Sign in
Sign in
Recover your password.
A password will be e-mailed to you.
Browsing Category
Mafi Shahara
Gwamnoni Ba Abun Yarda Ba Ne Kan Tallafin Da Za A Rabawa Talakawa – NLC
Ƙungiya Ƙwadago ta ƙwanƙwashi Gwamnatin Tarayya kan sakin kuɗi naira biliyan 180 ga gwamnonin jihohi a matsayin kuɗin tallafawa talakawa wajen magance matsalolin da janye tallafin man fetur ya tsunduma shi a ciki.
Ƙungiyar Ƙwadago, NLC,!-->!-->!-->…
JANYE TALLAFI: Jihohi Zasu Samu Naira Biliyan 5 Kowaccensu A Matsayin Tallafi
Gwamnatin Tarayya ta amince da fitar da naira biliyan 5 ga kowacce jiha da Babban Birnin Tarayya domin su samu damar samar da abincin da zasu rabawa talakawa a jihohinsu.
Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ne ya bayyana hakan yau a!-->!-->!-->…
Kusan Sabon Ministan Ilimi Na Najeriya, Farfesa Mamman
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Babban Lauyan Najeriya, Farfesa Tahir Mamman a matsayin sabon Ministan Ilimi na Najeriya.
Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Kafafen Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Ajuri Ngelale ne ya bayyana!-->!-->!-->…
Wani Tsoho Ɗan Shekara 84 Ya Kashe Matarsa Saboda Ta Ƙi Kwanciya Da Shi
Wani tsoho ɗan shekara 84 mai ƴaƴa 7 mai suna Gabriel Uhuwa ɗan Jihar Edo ya faɗa komar ƴansanda saboda zarginsa da ake da kashe matarsa saboda ta ƙi yarda ta kwanta da shi.
Ƴansandan ne suka tabbatar da kama tsohon a jiya Laraba,!-->!-->!-->…
JUYIN MULKIN NIJAR: Ƴan Arewa Na Asarar Naira Biliyan 13 Duk Sati
Ƴan kasuwa a yankin Arewacin Najeriya sun koka kan yanda suke asarar kimanin naira biliyan 13 duk sati saboda rufe boda da aka yi biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar.
A ranar 4 ga watan nan na Agusta ne, Shugaban Ƙasa Bola!-->!-->!-->…
Najeriya Ta Yi Fice A Duniya Wajen Fama Da Ƙarancin Abinci Mai Gina Jiki
Hukumar Kula da Ci Gaban Ƙasashe ta Amurka, USAID, ta bayyana Najeriya a matsayin ƙasa ta biyu a duniya da take fama ƙarancin abinci mai gina jiki.
Daraktar USAID, Anne Patterson ce ta bayyana hakan a jiya Laraba, lokacin da take jawabi!-->!-->!-->…
Kar Ku Bari Shugaban Ƙasa Da Gwamnoni Su Wulaƙanta Ku – Sarki Sunusi Ga Ƴan Najeriya
Bayan nazarin abubuwan da suke ƙasar nan, Sarkin Kano na 14, Mai Martaba Sunusi Lamido Sunusi II ya ce, ƴan Najeriya na karɓar wulaƙanci da yawa daga ƴan siyasar da suka rena su.
Ya yi kiran ƴan Najeriya da kar su bari shugaban ƙasa ko!-->!-->!-->…
NAƊIN MINISTOCI: Tinubu Ya Naɗa Kansa Babban Ministan Mai, Zai Rantsar Da Ministoci Ranar Litinin
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa kansa Babban Ministan Albarkatun Mai na ƙasa yayin da ya naɗa tsohon sanata, Sanata Heineken Lokpobiri a matsayin Ƙaramin Ministan Albarkatun Mai.
Kamar dai yanda ya kasance a shugaban ƙasar da ya!-->!-->!-->…
JERIN SUNAYE: Tinubu Ya Naɗa Badaru Ministan Tsaro, Wike Ministan Abuja, Ya Bai Wa Saura Muƙamansu
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya saki sunayen sabbin ministocinsa da ofisoshin da ya ba su.
Tsohon Gwaman Jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar ya samu muƙanmin ministan tsaro, sai kuma tsohon Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike ya!-->!-->!-->…
Darajar Naira Na Ƙara Farfaɗowa
Farashin dala na faɗuwa a kasuwannin canjin kuɗi a Najeriya daga naira 940 zuwa naira 890 a safiyar Laraba, kamar yadda bayanan da BBC ta samu daga kasuwannin canji a birnin Legas suka nuna.
