Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Buratai Ya Yi Kiran A Yi Kulle A Najeriya Irin Na Lokacin Korona Don Magance Matsalar Tsaro

Tsohon Babban Hafsan Soja, Lt-Gen Tukur Buratai (retd.), ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakin kiran mutanen ƙasa baki ɗaya kamar lokacin kulle ƙasa saboda COVID-19 don magance ta’addanci, ƴan fashi da satar mutane.

A hirar da ya yi da Channels Television, Buratai ya ce, “a lokacin matsaloli na ƙasa, dole ne mu tayar da kowa ba wai sojoji kaɗai ba,” yana mai cewa ana buƙatar haɗin kai da sadaukarwa.

Ya ja hankalin gwamnati kan yawan kuɗaɗen da aka kashe wajen sanarwa, tallafi da matakan rigakafi a lokacin COVID-19 a matsayin darasi, kuma ya ce, “za mu iya kulle ƙasar domin kowa ya mayar da hankali wajen shawo kan wannan cutar ta so-called terrorists da bandits.”

Ya sake yin gargaɗin cewa rikicin zai iya ɗaukar lokaci idan ba a kafa tsayayyen tsari na dogon lokaci ba, yana mai cewa ya daɗe yana jawo hankali tun kafin ya bar muƙaminsa.

Buratai ya bayar da misali na yadda al’umma suka haɗa kai lokacin ambaliyar Maiduguri a baya, yana mai cewa irin wannan haɗin kan zai iya ƙarfafa yaƙi da rashin tsaro.

Ya jaddada cewa dole ne a haɗa da fararen hula cikin wayar da kai ta hanyar kafafen sada zumunta da wuraren taruwar al’umma, “ƴan ƙasa dole su tashi tsaye,” in ji shi.

Maganganunsa sun zo ne a daidai lokacin da Rahoton NHRC ya nuna damuwa kan ƙaruwar kisan kai da take haƙƙin rayuwa a ƙasashen Afirka.