Sign in
Sign in
Recover your password.
A password will be e-mailed to you.
Browsing Category
Gwamnati
Ana Matsawa Najeriya Kan Ta Amince Da Auren Jinsi
Cocin Angalican ta Najeriya ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta bijirewa kiraye-kirayen da Turawan Yamma ke mata na ta sake matsayinta kan auren jinsi a Najeriya.
Wannan dai na a cikin jawabin bayan taron da cocin ta saki bayan!-->!-->!-->…
Masu HND Zasu Mallaki Shaidar Digiri A Shekara 1 A Sabon Shirin Gwamnati
Hukumar Kula da Ilimin Fasaha ta Ƙasa, NBTE, ta ƙaddamar da shirin yin karatu ta yanar gizo ga masu shaidar Babbar Diploma ta Ƙasa, HND, domin su mallaki shaidar kammala digiri a shekara ɗaya.
NBTE ta bayyana cewar, karatun na shekara!-->!-->!-->…
Masu Juyin Mulkin Nijar Zasu Yankewa Bazoum Hukuncin Cin Amanar Ƙasa
A ranar Lahadin da ta gabata ne da daddare, gwamnatin mulkin sojin Nijar ta yi iƙirarin yankewa tsohon shugaban ƙasar da ta tunɓukar, Mohammed Bazoum hukuncin cin amanar ƙasa.
Sojojin sun kuma kushe hukuncin shugabannin ƙasashen Afirka!-->!-->!-->…
Kwanannan Naira Zata Farfaɗo, Masu Dala Zasu Tafka Asara – CBN
Akwai ƙwararan alamu da ke nuni da cewar, Babban Bankin Najeriya, CBN, ya shirya domin ɗaukar matakan farfaɗo da darajar naira a ƴan kwanaki masu zuwa kaɗan.
Wannan ci gaba dai idan ya tabbata, ana sa ran zai jawo faɗuwar farashin dala!-->!-->!-->…
DA ƊUMI-ƊUMI: NLC Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Matuƙar Aka Ƙara Kuɗin Mai
Ƙungiyar Ƙwadago, NLC, ta yi barazanar tsunduma yajin aikin sai-baba-ta-gani a duk faɗin Najeriya matuƙar aka ƙara kuɗin man fetur daga naira 617 da ake siyarwa a yanzu.
Ƙungiyar ta bayyana yunƙurin ƙarin da take ji ana yi a matsayin!-->!-->!-->…
Gwamnatin Kano Ta Soke Lasisin Makarantu Masu Zaman Kansu
Gwamnatin Jihar Kano ta soke lasisin dukkan makarantu masu zaman kansu da ke faɗin jihar.
Gwamnatin ta ɗauki wannan mataki ne a ranar Asabar da ta gabata, a lokacin zaman tattaunawa tsakaninta da masu makarantu masu zaman kansu a jihar.!-->!-->!-->…
Kwanannan Za A Koma Siyar Da Litar Fetur Naira 720 Saboda Faɗuwar Darajar Naira
Masu siyar da mai sun nuna cewar farshin man fetur zai tashi daga yanda yake a yanzu ya koma tsakanin naira 680 zuwa 720 a kwanaki masu zuwa matuƙar aka ci gaba da canja dala a kan naira 910 zuwa 950 a guraren canjin kuɗaɗe.
Su kuma!-->!-->!-->…
Ma’aikatan NBAIS Na Zanga-Zanga Kan Rashin Biyansu Albashin Watanni 17
Sama da ma’aikata 700 ne na Hukumar Kula da Ilimin Arabiya da Addinin Musulunci, NBAIS, suka koka kan rashin biyansu alabashin watanni 17 da suke bin gwamnati.
Ma’aikatan sun kuma bayyana cewa, sun cika dukkan wasu ƙa’idoji na yin!-->!-->!-->…
Gwamnatina Zata Magance Matsalar Tsaro A Najeriya – Shugaba Tinubu
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce, gwamnatinsa zata tanadi abubuwan da ake buƙata domin ƙara ƙarfin jami’an tsaro da samar musu da ƙarin walwala a sabon ƙudirinta na magance matsalar tsaro da sauran abubuwan da ke da alaƙa da shi a!-->…
El-Rufai Ya Haƙura Da Muƙamin Minista, Ya Tura Sunan Madadinsa
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai ya janye daga buƙatar zama ɗaya daga cikin ministocin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, kamar yanda jaridar PREMIUM TIMES ta gano.
