Sign in
Sign in
Recover your password.
A password will be e-mailed to you.
Browsing Category
Mafi Shahara
NA MUSAMMAN: LGs A Jigawa Sun Gaza Shigar Da Kuɗin Fansho Kimanin Naira Biliyan 3.2
Ƙananan Hukumomi 27 na Jihar Jigawa sun gaza shigar da a ƙalla naira biliyan 3.2 na gudunmawar fansho tsawon shekaru kamar yanda jaridar PREMIUM TIMES ta gano.
Wasu takardu na gwamnati da jaridar ta samu sun bayyana cewar, ƙananan!-->!-->!-->…
DA ƊUMI-ƊUMI: Sojoji Sun Yi Wa Shugaban Ƙasar Gabon Juyin Mulki
Da sanyin safiyar yau Laraba, sojoji suka sanar da yin juyin mulki a ƙasa Gabon, inda suka ce, sun tunɓuke Shugaban Ƙasar Ali Bongo wanda ya ƙara lashe zaɓe a ranar Asabar da ta gabata.
Ali Bongo dai ya fara mulkin ƙasar Gabon ne a!-->!-->!-->…
Gwamna Namadi Ya Naɗa Masu Ba Shi Shawara Na Musamman Guda 35
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar A. Namadi ya amince da naɗin kashin farko na masu ba shi shawara, inda ya naɗa manyan masu ba shi shawara guda biyu da kuma masu ba shi shawara guda talatin uku.
Naɗin na ƙunshe ne cikin sanarwar da!-->!-->!-->…
JERIN SUNAYE: Sojojin Da Suka Mutu Sanadiyar Harbo Jirginsu Da Ƴan-ta’adda Suka Yi A Neja
Sojojin Najeriya sun yi jana'izar sojojin da suka rasa rayukansu a sanadiyar hatsarin jirginsu da ƴan-ta’adda suka jawo da kuma waɗanda aka kai harin kwanton ɓauna.
A makon da ya gabata ne, sojojin Najeriya suka bayyana cewar jami’ansu!-->!-->!-->…
Gwamna Namadi Ya Naɗa Ƙwararrun Masu Ba Shi Shawara Guda 6
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi ya amince da naɗin Ƙwararrun Masu Ba Shi Shawara guda shida.
Sanarwar naɗin na ƙunshe ne a sanarwar da Sakataren Gwamnatin Jiha, Malam Bala Ibrahim ya sanya wa hannu, sannan Jami’in Hulɗa da!-->!-->!-->…
Tinubu Ya Amsa Cewar Akwai Kurakurai A Takardun Karatunsa Na Jami’ar Jihar Chicago
Shari’ar da ɗan takarar jami’iyyar PDP a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Atiku Abubakar ya shigar ya neman Jami’ar Jihar Chicago ta bayyana bayanan karatun Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a cikinta ya ɗauki sabon salo, inda Tinubu ya karɓi!-->…
Sojojin Najeriya Da Na Birtaniya Za Su Yi Aiki Tare Wajen Kawo Ƙarshen Boko Haram – Badaru
Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar ya ce, Najeriya za ta ƙarfafa alaƙa da ƙasar Birtaniya domin magance matsalar tsaro a Najeriya.
Badaru ya bayyana hakan ne a yau, lokacin da wakilan ƙasar Birtaniya ƙarƙashin Ministan Sojojin!-->!-->!-->…
RIKICIN SARAUTA: Fusatattun Dangin Sarkin Dutse Sun Farmaki Gidansa Saboda Kalamai Kan Galadiman…
Wasu fusatattun dangin Mai Martaba Sarkin Dutse, Hamim Nuhu Sunusi, sun kutsa gidan kwanansa, inda su ka ci zarafin fadawa tare da sara abokin sarkin na ƙuruciya bisa kalaman da aka yi kan kawun sarkin, Galadiman Dutse, Basiru Sunusi.
!-->!-->!-->…
ƊAUKAR MA’AIKATA: Leadership Hausa Na Neman Ma’aikata
Shararriyar Jaridar Leadership wadda ke da sashin Hausa, na neman ma'aikata waɗanda za su yi aiki a ɓangaren kafafen sa da zumunta.
Domin neman wannan aiki a yi nazarin sanarwar da ke hoto na ƙasa.
