Sign in
Sign in
Recover your password.
A password will be e-mailed to you.
Browsing Category
Ilimi
Labarai da nazari kan ilimi: makarantun firamare, sakandare, jami’o’i da horo. Muna duba ingancin koyarwa, manhaja da damar karatu a gida da ƙasashen waje. Bayani ga iyaye, malamai da ɗalibai.
NANS Ta Roƙi Gwamnati Da Ta Janye Sokewar Da Tai Wa Digirin Benin Da Togo
Shugabannin Ƙungiyar Ɗaliban Najeriya ta NANS a yankin kudu maso yamma sun roƙi gwamnatin tarayya da ta sake nazari kan soke shaidar karatun digiri daga manyan makarantu na ƙasar Benin da Togo.
A cikin wata sanarwa da Shugaban Reshen!-->!-->!-->…
JAMB Ta Gano Ɗalibai 21 Da Ke Da Sakamakon Jarabawar Bogi
Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a (JAMB) ta gano ɗalibai 21 da suka yi amfani da sakamakon jarrabawar Interim Joint Matriculation Board (IJMB) na bogi don samun gurbin karatu a shekarar 2023.
Wata takarda daga JAMB ta bayyana cewa,!-->!-->!-->…
Sama Da Kaso 30 Cikin 100 Na Malaman Makaranta A Najeriya Sun Ajjiye Aiki – Shugaban UBEC
Babban Sakataren Hukumar Kula da Ilimi Matakin Farko, UBEC, Hamid Bobboyi ya bayyana cewar, sama da kaso 30 cikin 100 na malaman makaranta da ke koyarwa a makarantun Najeriya sun ajjiye cikin shekaru uku da suka gabata.
Bobboyi ya!-->!-->!-->…
Kashim Shettima Ya Yi Gargaɗi Kan Wulaƙanta Kuɗaɗen Ƙananan Hukumomi
Matimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya bayyana cewar, ƴancin ƙananan hukumomi zai magance matsalolin kuɗaɗe da ke jawo tarnaƙi ga cigaban ilimi a matakin farko a Najeriya.
Shettima ya ƙara da cewa, hukuncin Kotun Ƙoli na kwanan nan!-->!-->!-->…
WAHALAR RAYUWA: Iya Ɗalibai 5,000 Ne Su Kai Rijistar Komawa Wata Jami’a Cikin Ɗalibai 30,000
A yayin da matsin tattalin arziƙi ke ƙara tsananta ga talakawan Najeriya, Jaridar NIGERIAN TRACKER ta gano cewar a Jami’ar Bayero da ke Kano, iya ɗalibai 5,000 ne suka yi rijistar komawa jami’ar cikin ɗalibai 30,000 da suka kammala hutu.
!-->!-->…
An Yi Kira Ga JAMB Da Ta Sauƙaƙa Hanyar Yin Regularization Ga Masu Cike DE
Hukumar Shiraya Jarabawar Share Fagen Shiga Jami’a, JAMB ta ce duk dalibin da ya zaɓi ya sami addmission ba ta ingantacciyar hanya ba zai fuskanci.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da JAMB ke jaddada cewar, duk wani admission na shiga!-->!-->!-->…
Malam Adamu Foundation Zata Ɗau Nauyin Karatun Ɗaliban Jigawa A Khadija University Majia
Gidauniyar Malam Adamu Foundation (MAF) ta Alhaji Musa Adamu Majia mamallakin Jami’ar Khadija da ke Majia a Jihar Jigawa zata ɗau nauyin karatun ɗalibai masu ƙaramin ƙarfi a Khadija University Majia.
MAF ta tanadi ɗaukar nauyin karatun!-->!-->!-->…
JAMB Ta Ƙara Kuɗin Rijistar Jarabawa
Hukumar Shirya Jarabawar Share Fagen Shiga Jami’a, JAMB ta ƙara kuɗin rijistar yin jarabawar UTME zuwa naira 7,700 da kuma naira 6,200.
Sanarwar ƙarin kuɗin ta fito ne daga hukumar shirya jarabawar a shafinta na X, inda ta sanar da fara!-->!-->!-->…
Gwamnatin Jigawa Ta Dakatar Da Biyan Ƴan J-Teach, Ta Kuma Gano Malaman Bogi 240 Da Masu Takardun…
Gwamnatin Jihar Jigawa ƙarƙashin jagorancin Gwamna Umar Namadi ta sanar da dakatar da biyan dukkan malaman da suke koyarwa a makarantun jihar ƙarƙashin shirin J-Teach.
Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu, Sagir Musa ne!-->!-->!-->…
Gwamnatin Tarayya Ta Shirya Kashe Wa Ɓangaren Ilimi Kaso 25% Na Kasafin Kuɗi
Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman ya bayyana cewar, Gwamnatin Tarayya ta shirya kashewa ɓangaren ilimi kaso 25 cikin ɗari na kasafin kuɗin kowacce shekara matuƙar akwai tsare-tsaren da su tabbatar da buƙatar kuɗaɗen.
Ministan ya!-->!-->!-->…
Tarayyar Turai Ta Ware Maƙudan Kuɗaɗe Don Malaman Makaranta Na Arewa Maso Yamma
A ƙoƙarinta na magance yawaitar yaran da ba sa zuwa makaranta a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya ta hanyar bunƙasa hanyoyin samun ingantaccen ilimi da rayuwar matasan yankin, Ƙungiyar Tarayyar Turai, EU, ta sanar da ƙarin tallafi na!-->…
Ɗiban Malaman Sa Kai Na J-Teach Ba Mafita Ba Ce Ga Matsalar Ƙarancin Malamai A Jigawa
Daga: Kabiru Zubairu Birnin Kudu
Na daɗe da ƙalubalantar yunƙurin gwamnatin Jihar Jigawa na magance gagarumar matsalar ƙarancin malaman makaranta da tai wa harkar ci gaban ilimin jihar dabaibayi tsawon shekaru na amfani da malaman sa!-->!-->!-->…
Kano Ta Ɓullo Da Tsarin Bai Wa Ɗalibai Mata Tukuicin Naira 20,000 Don Bunƙasa Shigarsu Makarantu
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanar da fara bayar da tukuicin naira 20,000 ga ɗalibai mata da ke jihar domin bunƙasa sha’awarsu ta zuwa makaranta.
Gwamnan wanda ya sanar da ci gaban a jiya Lahadi lokacin da yake jawabin!-->!-->!-->…
JERIN SUNAYE: Masu Degree Da Suka Samu Aikin Sa Kai Na J-Teach A Jigawa
Gwamnatin Jihar Jigawa ta saki sunayen masu degree waɗanda suka samu aiki sa kai na J-Teach domin koyarwa a manyan makarantun sikandiren jihar.
Gwamnatin ta kuma sanar da shirin bayar da horo na kwana ɗaya da aka shiryawa sabbin malaman!-->!-->!-->…
Gwamnatin Kano Za Ta Raba Littattafai Miliyan 3 A Makarantu, Za Ta Kuma Ginawa Malamai Gidaje
Gwamnatin Jihar Kano za ta raba littattafai miliyan uku ga ɗaliban da su ke karatu a makarantun gwamnati da ke jihar.
Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Umar Haruna Doguwa ne ya bayyana hakan a yau, yayin shirin BBC Hausa na ‘A Faɗa A!-->!-->!-->…
JERIN DARUSSA: Hukumar Kula Da Jami’o’i Ta Saki Sabuwar Manhajar Darussan Digiri A Najeriya
Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa, NUC, ta bayyana sabuwar manhajar da jami’o’in Najeriya za su na yin amfani da ita.
Da yake magana a taron da aka gudanar a Abuja, Mai Riƙon Shugabancin Hukumar NUC, Dr. Chris Maiyaki ya ce, sabuwar!-->!-->!-->…
DA ƊUMI-ƊUMI: ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki
Ƙungiyar Malam Jami’o’i ta Ƙasa, ASUU, biyo bayan Taron Shugabanninta na Ƙasa da ta yi a Jami’ar Maiduguri ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ofishin Babban Akawunta na Tarayya da ta saki kuɗaɗen ariyas na ƙarin girma da mambobin ƙungiyar ke!-->…
A Ɗauki Nauyin Karatun Mace 100% Ko Kuma . . .
'Ya mace, idan ba za a iya ɗaukar nauyin karatunta da buƙatunta a lokacin karatu 100% ba, a haƙura, ya fi maslaha da alheri.
Ke ma idan kin san gidanku ba za su ba ki full scholarship ba, ki haƙura.
Wasu na amfani da talaucinsu yara!-->!-->!-->!-->!-->…
Sanata Malam Madori Ya Fi Kowa Temakawa Ɗalibai A Yankin Jigawa Ta Gabas
Daga: Ahmed Ilallah
Duk da cewa a nawa ra'ayin kamata yayi wakilan al'ummah musamman a Majalissar Dokoki su maida hankali wajen samar da doka da kuma tilastawa shugabannin wajen samar da yanayi mai kyau da duk Dan Talaka zai samu kowane!-->!-->!-->…
Kusan Sabon Ministan Ilimi Na Najeriya, Farfesa Mamman
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Babban Lauyan Najeriya, Farfesa Tahir Mamman a matsayin sabon Ministan Ilimi na Najeriya.
Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Kafafen Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Ajuri Ngelale ne ya bayyana!-->!-->!-->…