Sign in
Sign in
Recover your password.
A password will be e-mailed to you.
Browsing Category
Kasuwanci
Labaran kasuwanci da tattalin arziki: farashi, sana’o’i, banki, jari da kasuwa. Muna mayar da hankali kan damammaki ga ’yan kasuwa da masu zuba jari a Arewa da sauran yankuna. Karanta shawarwari da kididdiga masu amfani.
An Sanya Ranar Kammala Aikin Gyaran Wutar Yankunan Gagarawa, Hadejia Da Nguru
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya, TCN, ya fara aikin gyaran ƙarfen tawa ta 16 da ya karye a Ƙauyen Gunduwawa da ke Ƙaramar Hukumar Gezewa a Jihar Kano.
Shugaban Sashin Hulɗa da Jama’a na kamfanin, Ndidi Mbah ne ya bayyana!-->!-->!-->…
Dalilan Da Suka Sa CBN Ya Amince Bankin Providus Ya Mallaki Bankin Unity
Wasu dalilai sun ƙara bayyana a jiya da suke nuni da abun da ya sa Babban Bankin Najeriya, CBN ya amince da hukuncin cewar Bankin Providus ya mallaki Bankin Unity.
Jaridar THISDAY ta tattaro muhimman abubuwan da babban bankin yai!-->!-->!-->…
Gwamnatin Tarayya Zata Buɗe Boda, Ta Janye Harajin Shigo Da Shinkafa, Alkama, Wake Da Sauransu
Gwamnatin Tarayya na shirin buɗe boda tare janye harajin shigo da wasu muhimman kayan abinci ta iyakokin ƙasa da kuma na ruwa.
TASKAR YANCI ta tattaro cewar, wannan hukunci ya fito ne saboda buƙatar da ake da ita na samun sauƙin!-->!-->!-->…
Naira Ta Ƙara Daraja A Farashin Gwamnati Jiya Litinin
Naira ta samu ƙarin daraja jiya Litinin, inda aka siyar da dala 1 a kan naira 1,339.33 a farashin gwamnati, abun da ya nuna cewar ta samu ƙarin daraja da kaso 9.68 cikin 100 kan yanda darajarta ta kasance a ranar Juma’ar da ta gabata inda!-->…
Babu Buƙatar Najeriya Ta Ƙara Shigowa Da Man Fetur Daga Wata Mai Zuwa, In Ji Dangote
Wanda ya fi kowa kuɗi a Afirka kuma Shugaban Rukunin Kamfanonin Ɗangote, Aliko Dangote ya bayyana tabbatuwar shirye-shiryen Matatar Dangote da zasu kai Najeriya ga dena shigowa da tattaccen manfetur daga wata mai zuwa.
Dangote ya kuma!-->!-->!-->…
Najeriya Zata Karɓi Bashin Naira Tiriliyan 3.2 Daga Bankin Duniya A Ranar 13 Ga Yuni
Gwamnatin Tarayya ta shirya domin karɓar sabon bashi daga Bankin Duniya mai yawan adadin dala biliyan 2.25 daidai da naira tiriliyan 3.2 a ranar 13 ga watan Yuni, 2024.
Najeriyar zata karɓi waɗannan maƙudan kuɗaɗe ne saboda wasu manyan!-->!-->!-->…
Shugaba Tinubu Ya Ce CBN Ya Dakatar Da Maganar Cirar Harajin Kula Da Intanet Kan Asusun Mutane
Wasu majiyoyi da ke da kusanci da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu sun bayyana cewar shugaban ya umarci Babban Bankin Najeriya, CBN da ya dakatar da batun cirar harajin bayar da tsaron intanet ga asusun bankunan ƴan Najeriya.
Majiyoyin!-->!-->!-->…
Gwamnatin Tarayya Zata Sauƙaƙa Hanyar Samun Asusun Bankuna Ga Waɗanda Ba Su Da Su
Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana tsare-tsaren gwamnantin tarayya domin rage talauci da matsalar tsaro a faɗin ƙasa ta hanyar shigar da ƴan Najeriya cikin harkokin samun kuɗaɗe.
Fadar ta bayyana cewar akwai muhimman tattaunawa da ake yi!-->!-->!-->…
Litar Man Fetur Zata Dawo Naira 500 Idan Matatar Mai Ta Port Harcourt Ta Fara Aiki A Kwanannan
A daidai lokacin da ma’aikatan matatar mai ta Port Harcourt ke rige-rige wajen ganin sun kammala aikin daidaita matatar domin fara fitar da tataccen mai, dillalan man fetur na shiryawa domin fara saro man fetur daga matatar.
A ranar!-->!-->!-->…
Katafariyar Kasuwar Zamani Ta Shoprite Ta Sanya Ranar Barin Kano
Kamfanin Kasuwar Shoprite ya yanke shawarar bin kamfanin Procter & Gamble da sauran manyan kamfanonin ƙasa da ƙasa na dakatar da kasuwanci a reshensa na Kano daga ranar 14 ga watan Janairu mai kamawa.