Bayanan sun ce a safiyar jiya Talata, an!-->!-->!-->…
Jigawa Zata Gabatar Da Ƙwarya-Ƙwaryar Kasafin Kuɗi Na Naira Biliyan 44.7
Majalissar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da miƙa ƙwarya-ƙwaryar kasafin kuɗi na naira biliyan 44,700,000,000 ga Majalissar Dokoki ta jihar domin amincewa.
Majalissar ta amince da miƙa kasafin kuɗin ne a yau, lokacin gabatar da!-->!-->!-->…
DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnatin Kano Ta Hana Private Schools Ƙarin Kuɗin Makaranta
Gwamnatin Kano ta tabbatar da dakatar da ƙarin kuɗin makaranta da makarantu masu zaman kansu na jihar ke ƙoƙarin yi.
Sannan gwamnatin ta umarci dukkan makarantun da su sabunta lasisinsu domin su dace da tsarin inganta ilimi na gwamnan!-->!-->!-->…
An Kashe Sojojin Nijar 17 A Iyakar Ƙasar Da Mali
An kashe sojojin Jamhuriyar 17 a jiya Talata a wani hari da ake zargin ƴan ta’adda ne suka kai musu a iyakar ƙasar ta yamma wadda ta haɗa ƙasar da Mali, in ji Ma’aikatar Tsaro ta ƙasar.
Ma’aikatar Tsaron ta ce, sojojin sun fuskanci!-->!-->!-->…
Ƴan Najeriya Na Nadamar Cin Zaɓen Tinubu Da APC, In Ji PDP
Jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, reshen Jihar Ondo, a jiya Talata, ta bayyana matsayarta kan yanayin wahalar rayuwar da ƴan Najeriya ke sha, wadda jam’iyyar ta bayyana a matsayin abun da aka ƙaƙabawa ƴan Najeriya ta hanyar tallata!-->…
Ƴansanda Sun Kama Ɓarayin Wayar Lantarki, Shanu, Awaki Da Ƴan-Fashi A Jigawa
Jami’an ƴansanda na Rundunar Ƴansanda ta Jihar Jigawa sun kama wasu da ake zargin ƙwararrun ɓarayin shanu da awaki ne a garin Maigatari.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, DSP Shiisu Adam ne ya bayyana hakan lokacin da yake jawabi ga!-->!-->!-->…
HOTUNA: Kashifu Inuwa Ya Karɓi Baƙuncin Shugabannin Google Kan Bunƙasa Fasahar Zamani Ga Matasa
Babban Daraktan Hukumar Bunƙasa Fasahar Zamani da Sadarwa, NITDA, Malam Kashifu Inuwa Abdullahi ya karbi baƙuncin tawaga ƙarƙashin jagorancin Olu,ide Balogun, Daraktan Google na Afirka ta Yamma daga kamfanin Google.
KARANTA WANNAN:!-->!-->!-->…
An Saka Ranaku, Gurare Da Lokutan Tantance Ƴan J-Teach Masu Digiri A Jigawa
Ma’aikatar Ilimi mai Zurfi, Kimiya da Fasaha ta Jihar Jigawa ta sanar da ranakun tantance waɗanda suka zana jarabawar neman aikin koyarwa na J-Teach a jihar.
Ma’aikatar ilimin ta rarraba ranakun gudanar da tantancewar zuwa yankunan!-->!-->!-->…
TSADAR MAI: Babu Wani Shirin Dawo Da Tallafin Mai A Najeriya, In Ji Fadar Shugaban Ƙasa
Babban Mai Temakawa Shugaban Ƙasa a Kan Harkokin Yaɗa Labari da Hulɗa da Jama’a. Tope Ajayi, ya ce, babu wani shirin da gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu take yi na dawo da tallafin man fetur.
Ajayi ya yi wannan bayani ne a yau!-->!-->!-->…
Wasu Da Ake Zargin Makiyaya Ne Sun Kai Hari Wata Makaranta, Sun Kashe Ango Da Amarya
Wani ango da amaryarsa, sabbin aure, sun rasa ransu a yayin da wasu da ake zargin makiyaya ne suka kai hari kan Makarantar Sikandire ta BECO Comprehensive da ke garin Kwi a Ƙaramar Hukumar Riyom ta Jihar Plateau.
Lamarin dai ya faru ne!-->!-->!-->…
Ana Matsawa Najeriya Kan Ta Amince Da Auren Jinsi
Cocin Angalican ta Najeriya ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta bijirewa kiraye-kirayen da Turawan Yamma ke mata na ta sake matsayinta kan auren jinsi a Najeriya.
Wannan dai na a cikin jawabin bayan taron da cocin ta saki bayan!-->!-->!-->…