DA ƊUMI-ƊUMI: ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki
Ƙungiyar Malam Jami’o’i ta Ƙasa, ASUU, biyo bayan Taron Shugabanninta na Ƙasa da ta yi a Jami’ar Maiduguri ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ofishin Babban Akawunta na Tarayya da ta saki kuɗaɗen ariyas na ƙarin girma da mambobin ƙungiyar ke!-->…
Ƴan-ta’adda 41 Ne Suka Mutu A Faɗan Da Ya Ɓarke Tsakanin Boko Haram Da ISWAP A Borno
Mayaƙan Boko Haram da na ISWAP a ƙalla 41 aka kashe bayan ɓarkewar faɗa tsakanin ƴan ƙungiyoyin a jiya Laraba a Jihar Borno.
Bayanai sun tabbatar da cewar, mayaƙan ISWAP waɗanda suka je wajen faɗan a kan ƙananan jiragen ruwa, sun!-->!-->!-->…
YANZU-YANZU: Mutane Da Dama Sun Mutu Yayin Da Wasu Su Ka Maƙale A Dogon Benin Da Ya Rushe A Abuja
Wani beni mai hawa da dama da ke kan Lagos Street a yankin Garki da ke Abuja ya rushe, inda mutane kusan 37 suka rasa rayukansu wasu kuma da dama suka maƙale a cikin ɓaraguzai, in ji PUNCH.
Lamarin dai ya faru ne a daren jiya Laraba!-->!-->!-->…
Jihar Kaduna Ta Fara Gina Babban Birni Mai Gidaje Dubu 500,000 Don Talakawa
Gwamnatin Jihar Kaduna ta fara gina babban birni mai ɗauke da gidaje 500,000 don talakawa da marassa ƙarfi mazauna jihar.
Wannan babban birni dai, gwamnatin za ta gina shi ne, haɗin guiwa da kamfanin ƙasar Qatar mai suna Qatar!-->!-->!-->…
A Ɗauki Nauyin Karatun Mace 100% Ko Kuma . . .
'Ya mace, idan ba za a iya ɗaukar nauyin karatunta da buƙatunta a lokacin karatu 100% ba, a haƙura, ya fi maslaha da alheri.
Ke ma idan kin san gidanku ba za su ba ki full scholarship ba, ki haƙura.
Wasu na amfani da talaucinsu yara!-->!-->!-->!-->!-->…
Kuskure Ne Ci Gaba Da Kasancewa Da Tsinanne
Daga: Aliyu M. Ahmad
Ina mamaki mutanen da za su tsinewa wasu mutane, kuma su ci gaba da bibiyar su.
Misali, wasu za su tsine wa 'yan film, Arewa24 ko 'yan TikTok amma kuma suna ci gaba da kallon shirye-shiryensu. Cikin wayarka akwai!-->!-->!-->!-->!-->…
Sanata Malam Madori Ya Fi Kowa Temakawa Ɗalibai A Yankin Jigawa Ta Gabas
Daga: Ahmed Ilallah
Duk da cewa a nawa ra'ayin kamata yayi wakilan al'ummah musamman a Majalissar Dokoki su maida hankali wajen samar da doka da kuma tilastawa shugabannin wajen samar da yanayi mai kyau da duk Dan Talaka zai samu kowane!-->!-->!-->…
Dubunnan Mutanen Da Suka Mutu A Dalilin Faɗan Manoma da Makiyaya
Malamai a Sashin Koyar da Kimiyyar Siyasa na Jami’ar Abuja sun koka kan irin rayuka da dukiyoyin da aka rasa a sanadiyyar faɗan manoma da makiyaya a jihohin Benue da Plateau.
Malaman sun bayyana rashin ƙoƙari daga ɓangaren gwamnati!-->!-->!-->…
Ministoci 8 Da Ƴan Najeriya Ke Mamakin Muƙaman Da Tinubu Ya Ba Su
Duba da yanayin aiki da karatun da waɗanda Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tura wa Majalissar Sanatoci domin tantancewa, ƴan Najeriya ciki har da su kansu sanatocin, sun yi tsammani daban da abun da suka gani a matsayin muƙaman da!-->…
Tallafin Naira Biliyan Biyar Ba Zai Magance Talauci Ba, In Ji NLC
Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya, NLC, Joe Ajero ya bayyana cewar, tallafin naira biliyan biyar ga kowacce jiha, wanda Gwamnatin Tarayya ta sanar bai kai kowa ya samu naira dubu 1500 ba, idan aka raba wa ƴan Najeriya sama miliyan 133!-->…
Wani Mutum Ɗan Shekara 50 Ya Kashe Agolan Gidansa A Jigawa
Rundunar ƴansandan Jihar Jigawa ta kama wani mutum ɗan shekara 50 mai suna Ibrahim Adamu da gangancin yin amfani da abu mai kaifi wajen yanka agolan gidansa ɗan shekara huɗu a duniya.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar Ƴansandan Jihar!-->!-->!-->…