Sign in
Sign in
Recover your password.
A password will be e-mailed to you.
Browsing Category
Gwamnati
Sama Da Kaso 30 Cikin 100 Na Malaman Makaranta A Najeriya Sun Ajjiye Aiki – Shugaban UBEC
Babban Sakataren Hukumar Kula da Ilimi Matakin Farko, UBEC, Hamid Bobboyi ya bayyana cewar, sama da kaso 30 cikin 100 na malaman makaranta da ke koyarwa a makarantun Najeriya sun ajjiye cikin shekaru uku da suka gabata.
Bobboyi ya!-->!-->!-->…
Kashim Shettima Ya Yi Gargaɗi Kan Wulaƙanta Kuɗaɗen Ƙananan Hukumomi
Matimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya bayyana cewar, ƴancin ƙananan hukumomi zai magance matsalolin kuɗaɗe da ke jawo tarnaƙi ga cigaban ilimi a matakin farko a Najeriya.
Shettima ya ƙara da cewa, hukuncin Kotun Ƙoli na kwanan nan!-->!-->!-->…
Har Yanzu Ba A Bayar Da Umarnin Biyan Mambobin NYSC ₦70,000 Ba
Hukumar kula da masu yi wa ƙasa hidima ta NYSC ta musanta labarin da ta kira na ƙanzon kurege wanda ke zagayawa a kafafen yaɗa labarai, na cewar za a biya masu bautar ƙasa mafi ƙarancin albashi na naira 70,000.
A wata sanarwa da!-->!-->!-->…
Jami’an Gwamnatin Najeriya Sun Yi Badaƙalar Cinhanci Ta Naira Biliyan 721 A 2023 – NBS
Wani sabon rahoto da Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa, NBS, ta fitar ya nuna cewar, jami’an gwamnatin Najeriya sun bayar da cinhancin da ya kai naira biliyan 721 a shekarar 2023 da ta gabata.
Rahoton mai taken ‘Cinhanci a Najeriya: Yanayi da!-->!-->!-->…
Bin Hukuncin Kotun Ƙoli Kan Ƙananan Hukumomi Dole Ne, In Ji Wani Gwamna
Gwamnan Jihar Anambra, Charles Soludo ya ce, gwamnoni zasu yi duba ga hukuncin Kotun Ƙoli wanda ya bai wa ƙananan hukumomi ƴancin tasarrufi da kuɗaɗensu.
Soludo ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis bayan ganawa da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed!-->!-->!-->…
DA ƊUMI-ƊUMI: Shugaba Tinubu Ya Ƙirƙiri Sabuwar Ministry A Najeriya
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da ƙirƙirar sabuwar Ma’aikatar Gwamnatin Tarayya kan Harkokin Kiwo.
Shugaban ya bayyana hakan ne yau Talata lokacin da yake ƙaddamar da Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Inganta Harkokin Kiwo a Fadar!-->!-->!-->…
Gwamnatin Tarayya Zata Buɗe Boda, Ta Janye Harajin Shigo Da Shinkafa, Alkama, Wake Da Sauransu
Gwamnatin Tarayya na shirin buɗe boda tare janye harajin shigo da wasu muhimman kayan abinci ta iyakokin ƙasa da kuma na ruwa.
TASKAR YANCI ta tattaro cewar, wannan hukunci ya fito ne saboda buƙatar da ake da ita na samun sauƙin!-->!-->!-->…
Gwamnatin Tarayya Ta Bayar Da Hutun Ranar Demokaraɗiyya
Gwamnatin Tarayya ta bayyana ranar Laraba, 12 ga watan Yuni, 2024 a matsayin ranar hutu a Najeriya domin murnar zagayowar ranar demokaraɗiyya.
A wata sanarwa da ta fita yau Talata daga Ministan Harkokin Cikin Gida, Tunji Ojo a madadin!-->!-->!-->…
Kwamitin Samar Da Sabon Mafi Ƙarancin Albashi Ya Miƙa Rahoton Kammala Aikinsa Ga Gwamnatin Tarayya
A jiya Litinin, Kwamitin Samar da Sabon Mafi Ƙarancin Albashi ya miƙa rahotonsa ga Sakataren Gwamnatin Tarayya bayan kammala aikinsa.
Daraktan Sadarwa da Hulɗa da Jama’a na ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Segun Imohiosen ne ya!-->!-->!-->…
Ƴan Najeriya Na Roƙon Ƴan Ƙwadago Da Su Bar Wutar Lantarki A Lokacin Yajin Aiki
A daidai lokacin da dambarwa ke cigaba da ƙamari tsakanin ƙungiyoyin ƙwadago da Gwamnatin Tarayya kan mafi ƙarancin albashi, ƴan Najeriya sun shiga shafukan sa da zumunta domin roƙar ƴan ƙwadagon da kar su katse wutar lantarki a lokacin!-->…
DA ƊUMI-ƊUMI: Ƴan Majalissar Wakilai Na Neman A Mayar Da Wa’adin Shugaban Ƙasa Shekaru 6
Wani gungun ƴan majalissar wakilai na neman a gyara Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 domin bayar da damar zagaya muƙamin shugaban ƙasa zuwa yankuna 6 na Najeriya.