Wata majiya daga Fadar Shugaban Ƙasa ta ce, El-Rufai ya!-->!-->!-->…
Wasu Sanatocin Sun Samu Naira Miliyan Biyu Ta Shiga Hutunsu – Sanata Ningi
Sanata Abdul Ningi mai wakiltar Mazaɓar Sanata ta Bauchi ta Tsakiya ya ce, wasu ƴan majalissar sun samu naira miliyan biyu a matsayin kuɗin alawus na hutunsu, duk da dai shi bai samu nasa ba.
A wani yanayi da sanatocin ba su so ba,!-->!-->!-->…
Likitoci Sun Janye Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani Da Suka Yi
Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Najeriya, NARD, ta janye yajin aikin sai baba ta gani da take yi a duk faɗin ƙasa, inda likitocin suka dawo aiki a yau Asabar.
Shugaban Ƙungiyar na Ƙasa, Innocent Orji ne ya tabbatar da hakan a!-->!-->!-->…
Naɗin Ministoci 5 Kacal Daga Kudu Maso Gabas Rashin Adalci Ne – Ƙungiyar Inyamurai
Ƙungiyar Al’ummar Inyamurai (Igbo) ta Ohanaeze Ndigbo ta koka kan naɗin iya ministoci biyar daga yankin Kudu Maso Gabas da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi.
Shugaban Ohanaeze, Emmanuel Iwuanyanwu ya ce, bai wa yankin Kudu Maso!-->!-->!-->…
DA ƊUMI-ƊUMI: Zamu Kashe Bazoum Matuƙar Aka Kawo Mana Hari – Sojojin Nijar
Rayuwar hanɓararren Shugaban Ƙasar Nijar, Mohammed Bazoum na cikin hatsari saboda barazanar da waɗanda suka hamɓarar da shi kuma suke riƙe da shi suka yi, ta cewar zasu kashe shi matuƙar ECOWAS tai ƙoƙarin tura sojoji don su dawo da!-->…
Kebbi Ta Amince Da Kashewa Ciyamomi Naira Miliyan 675 A Matsayin Alawus Na Kayan Gida
Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris ya amince da fitar da kuɗi kimanin naira miliyan 675 domin bayar wa ga shugabannin ƙananan hukumomi 21 da aka zaɓa a jihar.
Babban Sakataren Yaɗa Labarai na gwamnan, Alhaji Ahmed Idris ne ya bayyana!-->!-->!-->…
DA ƊUMI-ƊUMI: ECOWAS Ta Bayar Da Umarni Sojoji Su Yaƙi Masu Juyin Mulkin Nijar
Ƙungiyar Ci Gaban Tattalin Arziƙin Africa ta Yamma, ECOWAS, ta bayar da umarni ga sojojinta da ke jiran umarni da su farmaki masu juyin mulki a Nijar domin dawo da amfani da kundin tsarin mulkin ƙasar.
Jagoran ECOWAS, Omar Alieu Touray!-->!-->!-->…
‘Dole Ne Mu Yi Amfani Da Tattaunawa’ – Bola Tinubu A Buɗe Taron ECOWAS Na 2 Kan Juyin Mulki A Nijar
Shugaban Najeriya, kuma Shugaban Ƙungiyar Bunƙasa Tattalin Arziƙin Africa ta Yamma, Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da jawabin buɗe taron ECOWAS karo na biyu kan juyin mulkin da sojoji suka yi a Jamhuriyar Nijar.
A cikin jawabin nasa,!-->!-->!-->…
Ƴan Najeriya Sun Kashe Naira Tiriliyan 3.33 A Kira Da Data A 2022
Ƴan Najeriya da sauran masu amfani da netwok a Najeriya sun kashe naira tiriliyan 3.33 a kira, saka data, tura saƙon kar ta kwana da sauran abubuwan da ake da netwok a cikin shekarar 2022, in ji Hukumar Sadarwa ta Najeriya, NCC.
Wannan!-->!-->!-->…
Jihar Kano Na Buƙatar A Cire Jihohi 2 Daga Cikinta – Sanata Doguwa
Mataimakin Shugaban Majalissar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya tabbatarwa da masu neman Jihar Tiga da Jihar Gari daga cikin Jihar Kano cewar, Majalissar Tarayya za tai musu adalci a lokacin gyaran kundin tsarin mulki.
Sanata Barau!-->!-->!-->!-->!-->…
An Gwangwaje Sanatoci Da Kuɗaɗe Domin Su Ji Daɗin Yin Hutunsu
Shugaban Majalissar Dattawa, Godswill Akpabio ya faɗawa sanatoci cewar, Magatakardar Majalissar Tarayya zai tura musu wasu kuɗaɗe a asusunsu na banki domin su ji daɗin yin hutun da zasu shiga.
A wani bidiyo da ya zagaya yanar gizo a yau!-->!-->!-->…