Sign in
Sign in
Recover your password.
A password will be e-mailed to you.
Browsing Category
Gwamnati
YANZU-YANZU: Tinubu Ya Naɗa Jamila Da Ayodele A Matsayin Ministocin Matasa
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa Dr. Jamila Bio Ibrahim da Mr. Ayodele Olawande a matsayin ministocin da za su jagoranci Ma’aikatar Matasa ta Tarayya.
Sanarwar naɗin na su ta fito ne a wani jawabi da Mai Bayar da Shawara na!-->!-->!-->…
Tinubu Ya Karya Dokar CBN Wajen Naɗa Madadin Emefiele, In Ji Wani Lauya
Babban Daraktan Ƙungiyar Wayar da Kan Ƴan Ƙasa kan Ƴancin Kai ta CASER, Frank Tietie ya ƙalubalanci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa karya dokar Babban Bankin Najeriya, CBN kan cire tsohon gwamnan Babban Bankin, Godwin Emefiele, tsofin!-->…
JERIN SANAYE: Gwamnati Ta Goge Baragurbin Apps Na Bayar Da Bashi
Adadin apps na bayar da bashi da aka goge ya ƙaru daga tara zuwa 37, kamar yanda Hukumar Kula da Haƙƙin Mai Saye da Gogayya Tsakanin Kasuwanci ta Tarayya, FCCPC, ta fitar.
Haka kuma adadin apps na bayar da bashi waɗanda gwamnati ta!-->!-->!-->…
Tinubu Ya Ce Yana Firgita In Aka Nuna Ma Sa Yawan Ma’aikatan Da Ke Karɓar Albashi A Najeriya
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna damuwarsa bisa yawan ma’aikatan da ke karɓar albashi a matakin ƙasa da sauran matakai.
Shugaban Ƙasar ya bayyana abin da ke zuciyarsa ne a jiya Litinin lokacin da ya ke magana a wajen wani zaman!-->!-->!-->…
Kwamitin Majalissar Wakilai Ya Dakatar Da Aikinsa Saboda Yajin Aikin NLC
Saboda yajin aikin gargaɗin da NLC ta sanar da farawa a yau, kwamitin wucin gadi da ke bincikar badaƙalar ɗaukar ma’aikata a ma’aikatu da hukumomi, a jiya Litinin ya sanar da ɗage ci gaba da aikinsa har sai ranar Alhamis 7 ga watan!-->…
ASUU, ASUP, Bankuna Da Ma’aikatan Wutar Lantarki Sun Shiga Yajin Aiki Ƙarƙashin NLC
Ƙungiyoyin da ke ƙarƙashin Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya, NLC, sun jaddada goyon bayansu na shiga yajin aikin gargaɗi na kwanaki biyu da NLC ta fara a yau Talata.
Ƙungiyoyin sun haɗa da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa, ASUU; Ƙungiyar!-->!-->!-->…
NLC Ta Ƙi Yarda Da Kiran Gwamnatin Tarayya, Ta Jaddada Shiga Yajin Aiki
Shugabancin Ƙungiyar Ƙwadago, NLC, ya bijirewa zaman da Ministan Ƙwadago da Ɗaukar Ma’aikata, Simon Lalong ya kira domin dakatar da yajin aikin kwanaki biyu da NLC ta fara a yau Talata.
A zaman da aka gudanar jiya Litinin da yamma, iya!-->!-->!-->…
Ɗalibai Da Fusatattun Matasa Na Shirin Yin Zanga-Zangar Tarzoma Kan Matsatsin Da Ake Ciki A…
Sashin Tsaro na Farin Kaya, DSS, a yau Litinin ya bayyana cewar ya gano shirin da wasu suke yi a sassan ƙasar nan da gudanar da zanga-zanga mai ɗauke da tarzoma.
A sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na DSS, Peter Afunanya ya fitar, ya!-->!-->!-->…
Shugaban Ƙasa Tinubu Ya Dawo Da Dukkan Ambasadojin Najeriya Gida
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dawo dukkan ambasadojin Najeriya da ke ƙasashe daban-daban gida, in ji Ma’aikatar Harkokin Ƙasashen Waje.
Wannan na cikin sanarwar da Mai Taimakawa na Musamman kan Harkokin Sadarwa da Yaɗa Labarai na!-->!-->!-->…
Gwamnan Kano Ya Naɗa Ƙarin Masu Ba Shi Sahawara Guda 14 Da Masu Ba Shi Rahoto Guda 44
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, a yau Asabar hya sanar da ƙarin wasu masu ba shi shawara da ya naɗa su 14 da kuma manyan masu ba shi rahoto daga ma’aikatu da hukumomi a jihar su 44.
