Sign in
Sign in
Recover your password.
A password will be e-mailed to you.
Browsing Category
Labarai
Sabbin labarai daga gida da waje cikin Hausa, tare da bayanai masu zurfi da gaskiya. Muna kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya, Arewa da sauran duniya cikin lokaci. Karanta takaitattun rahotanni, bincike da kwakkwaran bayani.
‘Zai Iya Zamewa Yaƙi,’ Burkina Faso Da Mali Sun Goyi Bayan Sojojin Nijar Sun Kuma Gargaɗi ECOWAS
Sojojin da ke mulki a Burkina Faso da Mali sun yi gargaɗi kan yunƙurin amfani da ƙarfin soji a kan sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar, inda suka ce yin hakan tsokanar yaƙi ce a Afirka ta Yamma.
Gargaɗin wanda ya zo a wata sanarwar!-->!-->!-->…
JIGAWA: Gwamna Namadi Ya Cire Shugabannin Asibitin Gumel
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi ya amince da hukuncin ladabtarwa ga jagororin Babban Asibitin Gumel da ke Jihar Jigawa.
Wannan na zuwa ne bayan ziyarar bazata da gwamnan ya kai Babban Asibitin a ranar Juma’ar da ta gabata, inda!-->!-->!-->…
Ka Gaggauta Ceton Miliyoyin Mutane Daga Matsananciyar Yunwa – Dattawan Arewa Ga Tinubu
Ƙungiyar Dattawan Arewa, NEF, ta buƙaci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta yin hoɓɓasa wajen ceton miliyoyin ƴan Najeriya daga cikin matsananciyar yunwa da wahalar da suke ciki.
Dattawan Arewan dai sun bayar da wannan!-->!-->!-->…
A Ƙarshe Dai, Tinubu Ya Tare Villa
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a ranar Lahadin da ta gabata ya tare a ɗaya daga cikin gidajen da ke Gidan Shugaban Ƙasa, Villa, Abuja, wanda aka fi sani da Gidan Gilas (Glass House).
A baya dai, Shugaban yana zuwa ofis ne domin yin!-->!-->!-->…
Ƴan Ƙwadago Sun Kushe Jawabin Tinubu, Sun Ce Fita Zanga-Zanga Tana Nan Daram A Gobe Laraba
Ƙungiyoyin ƙwadago sun nuna rashin gamsuwarsu da gaskiyar tsare-tsaren tallafin da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya faɗa a jawabin da yai wa ƴan Najeriya kan magance matsalolin da tsare-tsaren gwamnatinsa suka jawowa ƴan ƙasa.
!-->!-->!-->…
Mutane 83 Sun Mutu, 836 Sun Kamu Yayinda Cutar Diphtheria Ta Yaɗu A Jihohi 8 Na Najeriya
Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Ƙasa, NPHCDA, ta ce, an samu mutuwar mutane 83 a Najeriya yayinda mutane 836 suka kamu da cutar diphtheria daga farkon wannan shekarar kawo yanzu.
Babban Daraktan Hukumar, Faisal Shuaib ne ya!-->!-->!-->…
TANTANCE MINISTOCI: Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Takurawa Wike Ba – Akpabio
Shugaban Majalissar Dattawa, Godswill Akpabio ya bayyana dalilin da ya sa sanatocin ba su takurawa tsohon Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike ba a lokacin da suka tantance shi domin a naɗa shi minista.
Akpabio ya bayyana ƙwarewar Wike a!-->!-->!-->…
DA ƊUMI-ƊUMI: Jihar Lagos Ta Rage Kuɗin Hawa Mota Da Kaso 50%
A ƙoƙarinta na rage raɗaɗin janye tallafin man fetur, Gwamnatin Jihar Lagos ta rage kuɗin hawa mota a dukkan motocin haya mallakar jihar da kaso 50 cikin 100, yayinda kuma tai alƙawarin raba kayan abinci ga marassa ƙarfi a jihar.
Da!-->!-->!-->…
DA ƊUMI-ƊUMI: Tinubu Ya Ce Manyan Makarantu Su Dakatar Da Ƙarin Kuɗin Makarantar Da Suka Yi
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci shugabannin makarantun gaba da sikandire na Gwamnatin Tarayya da su guji ƙarin kuɗaɗen makaranta da ake biya da kuma duba yiwuwar gujewa ƙarin a nan gaba don kar iyaye su fuskanci ƙarin shiga cikin!-->…
Tsohon Rijistaran NECO Ya Zama Shugaban Jami’ar Khalifa Isyaka Rabiu University
Tsohon Shugaban Hukumar Shirya Jarabawa ta Ƙasa, NECO, Farfesa Abdulrashid Garba ya zama Shugaban Jami’ar Khalifa Isyaka Rabiu University, KHAIRUN, na farko.
