Sign in
Sign in
Recover your password.
A password will be e-mailed to you.
Browsing Category
Labarai
Sabbin labarai daga gida da waje cikin Hausa, tare da bayanai masu zurfi da gaskiya. Muna kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya, Arewa da sauran duniya cikin lokaci. Karanta takaitattun rahotanni, bincike da kwakkwaran bayani.
‘Dole Ne Mu Yi Amfani Da Tattaunawa’ – Bola Tinubu A Buɗe Taron ECOWAS Na 2 Kan Juyin Mulki A Nijar
Shugaban Najeriya, kuma Shugaban Ƙungiyar Bunƙasa Tattalin Arziƙin Africa ta Yamma, Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da jawabin buɗe taron ECOWAS karo na biyu kan juyin mulkin da sojoji suka yi a Jamhuriyar Nijar.
A cikin jawabin nasa,!-->!-->!-->…
Ƴan Najeriya Sun Kashe Naira Tiriliyan 3.33 A Kira Da Data A 2022
Ƴan Najeriya da sauran masu amfani da netwok a Najeriya sun kashe naira tiriliyan 3.33 a kira, saka data, tura saƙon kar ta kwana da sauran abubuwan da ake da netwok a cikin shekarar 2022, in ji Hukumar Sadarwa ta Najeriya, NCC.
Wannan!-->!-->!-->…
Ɗan Majalissar Jiha Ya Samar Da Wutar Sola A Babban Masallacin Birnin Kudu
Ɗan Majalissar Jiha mai wakiltar, Mazaɓar Birnin Kudu a Majalissar Jihar Jigawa, Muhammad Kabir Ibrahim ya samar da hasken wutar lantarki a Babban Masallacin Birnin Kudu.
Ɗan Majalissar ya samar da wutar ne ta hanyar sanya kayan samar!-->!-->!-->…
Ɗan Majalissar Wakilai Zai Raba Kayan Abinci Ga Zawara 2,000
Ɗan Majalissar Wakilai mai wakiltar Darazo da Ganjuwa daga Jihar Bauchi, Mansur Manu Soro ya ce, zai samar da kayan abinci kyauta ga zawara 2,000 a mazaɓarsa.
Ɗan majalissar ya bayyana hakan ne ga jaridar DAILY TRUST a jiya Laraba, a!-->!-->!-->…
Jihar Kano Na Buƙatar A Cire Jihohi 2 Daga Cikinta – Sanata Doguwa
Mataimakin Shugaban Majalissar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya tabbatarwa da masu neman Jihar Tiga da Jihar Gari daga cikin Jihar Kano cewar, Majalissar Tarayya za tai musu adalci a lokacin gyaran kundin tsarin mulki.
Sanata Barau!-->!-->!-->!-->!-->…
JUYIN MULKI: Sarki Sunusi Lamido Ya Haɗu Da Sojoji Masu Mulkin Nijar
Sarkin Kano Mai Murabus, Alhaji Muhammadu Sunusi ya haɗu da shugabannin mulkin soja na Nijar a ƙasar ta Nijar ana tsaka da matsin lamba kan a dawo da Shugaba Mohammed Bazoum.
Sarkin wanda tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN ne,!-->!-->!-->…
‘Tana Kirana Ne Kaɗai Idan Tana Buƙatar Kuɗi,’ In Ji Wanda Yai Wa Budurwarsa Kisan Gilla
Wani matashi ɗan shekara 45 mai suna Bankole Oginni, wanda ƴansanda suka kama a Jihar Ondo bisa zargin kashe tsohuwar budurwarsa, ya bayyana dalilan da suka sa ya aikata aika-aikar.
Wanda ake zargin dai ya aikata laifin ne a gidansa da!-->!-->!-->…
An Gwangwaje Sanatoci Da Kuɗaɗe Domin Su Ji Daɗin Yin Hutunsu
Shugaban Majalissar Dattawa, Godswill Akpabio ya faɗawa sanatoci cewar, Magatakardar Majalissar Tarayya zai tura musu wasu kuɗaɗe a asusunsu na banki domin su ji daɗin yin hutun da zasu shiga.
A wani bidiyo da ya zagaya yanar gizo a yau!-->!-->!-->…
Mamakon Ruwan Sama Ya Kashe Mutane 33 Tare Da Ɓatar Da 18 A Beijing
Wani mamakon ruwan saman da ba a taɓa ganin irinsa ba a Beijing ta Ƙasar China a yau Laraba, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 33 da kuma ɓatar da wasu su 18, in ji jami’an gwamnatin ƙasar.
