Sign in
Sign in
Recover your password.
A password will be e-mailed to you.
Browsing Category
Labarai
Sabbin labarai daga gida da waje cikin Hausa, tare da bayanai masu zurfi da gaskiya. Muna kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya, Arewa da sauran duniya cikin lokaci. Karanta takaitattun rahotanni, bincike da kwakkwaran bayani.
Tinubu Ya Naɗa Sabbin Shugabanni A Hukumar NCC Da Asusun USPF
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana sababbin naɗe-naɗe a hukumar Nigerian Communications Commission (NCC) da Universal Service Provision Fund (USPF) domin ƙara inganta aikin fasahar sadarwa da isar da intanet a yankunan karkara.
!-->!-->!-->…
Ƙananan Yara Na Fuskantar Gargaɗin Ƴan Sanda A Kano Saboda Tuƙa Adaidaita Sahu
Rundunar Ƴan Sanda a Jihar Kano ta yi kira mai ƙarfi ga masu keke Napep, musamman ƙananan yara, da kuma direbobi masu karya dokar fitilun kan hanya.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce ana samun “tuƙin ganganci” daga!-->!-->!-->…
Jihohi Da Yankunan Da Sabbin Manyan Sakatarorin Gwamnatin Tarayya Da Za A Naɗa Zasu Fito
Gwamnatin Tarayya ta fara aikin naɗa sabbin manyan sakatarori biyar, uku daga cikinsu za su jagoranci sababbin ma’aikatun da aka samar.
Wata wasiƙa daga Ofishin Shugaban Ma’aikata ta bayyana cewa wannan dama ce ga manyan daraktoci da ke!-->!-->!-->…
JAMB Zata Hana Wasu Manyan Makarantu Ɗaukar Sabbin Ɗalibai
Hukumar JAMB ta yi gargaɗin cewa ba za ta amince da ɗaukar ɗalibai na shekarar karatu ta 2024 da 2025 ba ga kowace makaranta da ta ƙi tura jerin sunayen sabbin ɗaliban da ta ɗauka.
Wannan matakin, wanda ya samo asali daga umarnin!-->!-->!-->…
Gwamnati Tarayya Zata Kori Ma’aikata 3,598, Ta Kira Su Tantancewa
Hukumar Kula da Ayyukan Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya (FCSC) ta fitar babban gargaɗi ga ma’aikata 3,598 da suka ƙi zuwa tantancewa a 2021, tana mai cewa duk wanda ya sake ƙin zuwa wannan lokaci za a ɗauka yana da takardun bogi ne.
Wannan!-->!-->!-->…
An Kama Wasu Masu Garkuwa Da Mutane Yayin Da Suke Raba Kuɗi
Rundunar Ƴan Sanda a Jihar Ondo ta cafke mutane uku da ake zargi da garkuwa da ma’aikatan Jami’ar Adekunle Ajasin, Akungba-Akoko.
Waɗanda aka sace sun haɗa da Omoniyi Eleyinmi, jami’in kula da harkokin gudanarwa na Kwalejin Ilimi, da!-->!-->!-->…
EFCC Ta Tsare Tsohon Gwamnan Sokoto Tambuwal Kan Zargin Cire Biliyoyin Nairori
Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya shiga hannun hukumar EFCC inda aka yi masa tambayoyi kan zargin cire kuɗaɗen gwamnati har Naira biliyan 189 a yanayin da ya saɓa da dokar hana safarar kuɗi ta 2022.
Rahotanni sun!-->!-->!-->…
Sankara Ya Raba Naira Miliyan 50 Ga Matasa Da Mata 250 A Ƙaramar Hukumarsa
Daga: Mika'il Tsoho, Dutse
A ƙalla matasa da mata 250 a Jihar Jigawa sun amfana da tallafin kuɗi har Naira miliyan 50 daga Kwamishinan Harkokin Jin Ƙai da Ayyuka na Musamman, Hon. Auwal Sankara, a wani shirin ƙarfafa tattalin arziki da!-->!-->!-->…
Jihohi da Yawan Masu Nema: Masu Neman Aiki Miliyan 1.91 Na Rige-Rigen Samun Aikin Para-Military A…
Hukumar Civil Defence, Correctional, Fire and Immigration Services Board (CDCFIB) ta bayyana cewa sama da masu neman aiki miliyan 1.91 ne suka yi rajista don neman guraben aiki a hukumomin tsaro na para-military a wannan shekarar.
!-->!-->!-->…
Babu Gaskiya a Jita-Jitar Rashin Lafiyar Tinubu – Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yi Zazzafan Raddi
Mai taimaka wa Shugaba Bola Tinubu kan harkokin wallafa, AbdulAziz AbdulAziz, ya ƙaryata rahoton wata jaridar yanar gizo, International Centre for Investigative Report (ICIR), da ta yi zargin cewa shugaban ƙasa yana fama da rashin lafiya.
