Sign in
Sign in
Recover your password.
A password will be e-mailed to you.
Browsing Category
Labarai
Sabbin labarai daga gida da waje cikin Hausa, tare da bayanai masu zurfi da gaskiya. Muna kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya, Arewa da sauran duniya cikin lokaci. Karanta takaitattun rahotanni, bincike da kwakkwaran bayani.
NELFUND Ya Fitar Da Sabon Tsarin Biyan Kuɗin Kula Da Kai A Makaranta ‘Upkeep Allowance’
Asusun Bayar da Bashin Karatu na Najeriya (NELFUND) ya sanar da dakatar da biyan kuɗin kula da kai na ɗalibai a lokacin da ake hutu.
Banda kuɗaɗen da ake biya kai tsaye ga makarantu, masu amfana na karɓar ₦20,000 a wata ne a tsawon!-->!-->!-->…
ASUU Ta Ƙara Yin Barazanar Tsunduma Yajin Aiki, Za A Gudanar Da Zanga-Zanga A Jami’o’i
Ƙungiyar malaman jami’o’i ta ASUU ta yi barazanar tsunduma yajin aiki na ƙasa baki ɗaya domin gwamnatin tarayya ba ta cika alƙawuran da ta ɗauka ba.
A taron manema labarai a Jami’ar Jos, Shugaban ASUU, Christopher Piwuna, ya ce malamai!-->!-->!-->…
JAM’IYYAR PDP: Rikicin Karɓa-Karɓa A Jam’iyyar Ya Ɓarke A Taron Lagos
Shugabannin PDP daga yankin Kudu sun hallara a Lagos cikin zazzafar muhawara kan rarraba muƙamai zuwa yankunan ƙasa kafin babban taron jam’iyyar.
An yi taron da aka kira “PDP Southern Zoning Consultative Summit” inda suka haɗu da!-->!-->!-->…
JIGAWA: Majalisar Tarayya Ta Yaba Wa Jihar Kan Juyin Juya Halin Lafiya
Kwamitin Majalisar Wakilai kan Ayyukan Lafiya ya yaba da zuba jari da gyare-gyaren Jigawa a ɓangaren lafiya.
Shugaban kwamitin, Amos Magaji, ya ce “fiye da kashi 15% na kasafin jihar na ɓangaren samar da lafiyar jama’a,” kuma hakan ya!-->!-->!-->…
Jami’ar Northwest, Ta Fara Ɗaukar Ɗalibai Don Shekarar Karatu Ta 2025/2026, Ta Bayyana Sharuɗɗa
Jami’ar Northwest, Sokoto, ta sanar da buɗe ɗaukar ɗalibai don shekarar karatu ta 2025/2026.
Rajistara, Alhaji Umar Mussa Garun Babba, ya ce an buɗe domin neman shiga tsangayu biyar na jami’ar.
A Tsangayar Lafiya akwai MBBS, Koyon!-->!-->!-->!-->!-->…
BAUCHI: Sarkin Ningi Ya Ƙaddamar Da Dashen Bishiyoyi Miliyan 1 Don Daƙile Hamadar Sahara
Sarkin Ningi, Alhaji Haruna Yunusa Danyaya III, ya ƙaddamar da dashen bishiyoyi miliyan ɗaya a Jimi, Ningi, Bauchi.
An yi aikin ne tare da Green Legacy Foundation ƙarƙashin jagorancin Magajin Garin Kano, inda aka raba shuke-shuke ga!-->!-->!-->…
Hukumar Ƴansanda Ta Ɗaga Darajar ASP 952 Zuwa DSP, Ta Ƙi Ɗaga Darajar Wasu Su 176
Hukumar Ƴansanda (PSC) ta amince da ƙarin girma ga ASP 952 zuwa muƙamin DSP bayan zaman majalisa na farko na sabon Kwamitin da aka samar.
Hukumar ta ƙi ɗaukaka wasu jami’ai 176 da aka gano sun yi ritaya da kuma uku da ake zargin sun!-->!-->!-->…
KATSINA: Dan Majalisa Ya Fashe Da Kuka a Zauren Majalissa Yayin Bayani Kan Matsalar tsaron Yankinsa
A Majalisar Katsina, Mai Tsawatarwa a Majalissar, Ibrahim Dikko ya sa kuka yayin da yake bayyana kisan manoma a Matazu.
Ya ce “daga cikin mazaɓu 10 na ƙaramar hukumar, takwas suna ƙarƙashin mamaya,” kuma “manoma ba sa iya zuwa gona.”
!-->!-->!-->!-->!-->…
PDP Ta Ce Wa Wike Ya Fice Daga Cikinta Idan Ba Zai Bi Ƙa’idojinta Ba
Jam’iyyar PDP ta yi gargaɗi cewa za ta hukunta duk wani mamba da ya karya kundinta bayan maganganun Ministan Abuja, Nyesom Wike.