Jami’an sun ƙara da cewar, mamakon ruwan saman!-->!-->!-->…
Yawan Dogaro Da Bashi Ya Zo Ƙarshe A Najeriya – Tinubu
A jiya Talata ne a Abuja, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Tsare-tsaren Kashe Kuɗaɗe da Sake Fasalin Karɓar Haraji, inda ya ce, yawan dogaro da bashi wajen kashe kuɗaɗen gudanar da gwamnati ya zo!-->…
Bankin Duniya Ya Dakatar Da Bai Wa Uganda Bashi Saboda Dokar Hana Auren Jinsi
Bankin Duniya ya sanar da cewar zai dakatar da bai wa ƙasar Uganda sabon bashi saboda dokar hana auren jinsi da ƙasar ta samar.
Bankin da ke birnin Washington ya bayyana hakan ne a jiya Talata, inda ya ce, zai dena biyan kuɗaɗen aiwatar!-->!-->!-->…
Amurka Ta Ce In Aka Takura Mata Zata Mamayi Nijar
Ƙasar Amurka ta yi gargaɗi ga sojojin da ke mulki a Nijar da cewar, matuƙar ba a dawo da bin kundin tsarin mulkin ƙasar ba, to zata mamaye ƙasar.
Mai Riƙon Muƙamin Mataimakiyar Sakatariyar Harkokin Waje ta Amurka, Victoria Nuland ce ta!-->!-->!-->…
DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnati Ta Kammala Ɗaukar Sabbin Immigration Da Civil Defence, Ta Saki Sunayen…
Hukumar Kula da Jami’an Civil Defence, Masu Kula da Gidan Gyaran Hali, Masu Kashe Gobara da kuma Masu Kula da Shige da Fice, CDCFIB, ta saki sunayen waɗanda suka samu nasarar samun aikin Immigration, da Civil Defence.
An bayyana wannan!-->!-->!-->…
Tinubu Ya Haɗu Da Okonjo Iweala A Aso Rock
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana ganawa da Babbar Daraktar Hukumar Kasuwanci ta Duniya, WTO, Farfesa Ngozi Okonjo Iweala a Fadar Shugaban Ƙasa, Villa da ke Abuja.
Farfesa Okonjo Iweala dai ta iso Fadar Shugaban Ƙasa ne da misalin!-->!-->!-->…
PDP Ta Ƙirƙiri Kwamiti Na Musamman Kan Zaɓen Jihohin Bayelsa, Imo Da Kogi
A daidai lokacin da zaɓen gwamnoni na ranar 11 ga watan Nuwamba wanda za a yi a jihohin Bayelsa, Imo da Kogi ke ƙara ƙuratowa, Jam’iyyar PDP ta ƙirƙiri kwamiti na musamman kan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a kan manufofin jam’iyyar da!-->…
Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga 3, Sun Ƙwato Makamai A Kaduna
Rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarunta da ke 1 Division sun kashe ƴan bindiga uku tare da ƙwato makamai da sauran abubuwa a Ƙaramar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.
A wata sanarwa da Musa Yahaya, mai riƙon Mataimakin Darakta kan Hulɗa!-->!-->!-->…
Kotu Ta Ce A Ci Gaba Da Tsare Wanda Ake Zargi Da Satar Ganda A Kano
An gurfanar da wani matashi ɗan shekara 23 mai suna Abdulwahab Yusuf a wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kano bisa zarginsa da satar fatar shanu wadda aka fi sani da ganda, wadda kuɗinta ya kai naira 8,500.
Ana tuhumar!-->!-->!-->…
JERIN SUNAYE: Jigawa Ta Samu Shugabannin Kwamitoci 2 Yayin Da Majalissar Sanatoci Ta Bayyana Sunayen…
An saki sunayen shugabannin kwamitocin dindindin na Majalissar Sanatoci jim kaɗan bayan sanatocin sun fitar da jerin sunayen ministocin Shugaba Tinubu da suka aminta da su.
Cikin jerin sunayen shugabannin kwamitocin sanatocin akwai!-->!-->!-->…
Wani Babban Ma’aikaci Ya Tona Asirin Karɓar Cin Hanci Don A Bayar Da Aikin Gwamnati
Wani tsohon ma’aikacin ofishin kula da manhajar biyan albashi ta IPPIS a Hukumar Raba Dai-dai ta Gwamnatin Tarayya, FCC, Haruna Kolo, wanda aka zarga da karɓar cin hanci kafin ya bayar da aiki, ya amsa laifinsa.
Ya amsa cewar, ya karɓi!-->!-->!-->…
Sojojin Nijar Sun Naɗa Wani Masanin Tattalin Arziƙi A Matsayin Firaminista
Kusan mako biyu da sojoji suka karɓe mulkin Jamhuriyar Nijar, masu juyin mulkin sun bayyana sunan tsohon ministan tatattalin arziƙi, Ali Mahamman Lamine Zeine a matsayin sabon firaministan ƙasar.
A jiya da daddare ne, mai magana da!-->!-->!-->…