Sign in
Sign in
Recover your password.
A password will be e-mailed to you.
Browsing Category
Labarai
Sabbin labarai daga gida da waje cikin Hausa, tare da bayanai masu zurfi da gaskiya. Muna kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya, Arewa da sauran duniya cikin lokaci. Karanta takaitattun rahotanni, bincike da kwakkwaran bayani.
Libya Zata Gudanar Da Zaɓen Da Zai Iya Nuna Makomar Haɗin Kan Gabashi Da Yammacin Ƙasar
Libya na shirin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a gobe Asabar, wani abin gwaji ga demokaraɗiyya a ƙasar da ke cike da rarrabuwar kai da rashin tsaro, kamar yadda AFP ta rawaito.
Muhimman biranen gabas da suka haɗa da Benghazi, Sirte!-->!-->!-->…
NELFUND Ya Fitar Da Sabon Bayani Kan Kuɗaɗen Da Yake Bai Wa Ɗalibai
Asusun Lamunin Dalibai na Ƙasa (NELFUND) ya ce ya riga ya raba naira biliyan 86 don tallafa wa ɗalibai 449,000 cikin buƙatu 735,000 da aka samu zuwa yau, kamar yadda Akintunde Sawyerr ya bayyana a shirin Sunrise Daily na Channels!-->…
Jihohin Arewa Na Ƙara Ƙuntata Rayuwar Dattawa Ƴan Fansho Da Ɗan Mitsitsin Kuɗin Fansho
Binciken Daily Trust ya gano cewa jihohi da dama a Arewacin Najeriya har yanzu na biyan fanshon da ya yi matuƙar ƙasa da sabon mafi ƙanƙantar kuɗin fansho na tarayya na ₦32,000, abin da ya bar dubban tsoffin ma’aikata cikin tsananin zafin!-->…
DSS Sun Yi Babban Kamu, Sun Kama Wani Ƙasurgumin Shugaban Ƴan Ta’adda
Daily Trust ta tabbatar da cewa Abubakar Abba, jagoran sabuwar ƙungiyar ta’addanci mai suna Mahmuda, yana hannun Hukumar Tsaro ta DSS bayan an cafke shi a Jihar Neja.
An gano cewa wannan shugaban ta’addanci, wanda jami’an sirri suka!-->!-->!-->…
Wata Kotu Ta Bayyana APC Da PDP A Matsayin Ƙaungiyoyin Ƴan Ta’adda Sai Dai PDP Ta Musanta
PDP ta ƙaryata rahotannin cewa wata Kotun Tarayya a Kanada ta ayyana PDP da APC a matsayin ƙungiyoyin ta’addanci, inda gwamnatin tarayya ke shirin fitar da martani a yau, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Mamba a Kwamitin Zartarwa,!-->!-->!-->…
Tashin Hankali A PDP: Shugabancin Jam’iyyar Ya Barranta Kansa Da Batun Neman Komawar Jonathan Da…
Tashin hankali ya sake kunno kai a jam’iyyar PDP yayin da ake tunkarar zaɓen shugaban ƙasa na 2027, bayan labarin cewa wasu manyan ƴan jam’iyyar na ƙoƙarin mayar da tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa!-->…
A Yau Alhamis Tinubu Zai Lula Ƙasashen Waje Don Gudanar Da Wasu Ayyukan Gwamnatinsa
Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, zai fara ziyarar ƙasashen Japan da Brazil daga ranar Alhamis, tare da tsayawa kaɗan a Dubai, UAE, domin halartar taron TICAD9 a Yokohama, Japan daga 20 zuwa 22 ga Agusta.
An shirya taron ne da taken!-->!-->!-->…
NBA Dutse Ta Alƙawarta Inganta Ayyukan Lauyoyi Don Hanzarta Yanke Shari’a A Jigawa
Daga: Mika'il Tsoho, Dutse
Rashen ƙungiyar lauyoyi ta NBA a Dutse, Jigawa, ya alƙawarta inganta ƙa’idojin aiki da riƙon gaskiya tsakanin lauyoyi domin hanzarta shari’a a jihar.
Shugaban reshen, Mustapha M. Kashim, ya bayyana hakan!-->!-->!-->!-->!-->…
FIRS, Customs, NUPRC, NIMASA, da NNPC Zasu Fuskanci Cikakken Bincike Kan Hada-Hadar Kuɗaɗensu
Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya umarci a gudanar da cikakken bincike kan dukkan cire kuɗaɗe da tsarin riƙe kudade da hukumomin tara kuɗaɗe ke yi, ciki har da FIRS, Customs, NUPRC, NIMASA, da NNPC.
Wannan mataki na nufin ƙara adana!-->!-->!-->…
Gwamnatin Tarayya Za ta Gina Tashoshin Mota A Jihohi 6 Kan Naira Biliyan 142
Gwamnatin Tarayya ta amince da gina sabbin tashoshin mota a kowane yanki shida na Najeriya, a kan kuɗi N142,028,576,008.17, wanda zai inganta sufuri da rage haɗura a kan manyan tituna.
