Sign in
Sign in
Recover your password.
A password will be e-mailed to you.
Browsing Category
Labarai
Sabbin labarai daga gida da waje cikin Hausa, tare da bayanai masu zurfi da gaskiya. Muna kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya, Arewa da sauran duniya cikin lokaci. Karanta takaitattun rahotanni, bincike da kwakkwaran bayani.
Kamfanin Meta Zai Dakatar Da Facebook Da Instagram A Najeriya
Kamfanin Meta, mai mallakar Facebook da Instagram, ya yi barazanar dakatar da ayyukansa a Najeriya sakamakon abin da ya bayyana a matsayin “buƙatu marasa cimmuwa” daga hukumomin Najeriya da kuma tarar kusan dala miliyan 290 da ake bin shi!-->…
Zamu Tsare Dazukanmu, Mu Ƙarfafa Harkokin Leƙen Asiri – Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana ƙudirin gwamnatinsa na ƙarfafa tsaro da sake ƙwace dazukan da ƴan bindiga da ƴan ta’adda suka mamaye musamman a yankin Arewa maso Yamma, inda ya ce “zamu zuba jari a fannin fasaha mu ƙwace!-->…
An Gano Fiye Da Naira Biliyan 80 A Asusun Wani Shugaban NNPC
Hukumar EFCC ta kama tsoffin shugabannin kamfanonin gyaran matatun mai na Port Harcourt, Warri da Kaduna tare da wasu manyan jami’an kamfanonin saboda zargin almundahana ta fiye da dala biliyan 2.9 da aka ware don gyaran matatun, yayin da!-->…
Gwamnatin Jigawa Na Kiran Manoman Shinkafa Ƴar Rani Don Su Karɓi Kayan Noma
Mai ba wa Gwamnan Jigawa, Malam Umar Namadi shawara kan harkokin noma, Alhaji Muhammad Idris Danzomo, ya buƙaci manoman shinkafa da suka samu saƙon karɓar kayayyakin shuka da su hanzarta zuwa domin karbar su a kan lokaci.
A wata ganawa!-->!-->!-->…
Birnin Kudu Za Ta Raba Kayan Koyon Sana’a Ga Matasa Don Rage Zaman Kashe Wando
Gwamnatin Ƙaramar hukumar Birnin Kudu ta bayyana damuwa kan yadda wasu ɓata-gari ke sace kayan gwamnati kamar su bututun ruwa da wayoyin lantarki, lamarin da ke haifar da matsaloli ga ci gaban al’umma.
Shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Dr.!-->!-->!-->…
Da Iya Lambobin Jikin ATM Ɗinka Ƴandamfara Zasu Sace Maka Kuɗi – Ƴansanda
Rundunar ƴan sandan jihar Delta ta gargaɗi ƴan Najeriya da su kiyaye wajen mu’amala da katin ATM domin guje wa faɗawa tarkon masu zamba ta yanar gizo da ke amfani da bayanan katin domin kwashe kuɗi daga asusun mutane.
Jami’in hulɗa da!-->!-->!-->…
YANZU-YANZU: Sojoji Na Artabu Da Ƴan ISWAP A Yobe
Dakarun rundunar Operation HADIN KAI sun shiga artabu mai tsanani da mayaƙan ƙungiyar ISWAP a garin Buni Gari da ke jihar Yobe, lamarin da ya haifar da fargaba a tsakanin mazauna yankin.
A wata gajeriyar sanarwa da rundunar ta wallafa a!-->!-->!-->…
Tinubu Ya Sa Ranar Da Za A Kammala Aikin Layin Dogo Na Kano-Jigawa-Katsina-Maradi
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya na shirin kammala aikin layin dogo mai tsawon kilomita 284 daga Kano zuwa Maradi wanda zai bi ta Jigawa da Katsina nan da shekarar 2026 domin rage cunkoson hanyoyi da!-->…
Jigawa Ta Fara Yi Wa Alhazai Rigakafi Kafin Tafiya Aikin Hajjin Bana
Gwamnatin Jihar Jigawa ta fara allurar rigakafi ga alhazai da ke shirin tafiya aikin hajjin bana a wani mataki na tabbatar da lafiyar su kafin su tashi zuwa ƙasa mai tsarki.
