Sign in
Sign in
Recover your password.
A password will be e-mailed to you.
Browsing Category
Babban Labari
NNPCL: NLC Ta Kira Zaman Gaggawa Kan Ƙarin Farashin Fetur
Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya, NLC, ta bayyana shirinta na yin zaman gaggawa dangane da karin kashi 45 cikin 100 a farashin man fetur da Kamfanin Man Fetur na Najeriya, NNPCL, ya yi kwanan nan.
Wannan na zuwa ne yayin da ƙungiyar ta!-->!-->!-->…
Gwamnatin Tarayya Ta Sha Alwashin Kakkaɓe Ƴanbindiga Yayin Da Minista, CDS Suka Isa Sokoto
A jiya ne Gwamnatin Tarayya ta bakin Ƙaramin Ministan Tsaro, Dr. Bello Matawalle, ta sha alwashin kakkaɓe ƴanbindiga da sauran gungun masu aikata laifuka da ke addabar yankin arewa maso yamma, biyo bayan umarnin Shugaban Kasa Bola Tinubu!-->…
HAUHAWAR FARASHI: FCCPC Ta Janye Shirinta Na Daidaita Farashin Kayayyaki A Najeriya
Biyo bayan cece-kuce da aka samu game da barazanar da Hukumar Kula da Gasar Kasuwanci da Kare Haƙƙin Masu Sayen Kaya ta Kasa (FCCPC) ta yi na shiga tsakani kan hauhawar farashin kayayyaki, hukumar ta bayyana cewa ba za ta shiga cikin!-->…
NLC Ta Yi Watsi Da Ƙarin Kuɗin Man Fetur, Ta Ce Gwamnati Ta Saɓa Alƙawarin Da Aka Yi Da Ita
Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta ce ƙarin farashin fetur da aka yi kwanan nan abin firgici ne da tayar da hankali.
NLC ta kuma ce Gwamnatin Tarayya ta yi mata kafar ungulu bayan yarjejeniyar da suka cimma yayin tattaunawa kan mafi!-->!-->!-->…
Gwamnan Jigawa Ya Jagoranci Tawaga Zuwa Taron Ƙoli Kan Tsarin Abinci Na Afirka A Kigali
Gwamnan Jihar Jigawa, Mallam Umar Namadi, ya jagoranci tawagar jihar zuwa taron shekara-shekara na Tsarin Abinci na Afirka na shekarar 2024, wanda aka fara a ranar Litinin a Kigali, Rwanda.
Halartar Gwamnan taron na nuna ƙudirin Jihar!-->!-->!-->…
Nan Da Awa 48 Man Dangote Zai Shiga Gidajen Mai, An Kuma Bayyana Yanda Farashi Zai Kasance
Mamallakin matatar mai da ke Lagos, Aliko Dangote, a yau Talata ya yi bayani kan yanda za a saka farashin fetur da matatarsa mai tace ganga 650,000 a kowace rana zata fara sayarwa.
Dangote ya bayyana cewa da zarar kamfaninsa ya kammala!-->!-->!-->…
Kamfanin NNPC Ya Ƙara Farashin Man Fetur A Najeriya
Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL) ya ƙara farashin man fetur daga ₦568 zuwa ₦855, ₦897 (dangane da wurin sayarwa), duk da ƙarancin fetur da kuma halin da ƙasar ke ciki.
Rahotanni kan sabon karin farashin sun biyo bayan furucin da!-->!-->!-->…
Gurfanar Da Masu Zanga-Zangar #EndBadGovernance Barazana Ce Ga Dimokuraɗiyya — NANS
Ƙungiyar Ɗaliban Najeriya (NANS) ta bayyana damuwarta game da gurfanar da mutanen da suka shiga zanga-zangar #EndBadGovernance.
Ƙungiyar ɗaliban ta bayyana matakin shari'a da aka ɗauka a matsayin babbar barazana ga dimokuradiyya a!-->!-->!-->…
YANZUNNAN: Zanga-Zanga Ta Barke A Abuja Kan Karancin Fetur
Wasu masu zanga-zanga sun mamaye titunan Abuja a yau Litinin suna neman a sauke Shugaban Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL), Mele Kyari, bisa matsalar karancin fetur da ke addabar kasar.
Zanga-zangar ta biyo bayan amincewar Kamfanin!-->!-->!-->…
PDP Na Tattaunawa Da Kwankwaso Da Peter Obi Kan Zaɓen 2027 — Kakakin Jam’iyyar
Jam’iyyar PDP ta fara tattaunawa da tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Kwankwaso da kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP) a zaben 2023, Mista Peter Obi, kan zaben 2027 mai zuwa.
