Sign in
Sign in
Recover your password.
A password will be e-mailed to you.
Browsing Category
Labarai
Sabbin labarai daga gida da waje cikin Hausa, tare da bayanai masu zurfi da gaskiya. Muna kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya, Arewa da sauran duniya cikin lokaci. Karanta takaitattun rahotanni, bincike da kwakkwaran bayani.
Siyasar 2027: Shin Atiku Ya Jinkirta Shiga ADC Saboda Raɗe-Raɗin Jonathan Ne Zai Yi Mata Takara?
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya jinkirta shirin karɓar katin shaidar zama ɗan jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), a daidai lokacin da ake raɗe-raɗin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan na shirin yin takarar!-->…
Zargin Kisa: Wanda Ake Tuhuma Da Kashe Jami’in Civil Defense Ya Mutu Yayin Yunƙurin Tserewa
Daga: Mika'il Tsoho, Dutse
Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) ta bayyana kama wani mai suna Salisu Muhd mai shekaru 45, da ake zargi da hannu a kisan gilla da aka yi wa jami’insu, Bashir Adamu Jibrin, a kasuwar Shuwarin a!-->!-->!-->…
ASUU Za Ta Tsunduma Sabon Yajin Aiki, Ta Ce Malamai Na “Koyarwa Cikin Yunwa”
Ƙungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya (ASUU) ta yi gargaɗin cewa za ta sake tsunduma yajin aiki na ƙasa baki ɗaya idan gwamnati ta gaza magance matsalolin da suka daɗe suna addabarta da suka haɗa da rashin biyan haƙƙoƙi, lalacewar kayan!-->…
Dalilin Da Ya Sa Najeriya Ke Bayar Da Lantarki Ga Ƙasashen Waje Duk Da Miliyoyin Mutane Na Cikin…
Najeriya na ƙara ƙaimi wajen karkata ga amfani da makamashi mai tsabta tare da kare matakin ta na tura wutar lantarki zuwa ƙasashe makwabta duk da cewa miliyoyin ƴan ƙasa ba su da isasshiyar wutar.
Daraktan Hukumar Makamashi ta Ƙasa!-->!-->!-->…
An Ƙulla Wata Sabuwar Hulɗa Da Birtaniya Don Ƙarfafa Ilimi a Najeriya
Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya bayyana farin ciki kan ƙulla yarjejeniya tsakanin Jami’ar Legas (UNILAG) da Jami’ar Birmingham, wata babbar jami’a a ƙungiyar Russell Group na Birtaniya.
Ya ce wannan haɗin gwiwa zai ƙarfafa bincike,!-->!-->!-->…
Ƴan Sanda Sun Musanta Azabtar da Sowore, Yayinda Ya Mayar Da Martani Mai Zafi
Rundunar ƴan sanda ta ƙasa ta fito da bayani mai tsawo don ƙaryata zargin cewa an azabtar da ɗan gwagwarmayar siyasa, Omoyele Sowore, yayin tsare shi bisa tuhume-tuhumen laifuka da suka haɗa da amfani da jabun takardu da amfani da yanar!-->…
ADC Ta Caccaki Gwamnatin Tinubu Kan Harajin Ƴan Bindiga da Ƙauyen da Aka Bar Shi a Kwara
Jam’iyyar ADC ta nuna takaici matuƙa kan rahoton karɓar haraji na naira miliyan 56 daga manoma a Jihar Zamfara da ƴan bindiga suka yi, tare da hoton faifan bidiyon wani ƙauye a Ifelodun Jihar Kwara, da ƴan ƙauyen suka fice baki ɗaya saboda!-->…
Ƙungiyar Shugabannin ADC Na Jihohi Ta Nuna Goyon Baya Ga Jagorancin David Mark
A wani jawabi daga Lokoja, shugaban ƙungiyar shugabannin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) na jihohi, kuma shugaban jam’iyyar a Jihar Kogi, Kingsley Temitope Ogga, ya bayyana goyon bayan su ga jagorancin tsohon shugaban majalisar!-->…
Uwargidan Gwamnan Jigawa Ta Roƙi Maza Su Tallafa Wa Mata Masu Shayarwa
Daga: Mika'il Tsoho, Dutse
Gwamnatin Jihar Jigawa ta gudanar da bikin makon shayar da jarirai da nonon uwa na duniya, inda Uwargidan Gwamnan Jihar, Hajiya Khadija Umar Namadi, ta roƙi maza su mara wa matan da ke shayarwa baya domin!-->!-->!-->…
Rikicin PDP Ya Ƙara Ƙamari, Sule Lamido Ya Nemi A Kori Wasu Jiga-Jigan Jam’iyyar
Jigo a Jam’iyyar PDP, Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya nemi a kori Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da tsoffin gwamnonin jihohin Benue da Abia, Samuel Ortom da Okezie Ikpeazu, daga jam’iyyar Peoples Democratic Party!-->…
Zamfara: Ƴan Bindiga Sun Kashe Waɗanda Suka Kama Bayan Sun Karɓi Kuɗin Fansa Sama Da Naira Miliyan…
Al’umma a ƙauyen Banga da ke ƙaramar hukumar Kaura Namoda a Jihar Zamfara sun shiga cikin alhini bayan da aka kashe mutane 38 da aka sace musu, duk da cewa an biya ƴan bindigar sama da naira miliyan 50 a matsayin kuɗin fansa.