Wannan sanarwar na ƙunshe ne cikin snarwar da!-->!-->!-->…
Tinubu Ya Sa Jami’an Tsaro Su Ƙwato Bashin Da Aka Bai Wa Manoma Kafin Nan Da 18 Ga Satumba
Tsarin bayar da bashin noma na Anchor Borrowers da Babban Bankin Najeriya ya samar domin bunƙasa samar da amfanin gona a Najeriya ya shiga cikin garari saboda gazawar waɗanda suka mori shirin wajen biyan bashin da suka karɓa.
Rashin!-->!-->!-->…
A Binciki Tsoffin Shugabanni, A Sake Sunan Najeriya, In Ji Wani Babban Lauya
Babban Lauyan Najeriya, SAN, kuma tsohon Shugaban Ƙungiyar Nigerian Body of Benchers, Chief Wole Olanipekun, ya yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya binciki tsoffin shugabannin Najeriya domin gano yanda akai ƙasar ta dagule!-->…
Za A Siyar Da Litar Fetur Ƙasa Da Naira 200 Idan Matatun Mai Na Aiki
Shugaban Ƙungiyar Dillalai Man Fetur Masu Zaman Kansu ta Najeriya, IPMAN, reshen Jihar Rivers, Joseph Obele, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta tabbatar da cewar an gyara matatun man Najeriya kamar yanda aka tsara.
Ya ce, farashin!-->!-->!-->…
JERIN DARUSSA: Hukumar Kula Da Jami’o’i Ta Saki Sabuwar Manhajar Darussan Digiri A Najeriya
Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa, NUC, ta bayyana sabuwar manhajar da jami’o’in Najeriya za su na yin amfani da ita.
Da yake magana a taron da aka gudanar a Abuja, Mai Riƙon Shugabancin Hukumar NUC, Dr. Chris Maiyaki ya ce, sabuwar!-->!-->!-->…
DA ƊUMI-ƊUMI: NLC Za Ta Yi Yajin Aikin Gargaɗi Na Kwana Biyu A Farkon Mako Mai Zuwa
Ƙungiyar Ƙwadago, NLC, za ta fara gudanar da yajin aikin gargaɗi na kwanaki biyu a ranar Talata, 5 ga Satumba, 2023 saboda nuna rashin jin daɗinta ga gwamnati na gazawa wajen magance raɗaɗin ƙuncin rayuwar da janye tallafin man fetur ya!-->…
Gwamnatin Tarayya Ta Sanar Da Rufe Filin Jirgin Sama Na Lagos
Ministan Harkokin Jiragen Sama da Bunƙasa Hanyoyin Sararin Samaniya, Festus Keyamo ya umarci dukkan jiragen sama da su bar filin jirgin na Murtala Muhammed International Airport, MMIA, da ke Lagos daga ranar 1 ga watan Oktoba, 2023.
!-->!-->!-->…
Jigawa Za Ta Siyo Buhun Shinkafa Dubu 42, Za Ta Biya Wa Ɗaliban Jami’a Kuɗin Makaranta
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da samar da kayan tallafin rage raɗaɗin janye tallafin man fetur, biyawa ɗaliban jihar kuɗin karatu a jami’o’i da kuma siyo taraktocin noma guda 54 domin manoman jihar.
Gwamnatin ta amince da aiwatar da!-->!-->!-->…
NA MUSAMMAN: LGs A Jigawa Sun Gaza Shigar Da Kuɗin Fansho Kimanin Naira Biliyan 3.2
Ƙananan Hukumomi 27 na Jihar Jigawa sun gaza shigar da a ƙalla naira biliyan 3.2 na gudunmawar fansho tsawon shekaru kamar yanda jaridar PREMIUM TIMES ta gano.
Wasu takardu na gwamnati da jaridar ta samu sun bayyana cewar, ƙananan!-->!-->!-->…
DA ƊUMI-ƊUMI: Sojoji Sun Yi Wa Shugaban Ƙasar Gabon Juyin Mulki
Da sanyin safiyar yau Laraba, sojoji suka sanar da yin juyin mulki a ƙasa Gabon, inda suka ce, sun tunɓuke Shugaban Ƙasar Ali Bongo wanda ya ƙara lashe zaɓe a ranar Asabar da ta gabata.
Ali Bongo dai ya fara mulkin ƙasar Gabon ne a!-->!-->!-->…
Gwamna Namadi Ya Naɗa Masu Ba Shi Shawara Na Musamman Guda 35
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar A. Namadi ya amince da naɗin kashin farko na masu ba shi shawara, inda ya naɗa manyan masu ba shi shawara guda biyu da kuma masu ba shi shawara guda talatin uku.
Naɗin na ƙunshe ne cikin sanarwar da!-->!-->!-->…