!-->!-->…
ADC Ta Zargi EFCC da Yin Aiki Kamar Rundunar Farautar Abokan Hamayyar APC
Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta zargi hukumar EFCC da yin bincike bisa son rai da kuma zama tamkar rundunar farautar abokan hamayya ga jam’iyyar APC mai mulki.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar na!-->!-->!-->…
Shin Jonathan Na Da Hurumin Tsayawa Takara A 2027? Nazarin Dokar 2017 Da Hukuncin Kotu Na 2022
Yayin da ake ci gaba da hasashe kan zaɓukan shugaban ƙasa na 2027, TIMES NIGERIA ta kalli tushen doka kan wata muhimmiyar tambaya: shin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan zai iya sake tsayawa takara?
Muhawarar ta ta’allaƙa ne kan!-->!-->!-->…
Siyasar 2027: Shin Atiku Ya Jinkirta Shiga ADC Saboda Raɗe-Raɗin Jonathan Ne Zai Yi Mata Takara?
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya jinkirta shirin karɓar katin shaidar zama ɗan jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), a daidai lokacin da ake raɗe-raɗin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan na shirin yin takarar!-->…
Zargin Kisa: Wanda Ake Tuhuma Da Kashe Jami’in Civil Defense Ya Mutu Yayin Yunƙurin Tserewa
Daga: Mika'il Tsoho, Dutse
Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) ta bayyana kama wani mai suna Salisu Muhd mai shekaru 45, da ake zargi da hannu a kisan gilla da aka yi wa jami’insu, Bashir Adamu Jibrin, a kasuwar Shuwarin a!-->!-->!-->…
ASUU Za Ta Tsunduma Sabon Yajin Aiki, Ta Ce Malamai Na “Koyarwa Cikin Yunwa”
Ƙungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya (ASUU) ta yi gargaɗin cewa za ta sake tsunduma yajin aiki na ƙasa baki ɗaya idan gwamnati ta gaza magance matsalolin da suka daɗe suna addabarta da suka haɗa da rashin biyan haƙƙoƙi, lalacewar kayan!-->…
Dalilin Da Ya Sa Najeriya Ke Bayar Da Lantarki Ga Ƙasashen Waje Duk Da Miliyoyin Mutane Na Cikin…
Najeriya na ƙara ƙaimi wajen karkata ga amfani da makamashi mai tsabta tare da kare matakin ta na tura wutar lantarki zuwa ƙasashe makwabta duk da cewa miliyoyin ƴan ƙasa ba su da isasshiyar wutar.
Daraktan Hukumar Makamashi ta Ƙasa!-->!-->!-->…
An Ƙulla Wata Sabuwar Hulɗa Da Birtaniya Don Ƙarfafa Ilimi a Najeriya
Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya bayyana farin ciki kan ƙulla yarjejeniya tsakanin Jami’ar Legas (UNILAG) da Jami’ar Birmingham, wata babbar jami’a a ƙungiyar Russell Group na Birtaniya.
Ya ce wannan haɗin gwiwa zai ƙarfafa bincike,!-->!-->!-->…
Ƴan Sanda Sun Musanta Azabtar da Sowore, Yayinda Ya Mayar Da Martani Mai Zafi
Rundunar ƴan sanda ta ƙasa ta fito da bayani mai tsawo don ƙaryata zargin cewa an azabtar da ɗan gwagwarmayar siyasa, Omoyele Sowore, yayin tsare shi bisa tuhume-tuhumen laifuka da suka haɗa da amfani da jabun takardu da amfani da yanar!-->…
ADC Ta Caccaki Gwamnatin Tinubu Kan Harajin Ƴan Bindiga da Ƙauyen da Aka Bar Shi a Kwara
Jam’iyyar ADC ta nuna takaici matuƙa kan rahoton karɓar haraji na naira miliyan 56 daga manoma a Jihar Zamfara da ƴan bindiga suka yi, tare da hoton faifan bidiyon wani ƙauye a Ifelodun Jihar Kwara, da ƴan ƙauyen suka fice baki ɗaya saboda!-->…
Ƙungiyar Shugabannin ADC Na Jihohi Ta Nuna Goyon Baya Ga Jagorancin David Mark
A wani jawabi daga Lokoja, shugaban ƙungiyar shugabannin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) na jihohi, kuma shugaban jam’iyyar a Jihar Kogi, Kingsley Temitope Ogga, ya bayyana goyon bayan su ga jagorancin tsohon shugaban majalisar!-->…