KHAIRUN dai na ɗaya daga cikin sabbin jami’o’i masu zaman kansu a Kano da suka!-->!-->!-->…
Ƴansanda Sun Kama Ɓarayin Babura A Bauchi
Jami’an ƴansanda a Jihar Bauchi sun sami nasarar kama wasu mutane guda biyu waɗanda ake zargi da sun ƙware wajen ƙwatar babura daga masu su a yankin Gudum Hausawa da ke jihar.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar Ƴansandan Jihar Bauchi,!-->!-->!-->…
Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya Zasu Rubuta Jarabawar Ƙarin Girma A Agusta
Za a fara rubuta jarabawar neman ƙarin girma ta ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ta bana a ranar 14 ga watan Agusta, kamar yanda sanarwa da Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ta fitar.
Sanarwar mai ɗauke da kwanan watan 28 ga!-->!-->!-->…
EU Ta Dakatar Da Tallafin Da Ta Ke Bai Wa Jamhuriyar Nijar
Ƙungiyar Tarayyar Turai, EU, ta ce ta dakatar da duk wani tallafi na kuɗi da take bai wa Nijar tare da yanke duk wata hulɗa a kan abin da ya shafi tsaro a tsakaninta da ita, biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasar.
!-->!-->!-->…
DA ƊUMI-ƊUMI: Shugaba Tinubu Zai Yi Wa Ƴan Ƙasa Jawabi Yau
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai yi wa ƴan ƙasa jawabi yau Litinin 31 ga watan Yuli, 2023 da misalin ƙarfe 7 na dare.
Mai Magana da Yawun Shugaban Ƙasa, Dele Alake ne ya sanar da hakan a safiyar yau.
Alake ya yi kira ga gidajen!-->!-->!-->!-->!-->…
YANZU-YANZU: Alƙalin Kotun Ƙolin Najeriya Ya Rasu
An rawaito cewa, Justice Chima Centus Nweze na Kotun Ƙolin Najeriya ya rasu a jiya Lahadi yana da shekaru 64 a duniya.
Har kawo yanzu dai Kotun Ƙolin ba ta sanar da mutuwar alƙalinba a hukumance.
In za a iya tunawa, Justice Nweze ne!-->!-->!-->!-->!-->…
Waɗanda Tinubu Zai Naɗa Ministoci Su 15 Ne Kaɗai Daga 28 Suka Gabatar Da Takardunsu
Aƙalla waɗanda za a naɗa ministoci 15 ne suka gabatar da takardunsu ga ofishin Babban Mai Temakawa Shugaban Ƙasa kan Harkokin Majalissar Dattawa, Abdullahi Gumel zuwa jiya Lahadi.
Waɗansu daga cikin waɗanda sunayensu suka fito a waɗanda!-->!-->!-->…
Yau Sabbin Ministocin Tinubu Zasu Fara Fuskantar Tantancewar Majalissar Dattawa
A yau Litinin ne Majalissar Dattawa zata fara tantance ingancin waɗanda Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ke son naɗawa ministoci.
A ranar Alhamis da ta gabata ne, Shugaban Majalissar Dattawa ya karanta sunayen mutane ashirin da takwas!-->!-->!-->…
Muna Nan Kan Bakanmu, Babu Wani Umarnin Kotu Da Ya Hana Mu Yin Zanga-Zanga – NLC
Ƙungiyar Ƙwadago, NLC, ta faɗawa Mai Shigar da Ƙara na Gwamnatin Tarayya kuma Babban Sakataren Ma’aikatar Shari’a cewa, babu wani umarnin kotu daga Kotun Ma’aikata ta Ƙasa ko wata kotu da ya hana ma’aikata ƴan Najeriya shiga cikin!-->…
Ko Kun San Ƙarancin Bacci Kan Jawo Yawan Ƙiba?
Masu karatu, ko kuna fama da karancin barci? Wani sabon nazari ya nuna mana cewa, wadanda ba sa samun isasshen barci su kan yi teba, wanda hakan ka iya zai illanta lafiyarsu.
Wata tawagar kasa da kasa karkashin shugabancin kwalejin!-->!-->!-->…
Atiku, Gwamnoni Da Manyan PDP Sun Tattauna Kan Makomar Jam’iyyar
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, a zaɓen da ya gabat, Atiku Abubakar da wasu daga cikin gwamnonin da aka zaɓa ta jam’iyyar sun fara tuntuɓa kan makomar jam’iyyar.
Abubuwan da aka tattauna a zaman na sirri da aka gudanar a!-->!-->!-->…