Shugaban!-->!-->!-->…
Niger: Haɗakar Rundunar Tsaro Ta Hallaka Ƴan Bindiga Da Dama A Ƙaramar Hukumar Shiroro, Ta Kuma Rasa…
A jihar Neja, sojojin Najeriya tare da haɗin gwiwar rundunar tsaro ta haɗaka da goyon bayan bayanan sirri daga hukumar DSS sun kashe aƙalla ƴan bindiga 45 a wani farmaki da suka kai a garin Iburu da ke ƙaramar hukumar Shiroro.
Rahotanni!-->!-->!-->…
Wasu Gwamnonin Na Shirin Komawa APC Kuma Zargin Ƙuntatawa Ba Gaskiya Ba Ne – Gwamnan Nasarawa
Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana cewa jam’iyyar APC na ƙara samun manyan ƴan siyasa daga jam’iyyun adawa da ke sauya sheƙa zuwa gare ta, yana mai musanta zargin ƙuntatawa da tsoratarwa daga ɓangaren gwamnati.
A hirar!-->!-->!-->…
Ana Ayyukan Raya Ƙasa Ne A Inda Zasu Yi Amfani, Martanin Abdulaziz Abdulaziz Ga Kwankwaso
Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan kafafen yaɗa labarai ɓangaren jaridu, Abdulaziz Abdulaziz, ya ce gwamnatin Tinubu na gudanar da ayyukan tituna ne bisa la’akari da amfanin da zasu yi wa tattalin arziƙin ƙasa da ƴan ƙasa gaba ɗaya.
A!-->!-->!-->…
Hatsarin Kwale-Kwale Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane Da Dama A Wata Jihar Arewa
Hukumomi sun bayyana cewa mutane da dama sun mutu sakamakon fashewar jirgin ruwa a ƙaramar hukumar Shiroro da ke jihar Neja jiya Asabar.
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA) ta tabbatar da afkuwar lamarin a yau Lahadi,!-->!-->!-->…
Kotu Ta Yanke Wani Muhimmin Hukunci Kan Shigar Ƴan Mata Masu Hidimar NYSC
Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke hukuncin cewa hana mata masu hidimar ƙasa (NYSC) sanya siket saboda wasu dalilai ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Najeriya.
A hukuncin da mai shari’a Hauwa Yilwa ta yanke a ranar 13 ga Yuni 2025,!-->!-->!-->…
Gwamnonin Da Ke Son Shiga Haɗakar ADC Na Tsoron Ƙuntatawa Daga Gwamnatin Tinubu
Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta bayyana cewa tsoron gallazawa da tsangwama daga ɓangaren gwamnati na hana gwamnoni shiga sabon gungun ƴan adawa da aka ƙaddamar domin fuskantar gwamnatin Tinubu a zaben 2027.
Kakakin!-->!-->!-->…
Ministan Ayyuka Ya Mayar Da Zazzafan Maratani Ga Kwankwaso, Ya Kuma Buƙaci Ya Ba Wa Tinubu Haƙuri
Ministan Ayyuka, David Umahi, ya buƙaci tsohon Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso da ya janye kalamansa tare da ba Shugaba Bola Tinubu haƙuri kan zargin cewa gwamnatin tarayya na fifita yankin Kudu wajen ayyukan raya ƙasa.
A wata sanarwa!-->!-->!-->…
Shugaban Ƙasa Tinubu Ya Faɗawa Gwamnoni Magana Kan Kuɗaɗen Da Suke Samu Daga Asusun Tarayya
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci gwamnonin jihohi da su tabbatar da cewa kuɗaɗen da suka karɓa daga gwamnatin tarayya sun haifar da gagarumin ci gaba, musamman a matakin ƙananan hukumomi.
Ya bayyana hakan ne a yayin taron!-->!-->!-->…
CIKAKKEN SHARHI KAN TATTALIN ARZIƘI: Alƙaluma Masu Kyau Amma Ƴan Najeriya Na Cikin Ƙunci
Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta bayyana cewa tattalin arziƙin Najeriya ya ƙaru da kaso 3.13 cikin ɗari a wannan mako, yayin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ci gaba da riƙe kuɗin ruwa a kaso 27.5 cikin ɗari karo na uku a jere.
Duk!-->!-->!-->…