An ƙaddamar da shirin rigakafin ne a Hadejia, hedkwatar yankin!-->!-->!-->…
An Kafa Kwamitin Da Zai Jagoranci Tallafawa Matan Jigawa A Fannin Tattalin Arziƙi
Gwamnatin Jihar Jigawa ta ƙaddamar da wani kwamiti mai mahimmanci da ake kira Multi-Sectoral Coordination Steering Committee domin jagorantar aiwatar da shirin Nigeria for Women Programme (NFWP), wani haɗin gwiwa ne tsakanin Bankin Duniya!-->…
Tinubu Ya Lalata Tattalin Arzikin Najeriya Fiye Da Yanda Buhari Ya Lalata Shi – Hakeem Baba-Ahmed
Tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara a ofishin mataimakin shugaban ƙasa kan al’amuran siyasa, Dr Hakeem Baba-Ahmed, ya caccaki gwamnatin Tinubu, yana mai cewa tattalin arziƙin Najeriya ya taɓarɓare fiye da yadda Muhammadu Buhari ya bar shi.!-->…
EFCC Ta Fara Bincike Kan Tsoffin Shugabannin NNPC Kan Badaƙalar Dubunnan Biliyoyi
Hukumar EFCC ta fara bincike mai zurfi kan zargin almundahana da amfani da ofis ba bisa ƙa’ida ba da ake yi wa wasu tsoffin manyan jami’an Kamfanin Mai na Ƙasa (NNPC), ciki har da tsohon GMD, Mele Kyari, da Abubakar Yar’Adua.
A wata!-->!-->!-->…
Darajar Naira Ta Ƙara Faɗuwa A Kasuwar Gwamnati
Naira ta sake fuskantar zubewar daraja a kasuwar musayar kudade ta hukuma a ranar Jumma’a, inda ta faɗo zuwa N1,602.18 a kan kowace dala, wanda hakan ke nuni da faɗuwar N5.49 daga yadda take a baya.
Bayanai daga shafin yanar gizo na!-->!-->!-->…
RIKICIN SARAUTA: Sarki Sunusi Da Sarki Aminu Sun Naɗa Galidiman Kano Daban-Daban
Masarautar Kano ta shiga wani sabon yanayi na ban mamaki bayan da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, da Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, suka naɗa mutane biyu daban-daban a matsayin Galadiman Kano a rana ɗaya.
Aminu Ado Bayero!-->!-->!-->…
Gwamna Abba Kabir Zai Samu Goyon Bayan Ma’aikatan Jihar Domin Yin Tazarce
Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya reshen Jihar Kano (NLC) ta bayyana goyon bayanta ga Gwamna Abba Kabir Yusuf domin ya ci gaba da mulki a karo na biyu, tana mai yabawa da kishinsa ga jin daɗin ma’aikata da ƴan ritaya a jihar.
Shugaban NLC na!-->!-->!-->…
Shugabannin Jami’o’i Da Shugaban NELFUND Zasu Gurfana Kan Zargin Satar Kuɗin Ɗalibai
Gwamnatin Tarayya ta gayyaci wasu shugabannin jami’o’i da kuma Babban Daraktan Asusun Rancen Dalibai na Ƙasa (NELFund) domin tattauna zargin karkatar da kuɗaɗen da aka ware don tsarin bayar da rancen karatu ga ɗalibai.
Wannan matakin ya!-->!-->!-->…
Yanda Ƴanbindiga Suka Kashe Liman Da Ƴaƴansa Biyu Da Jikansa Ɗan Shekara Biyu
Ɗan surukin tsohon babban Limamin Maru da ke ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara, Alƙali Salisu Suleiman, ya bayyana yanda ƴanbindiga suka kashe limamin tare da ƴaƴansa biyu da jikansa ɗan shekara biyu a hannun su bayan garkuwa da su.
!-->!-->!-->…
Hukumar FBI Da Ta Hana Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ta Amurka Sun Nemi Ƙarin Kwanaki Kafin Fallasa…
Hukumar FBI da ta hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta DEA a Amurka sun roƙi kotun tarayya da ke birnin Washington D.C. da ta ba su ƙarin kwanaki 90 domin kammala bincikensu kan batun da ya shafi zargin safarar miyagun kwayoyi da aka!-->…
Sama Da Mutum Dubu Sun Kamu Da Cutar Amai Da Gudawa A Najeriya, Wasu Sun Mutu, In Ji NCDC
Hukumar NCDC ta bayyana cewa an samu ƙaruwar yaɗuwar cutar amai da gudawa (cholera) a faɗin Najeriya, inda aka rawaito cewa, akwai mutum 1,307 da ake zargi da kamuwa da cutar da kuma mutuwar wasu 34 a jihohi 30 tun daga farkon shekarar!-->…
Na Ceto Tsarin Fanshon Jigawa Daga Rugujewa – Gwamna Namadi
Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta fitar da sama da naira biliyan bakwai domin ceton tsarin fansho na hadin gwiwa tsakanin jihar da ƙananan hukumomi daga rushewa, yana mai cewa “ya kamata a fahimta cewa!-->…