Ministan Sufuri, Sanata Sa’idu Alkali, ya bayyana!-->!-->!-->…
DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Kafa Sabbin Jami’o’i Da Kwalejoji Na Shekaru Bakwai
Gwamnatin Tarayya ta sanar da dakatar da kafa sabbin jami’o’i, kwalejoji, da polytechnics na tsawon shekaru bakwai domin magance raguwar inganci da rashin kayan more rayuwa a ɓangaren ilimin manyan makarantu.
Ministan Ilimi, Dr. Tunji!-->!-->!-->…
Tsoron Boko Harama Ya Sa Ɗaruruwan Ƴan Najeriya Tafiya Kamaru Domin Kwana A Kan Tituna
Ɗaruruwan mazauna Kirawa a jihar Borno da Boko Haram suka raba da muhallansu sun koka kan halin ƙuncin rayuwa, inda suka bayyana cewa suna kwana a Kamaru cikin tsoron hare-haren mayaƙa sannan su dawo Najeriya da safe.
Sun bayyana wa!-->!-->!-->…
Jam’iyyu A Kano Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya Kafin Zaɓen Cike Gurbin Ranar Asabar
Shugabannin jam’iyyun siyasa a jihar Kano sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya domin tabbatar da gudanar da zaɓukan cike gurbi cikin lumana a ranar Asabar, 16 ga Agusta 2025.
Kakakin rundunar ƴan sandan a jihar, SP Abdullahi!-->!-->!-->…
Majalissa Na Shirin Sauya Tsarin Shari’ar Zaɓen Gwamna Ta Yanda Zata Na Ƙarkewa Kafin Kotun Ƙoli
Wani ɗan majalisar wakilai, Bayo Balogun, ya bayyana cewa za a yi gyara ga kundin tsarin mulkin Najeriya domin sanya Kotun Daukaka Ƙara a matsayin matakin ƙarshe na sauraron ƙarar zaɓen gwamna a ƙasar.
Balogun, wanda shi ne shugaban!-->!-->!-->…
Tinubu Ya Naɗa Sabbin Shugabanni A Hukumar NCC Da Asusun USPF
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana sababbin naɗe-naɗe a hukumar Nigerian Communications Commission (NCC) da Universal Service Provision Fund (USPF) domin ƙara inganta aikin fasahar sadarwa da isar da intanet a yankunan karkara.
!-->!-->!-->…
Ƙananan Yara Na Fuskantar Gargaɗin Ƴan Sanda A Kano Saboda Tuƙa Adaidaita Sahu
Rundunar Ƴan Sanda a Jihar Kano ta yi kira mai ƙarfi ga masu keke Napep, musamman ƙananan yara, da kuma direbobi masu karya dokar fitilun kan hanya.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce ana samun “tuƙin ganganci” daga!-->!-->!-->…
Jihohi Da Yankunan Da Sabbin Manyan Sakatarorin Gwamnatin Tarayya Da Za A Naɗa Zasu Fito
Gwamnatin Tarayya ta fara aikin naɗa sabbin manyan sakatarori biyar, uku daga cikinsu za su jagoranci sababbin ma’aikatun da aka samar.
Wata wasiƙa daga Ofishin Shugaban Ma’aikata ta bayyana cewa wannan dama ce ga manyan daraktoci da ke!-->!-->!-->…
JAMB Zata Hana Wasu Manyan Makarantu Ɗaukar Sabbin Ɗalibai
Hukumar JAMB ta yi gargaɗin cewa ba za ta amince da ɗaukar ɗalibai na shekarar karatu ta 2024 da 2025 ba ga kowace makaranta da ta ƙi tura jerin sunayen sabbin ɗaliban da ta ɗauka.
Wannan matakin, wanda ya samo asali daga umarnin!-->!-->!-->…
Gwamnati Tarayya Zata Kori Ma’aikata 3,598, Ta Kira Su Tantancewa
Hukumar Kula da Ayyukan Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya (FCSC) ta fitar babban gargaɗi ga ma’aikata 3,598 da suka ƙi zuwa tantancewa a 2021, tana mai cewa duk wanda ya sake ƙin zuwa wannan lokaci za a ɗauka yana da takardun bogi ne.
Wannan!-->!-->!-->…
An Kama Wasu Masu Garkuwa Da Mutane Yayin Da Suke Raba Kuɗi
Rundunar Ƴan Sanda a Jihar Ondo ta cafke mutane uku da ake zargi da garkuwa da ma’aikatan Jami’ar Adekunle Ajasin, Akungba-Akoko.
Waɗanda aka sace sun haɗa da Omoniyi Eleyinmi, jami’in kula da harkokin gudanarwa na Kwalejin Ilimi, da!-->!-->!-->…