Ƴan majalissar na kuma son a samar da wa’adi ɗaya na shekaru 6 ga!-->!-->!-->…
Kotu Ta Hana Sarki Aminu Ado Kiran Kansa A Matsayin Sarki, Ta Kuma Umarci Ƴansanda Su Fitar Da Shi
Babbar Kotun Jihar Kano ta umarci tuɓaɓɓen Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero da ya dena kiran kansa a matsayin Sarkin Kano, sannan ta kuma umarci ƴansanda da su fitar da shi daga ƙaramar masarautar da ke kan titin State Road.
Kotun!-->!-->!-->…
Ƴansanda Da Sojoji Sun Bijirewa Gwamnan Kano, Sun Ce Zasu Tabbatar Da Umurnin Kotu Na Dakatar Da…
Jami'an tsaro a Kano sun ce sun karbi umarnin kotu kuma za su yi amfani da shi tare da samar da cikakken tsaro a faɗin jihar Kano.
Cikin wani jawabin hadin gwiwa da jami'an tsaron suka gabatar wa manema labarai a shalkwatar 'yan sanda!-->!-->!-->…
RIGIMAR SARAUTA: Malaman Musulunci Sun Roki Tinubu Da Ya Bari A Zauna Lafiya A Kano
Kungiyar Malaman Musulunci a Jihar Kano, Ulama, sun roƙi Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da ya sanya baki tare da kare duk wani abu da zai kawo hatsaniya da karya doka a jihar.
A wata sanarwa da mambobin Ulama 18 suka sanya wa hannu, malaman!-->!-->!-->…
Gwamanti Da Majalisa Sun Ceto Tarihin Kano – Sarki Muhammadu Sanusi Il
Sabon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi ll ya ce, da an bar batun rarraba masarautu a Kano, to da an ci gaba da rarraba masarautu a jihar kenan.
''Da an bar wannan lamari na rarraba masarautu to da wata rana sai an naɗa Sarkin Fagge, ko!-->!-->!-->…
Naira 48,000 Ko Naira 615,000 Cinikin Albashi Tsakanin Mai Mugun Tayi Da Mai Mugun Farashi
Daga: Ahmed Ilallah
Shin ya.za a kira wannan ciniki tsakaninn Kungiyar Kwadago da Gwamnatin Tarayya?
Shin Gwamnati zata iya biyan N615,000 ko Yan Kwadago zasu aminta da tayin N48,000 din a ka yi musu?
Wannan mugun tayi na!-->!-->!-->!-->!-->!-->!-->…
Gwamnonin Arewa Maso Gabas Sun Kushe Gwamnatin Tarayya Kan Watsi Da Yankinsu Da Ta Yi
A yau Asabar ne Ƙungiyar Gwamnonin Yankin Arewa Maso Gabas suka koka kan watsin da suka ce an yi da yankin.
Gwamnonin sun yi ƙorafin cewa, rashin samun aiyukan Gwamnatin Tarayya a yankin ya yi ƙamari.
Gwamnonin sun bayyana hakan ne a!-->!-->!-->!-->!-->…
Za A Cigaba Da Dambarwa Tsakanin Ƴanƙwadago Da Gwamnati Ranar Talata Kan Mafi Ƙarancin Albashi
Tattaunawa kan mafi ƙarancin albashi a Najeriya zata cigaba a ranar Talata mai zuwa a daidai lokacin da ake cigaba da musayen maganganu tsakanin jami’an gwamnati kan abun da ya faru a farkon makon nan inda gwamnati ta nuna zata bayar da!-->…
Najeriya Zata Karɓi Bashin Naira Tiriliyan 3.2 Daga Bankin Duniya A Ranar 13 Ga Yuni
Gwamnatin Tarayya ta shirya domin karɓar sabon bashi daga Bankin Duniya mai yawan adadin dala biliyan 2.25 daidai da naira tiriliyan 3.2 a ranar 13 ga watan Yuni, 2024.
Najeriyar zata karɓi waɗannan maƙudan kuɗaɗe ne saboda wasu manyan!-->!-->!-->…
Shugaba Tinubu Ya Ce CBN Ya Dakatar Da Maganar Cirar Harajin Kula Da Intanet Kan Asusun Mutane
Wasu majiyoyi da ke da kusanci da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu sun bayyana cewar shugaban ya umarci Babban Bankin Najeriya, CBN da ya dakatar da batun cirar harajin bayar da tsaron intanet ga asusun bankunan ƴan Najeriya.
Majiyoyin!-->!-->!-->…