Wike a wani shirin talabijin ya ce “ban san wani babban taron ƙasa ba,” kuma “ba za mu yarda da ‘rashin!-->!-->!-->…
An Buƙaci Tinubu Ya Zama Mai Shigar Da Ƙara A Kotun Duniya Kan Isra’ila, An Ce Lokaci Ya Yi
Ƙungiyar Muslim Public Affairs Centre (MPAC) ta buƙaci gwamnatin Najeriya ta shiga ƙarar da Afirka ta Kudu ta shigar a Kotun Duniya ICJ kan Isra’ila.
Shugaban MPAC, Disu Kamor, ya ce abin ya zama dole ganin yadda duniya ke kallo kawai!-->!-->!-->…
Rainin Hakali Ne Ke Sa Gwamnati Shirin Ƙarawa Shugabannin Siyasa Albashi – ADC
Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta yi watsi da shirin RMAFC na ƙara wa manyan masu riƙe da muƙaman siyasa albashi, tana kiran matakin “kurakurai ne na marasa tausayin talakawa.”
A cewar mai magana da yawun jam’iyyar, Mallam!-->!-->!-->…
Gwamnatin Tarayya Ta Rufe Shafukan TikTok, Facebook, Instagram Da X Miliyan 13.6, Ta Share Batutuwa…
Gwamnatin Tarayya ta sanar da rufe kusan asusun social media miliyan 13,597,057 tare da share batutuwan ciki guda miliyan 58,909,112 a TikTok, Facebook, Instagram da X saboda “cin zarafi da karya ƙa’idojin aiki” na dandamali.
A cewar!-->!-->!-->…
JIGAWA: Gwamnati Na Shirin Sauya Tsarin Tsangaya Don Samar Da Ingantacciyar Jiha
Jihar Jigawa ta kammala taron dabarun aiki na kwana biyu ga Hukumar Tsangaya (JSTEB) a Global Luxury Suites, Kano, inda aka gina tubalin sabuwar tafiyar da za ta sauya tsarin almajirci.
A cewar shirin gwamnatin jihar, wannan aikin “ya!-->!-->!-->…
Iran Ta Ce Ba Za Ta Yanke Hulɗa Gaba ɗaya Da IAEA Ba: Komawar Masu Sa-Ido Hannun Majalisar Tsaron…
Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce “ba za mu iya yanke hulɗa gaba ɗaya da hukumar ba,” sai dai dawowar masu sa-ido na IAEA na hannun Babbar Majalisar Tsaron Ƙasa, bayan dakatar da haɗin kai da hukumar kimanin watanni biyu!-->…
Tarbiyyara Matasa: Indiya Za Ta Haramta Caca Ta Yanar Gizo
Gwamnatin Indiya ta gabatar da ƙudirin doka a majalisar ƙasa domin haramta caca ta yanar gizo saboda halin jaraba, asarar kuɗi da kuma yiwuwar alaƙa da wanke kuɗaɗen haramun da ɗaukar nauyin ta’addanci, lamarin da ke barazana ga ɗaruruwan!-->…
JIGAWA: An Haɗa Kai Da UNICEF Don Haɓaka Kasafin Kuɗin Bangaren Ilimi
Gwamnatin Jihar Jigawa tare da UNICEF sun ƙaddamar da atisayen horaswa ga fiye da jami’ai 90 kan Result-Based Budgeting wato kasafin kuɗi mai amfani a Katsina, da mayar da hankali kan inganta kuɗaɗen ɓangaren ilimi.
A cewar Muntaka!-->!-->!-->…
KATSINA: Kwastam Ta Kama Miyagun Ƙwayoyi Na Miliyoyin Nairori, Ana Zarginsu Da Ta’addanci
Hukumar Kwastam ta kama miyagun ƙwayoyi da ƙimarsu ta kai naira miliyan 692 a Katsina, abin da aka bayyana a matsayin mafi girma a tarihin rundunar a jihar.
Jami’ai sun tare motoci biyu a yankin Kongolom da wasu unguwannin kan iyaka,!-->!-->!-->…
KANO: Hukumomin Saudiyya Sun Kama Ƴar Kano Da Jakar Wiwi
Hukumomin Saudiyya sun tsare Maryam Hussaini-Abdullahi, ƴar Najeriya ƴar asalin Kano mai ƴaƴa biyar, bayan wata jaka da ake zargi ɗauke da wiwi ta bayyana sunanta bisa kuskuren kamfanin jirgin Ethiopian Airlines yayin da ita da mijinta,!-->…
INEC Ta Ayyana Wani Mai Zaman Gidan Yari A Matsayin Wanda Ya Lashe Zaɓe A Enugu
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ayyana Bright Emeka Ngene na Labour Party a matsayin wanda ya yi nasara a sabon zaɓen Enugu ta Kudu da aka gudanar a ranar 16 ga Agusta 2025, bayan sake samun matsala tun daga Fabrairun 2024.
A sanarwar da!-->!-->!-->…
JIGAWA: An Fara Tantance Almajirai Don Ba Su Horo Da Rubuta Jarrabawar NBAIS
An kammala sa-ido kan yadda aka gudanar da zaɓen almajiran tsangaya da malamai masu horaswa a Cibiyar Hadejia (Jigawa Arewa maso Gabas), wani muhimmin mataki da Hukumar Ilimin Tsangaya ta Jihar Jigawa ta shirya a cibiyoyi uku a faɗin!-->…