A sanarwar da kamfanin Shoprite!-->!-->!-->…
DA ƊUMI-ƊUMI: Kamfanin BUA Ya Sauƙo Da Farashin Simintinsa Zuwa Naira 3,500
Kamfanin yin siminti na BUA ya sanar da rage farashin simintinsa mai nauyin kilogram 50 daga naira 4,800 zuwa naira 3,500 daga gobe Litinin.
Kamfanin ya sanar da rage farashin ne a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a yau Lahadi.
!-->!-->!-->!-->…
Najeriya Na Neman Sabon Bashin Naira Tiriliyan 1.2 Da Wasu Basussukan Daga Bankin Duniya
A yanzu haka Gwamnatin Tarayya na tattaunawa da Bankin Duniya kan sabon bashin da ya kai dalar Amurka biliyan 1.5 daidai da naira Tiriliyan 1.2, kamar yanda jaridar PUNCH ta gano.
Gwamnatin na neman bashin ne da a kai wa take da HOPE!-->!-->!-->…
JERIN SANAYE: Gwamnati Ta Goge Baragurbin Apps Na Bayar Da Bashi
Adadin apps na bayar da bashi da aka goge ya ƙaru daga tara zuwa 37, kamar yanda Hukumar Kula da Haƙƙin Mai Saye da Gogayya Tsakanin Kasuwanci ta Tarayya, FCCPC, ta fitar.
Haka kuma adadin apps na bayar da bashi waɗanda gwamnati ta!-->!-->!-->…
Za A Siyar Da Litar Fetur Ƙasa Da Naira 200 Idan Matatun Mai Na Aiki
Shugaban Ƙungiyar Dillalai Man Fetur Masu Zaman Kansu ta Najeriya, IPMAN, reshen Jihar Rivers, Joseph Obele, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta tabbatar da cewar an gyara matatun man Najeriya kamar yanda aka tsara.
Ya ce, farashin!-->!-->!-->…
Gwamnatin Tarayya Ta Sanar Da Rufe Filin Jirgin Sama Na Lagos
Ministan Harkokin Jiragen Sama da Bunƙasa Hanyoyin Sararin Samaniya, Festus Keyamo ya umarci dukkan jiragen sama da su bar filin jirgin na Murtala Muhammed International Airport, MMIA, da ke Lagos daga ranar 1 ga watan Oktoba, 2023.
!-->!-->!-->…
JUYIN MULKIN NIJAR: Ƴan Arewa Na Asarar Naira Biliyan 13 Duk Sati
Ƴan kasuwa a yankin Arewacin Najeriya sun koka kan yanda suke asarar kimanin naira biliyan 13 duk sati saboda rufe boda da aka yi biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar.
A ranar 4 ga watan nan na Agusta ne, Shugaban Ƙasa Bola!-->!-->!-->…
Darajar Naira Na Ƙara Farfaɗowa
Farashin dala na faɗuwa a kasuwannin canjin kuɗi a Najeriya daga naira 940 zuwa naira 890 a safiyar Laraba, kamar yadda bayanan da BBC ta samu daga kasuwannin canji a birnin Legas suka nuna.
Bayanan sun ce a safiyar jiya Talata, an!-->!-->!-->…
TSADAR MAI: Babu Wani Shirin Dawo Da Tallafin Mai A Najeriya, In Ji Fadar Shugaban Ƙasa
Babban Mai Temakawa Shugaban Ƙasa a Kan Harkokin Yaɗa Labari da Hulɗa da Jama’a. Tope Ajayi, ya ce, babu wani shirin da gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu take yi na dawo da tallafin man fetur.
Ajayi ya yi wannan bayani ne a yau!-->!-->!-->…
Kwanannan Naira Zata Farfaɗo, Masu Dala Zasu Tafka Asara – CBN
Akwai ƙwararan alamu da ke nuni da cewar, Babban Bankin Najeriya, CBN, ya shirya domin ɗaukar matakan farfaɗo da darajar naira a ƴan kwanaki masu zuwa kaɗan.
Wannan ci gaba dai idan ya tabbata, ana sa ran zai jawo faɗuwar farashin dala!-->!-->!-->…
Kwanannan Za A Koma Siyar Da Litar Fetur Naira 720 Saboda Faɗuwar Darajar Naira
Masu siyar da mai sun nuna cewar farshin man fetur zai tashi daga yanda yake a yanzu ya koma tsakanin naira 680 zuwa 720 a kwanaki masu zuwa matuƙar aka ci gaba da canja dala a kan naira 910 zuwa 950 a guraren canjin kuɗaɗe.
Su kuma!-->!-->!-->…