudiyya a yau Laraba.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya rawaito cewa, Jami’an Gwamnatin Saudiyya, sarakuna da malaman addini daga Najeriya da kuma manyan ma’aikatan ofishin jakadancin Najeriya na Saudiyya sun kasance a filin jirgin a lokacin da shugaban zai taso.

Shugaban Kasar ya samu damar gudanar aikin Umarah a cikin kulawar tsaro mai tsanani a daidai lokacin da ya isa Masallacin Ka’aba daga Madinah a safiyar Alhamis din da ta gabata.

A farkon ziyarar tasa, Shugaban Kasar ya ziyarci wasu muhimman guraren tarihi a Madinah a ranar Talata da Laraba kafin ya wuce Makkah domin yin aikin Umarah.

Haka kuma an rawaito cewa, Shugaban ya karbi bayanan yanda Najeriya ke kasancewa daga bakin wasu mukarraban gwamnati da suka hada da gwamnonin Borno da Yobe.

Haka kumaa lokacin da Shugaban yana Makkah, ya karbi wasu daga cikin sarakunan gargajiya da malaman addini a shan ruwa na musamman da aka shirya.

Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero da Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero wadanda suka yi bayani a wajen shan ruwan sun bayyana cewa, kasa mai cikakken hadin kai ce kadai zata samu damar ci gaba da cimma burikanta.

Malaman addinin da ke wajen shan ruwan sun hada da,  Malam Abubakar Sulaiman, Babban Limamin Aso Rock Villa, Sheikh Al-Kanawi Alhassan Ahmed, Dr. Bashir Umar, Muhammad Kamaluddeen Lemu da Nuruddeen Danesi Asunogie.

Sauran sun hada da Ibrahim Kasuwar Magani, Prof. Shehu Galadanchi, Abdulrasheed Adiatu, Sheikh Haroun Ogbonnia Ajah da kuma Bala Lau.

Shugaban Kasar ya kuma hadu da Otaru na Auchi, Dr. Aliru Momoh, Sarkin Lafia, Justice Sidi Mamman Bage, Sarkin Bauchi, Rilwan Adamu Sulaiman, Akadiri Saliu Momoh, Abdulfatah Chimaeze Emetumah, Fatima Ijeoma Emetumah da kuma Isa Sanusi Bayero.

Shugaban ya kuma hadu da hamshakin dan kasuwar nan, Alhaji Aminu Dantata a Makkah inda ya kara jaddada ta’aziyyarsa kan rasuwar matarsa, Rabi Dantata.

NAN