Hukumar CAC ta gargadi masu gudanar da kasuwancin POS da ba su yi rijista ba yayin da wa’adin da aka ba su ya ƙare.
Tun a baya dai aka sanar da su wa’adin yin rijista da aka ayyana tun ranar 7 ga Yuli, 2024, kuma wa’adin ya cika a ranar Alhamis 5 ga Satumba, 2024.
A wata sanarwa da CAC ta fitar a ranar Juma’a, ta bayyana damuwarta kan rashin cika wannan umarni duk da yawan masu gudanar da kasuwancin POS da ake da su a ƙasa.
Sai dai hukumar ta yabawa waɗanda suka fara cika wannan doka, tana jinjinawa irin kyakkyawan halinsu na biyayya tare da nuna damuwa game da yawan waɗanda ba su cika wannan umarni ba.
Hukumar CAC ta bayyana cewa tana aiki tare da jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki domin kafa ingantaccen tsari na hukunta waɗanda ba su bi doka ba.
Hakan na iya haɗawa da rufe kasuwanci da kuma ɗaukar matakan shari’a masu tsauri ga waɗanda suka ƙi cika wannan doka.