Mataimakin Kakakin Jam’iyyar PDP na!-->!-->!-->…
DA ƊUMI-ƊUMI: Ƴan Sanda Sun Ayyana Baturen Birtaniya Da Ɗan Najeriya a Matsayin Wadanda Ake Nema…
Rundunar ‘Yansandan Najeriya, a ranar Litinin, ta bayyana wani ɗan ƙasar Birtaniya mai suna Andrew Wynne, wanda kuma aka sani da Andrew Povich, da wani dan Najeriya mai suna Lucky Obiyan, a matsayin wadanda ake nema saboda zargin yunkurin!-->…
‘Zanga-Zanga Ba Cin Amanar Kasa Ba Ne’, Baturen Birtaniya Ya Caccaki Gwamnatin Tarayya Kan Zargin…
Baturen Birtaniya da ake zargi da tayar da fitina a kan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, Drew Povey, ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ka da ta dauki zanga-zanga a matsayin cin amanar kasa.
Mista Povey, wanda gwamnatin Najeriya ta ce!-->!-->!-->…
Gwajin Gado: Kashi 27% Na Maza Ba Su Ne Iyayen Yaran Da Aka Ce Sun Haifa Ba – Rahoto
Wani sabon rahoto daga Smart DNA, wata cibiya da ke gudanar da gwaje-gwajen kwayoyin halitta a Lagos, ya nuna cewa kashi 27% na maza da suka yi gwajin ƙwayoyin halitta ba su ne iyayen yaran da aka ce sun haifa ba.
Rahoton, wanda ya!-->!-->!-->…
Ambaliyar Ruwa Ta Mamaye Jihohi 29 Na Najeriya
Ambaliyar ruwa mai tsanani ta shafi jihohi 29 na ƙasar nan, inda adadin mutanen da suka mutu ya ƙaru zuwa 192, a cewar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA).
Ambaliyar, wadda aka alaƙanta da samun yawaitar ruwan sama da kuma!-->!-->!-->…
NNPCL Ya Amince Da Bashin Da Ake Binsa Ne Dalilin Matsalar Fetur A Najeriya
Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL) ya amince da cewa yana da ɗinbin bashi a kansa na masu kawo man fetur, wanda ya kai dala biliyan 6, wanda ya ce shi ne babban dalilin da ya haifar da karancin fetur a sassan ƙasar nan.
Kamfanin ya!-->!-->!-->…
Kwanan Nan Gwamnati Za Ta Buɗe Boda Don Hada-Hadar Kasuwanci – Wani Ɗan Majalisa
Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Mazaɓar Badagry, Mista Sesi Whingah, ya tabbatar wa al’ummar mazaɓarsa cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu za ta buɗe iyakokin ƙasar nan don gudanar da ayyukan kasuwanci nan ba da jimawa ba.
Whingah ya!-->!-->!-->…
Zaɓen 2027: Ko Jam’iyyun Adawa Zasu Iya Haɗa Kai Su Ƙalubalanci APC?
A halin yanzu, kowanne daga cikin manyan jam’iyyun adawa irin su Peoples Democratic Party (PDP), Labour Party (LP), All Progressives Grand Alliance (APGA), New Nigeria Peoples Party (NNPP), da African Democratic Congress (ADC) suna fama da!-->…
Yanda Zanga-Zangar #EndBadGovernance Ta Sa Tinubu Ya Kori Shugabannin DSS Da NIA
Dalilan da suka sa tsohon Darakta-Janar na Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS), Yusuf Bichi, da Darakta-Janar na Hukumar Leken Asiri ta Ƙasa (NIA), Ahmed Abubakar, suka sauka daga mukamansu sun bayyana.
Wata majiya daga fadar shugaban ƙasa!-->!-->!-->…
Wata Ƙungiyar Musulmai Ta Dasa Bishiyoyi 2000 A Sabon Ginin FMC, Birnin Kudu
Reshen Ƙungiyar Musulmai ta Jama’atu Nasril Islam, JNI, na Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu ya fara dashen bishiyoyi dubu biyu a sabon ginin asibitin Gwamnatin Tarayya na Federal Medical Centre Birnin Kudu.
Shugaban Sashin Yaɗa Labarai!-->!-->!-->…
Ba Zan Nemi Takarar Shugaban Ƙasa A 2027 Ba Matuƙar Goodluck Zai Nema, In Ji Bala Mohammed
A lokacin da ake cigaba da hasashe da kiraye-kiraye kan babban zaɓen shekarar 2027, ɗaya daga cikin waɗanda ake sa ran zasu nemi takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP, Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed ya ce, ba zai nemi takarar ba,!-->…