Sign in
Sign in
Recover your password.
A password will be e-mailed to you.
Browsing Category
Mafi Shahara
Hukumar Kidaya Ta Yi Bayanin Dalilan Dage Aikin Kidaya Ana Daf Da Fara Shi
Hukumar Kidaya ta Kasa, NPC, ta ce an dage kidayar yawan jama’a da gidaje ta shekarar 2023 saboda shirin mika mulki ga sabuwar gwamnati da kuma yanayin da kasa ta shiga bayan zabubbukan 2023.
Manajan Kidaya na Shekarar 2023 Kuma!-->!-->!-->…
Sojoji Sun Farmaki Ofishin KAEDCO Da Ke Kebbi, Sun Ci Zarafin Ma’aikata Saboda Rashin Wutar Lantarki
Sojoji dauke da makamai sun kai farmaki ofishin Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kaduna KAEDCO a jihar Kebbi tare da cin zarafin ma’aikatan da suka kasa samar musu da wutar lantarki a barikinsu.
Manajan kamfanin na jihar Kebbi,!-->!-->!-->…
An Dakatar Da Cire Tallafin Man Fetur A Najeriya
Majalissar Zartarwa ta Kasa, NEC, ta dakatar da shirin janye tallafin man fetur wanda a baya aka tsara cirewa a watan Yunin bana bayan karewar wa’adin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Da take yiwa manema labarai jawabi jim kadan bayan!-->!-->!-->…
Hukumar Lafiya Ta Gargadi Mutane Kan Shan Wani Maganin Tari Na Indiya
Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce an gano wasu tarin jabun magungunan tari da Indiya ta yi a tsibirin Marshall da ke Micronesia.
WHO ta ce gwajin maganin tarin mai suna Guaifenesin TG wanda kamfanin haɗa magunguna na QP Pharmachem!-->!-->!-->…
Ba A Samu Sanya Hannun Jari Ko Na Sisi Ba A Wasu Jihohi 8 Na Najeriya
Akalla jihohi takwas ne ba su iya jan hankalin masu sanya hannun jari daga kasashen waje ba amma bashin da suka ciyo ya kai naira biliyan 194.09 a tsakanin shekarar 2019 da 2022 kamar yanda jaridar PUNCH ta gano.
Bayanai daga Hukumar!-->!-->!-->…
Gwamnati Ta Dakatar Shugaban Hukumar Kula Ilimin Sakandire Saboda Zargin Cinhanci
An dakatar Shugaban Hukumar Kula da Ilimin Sakandire ta Kasa, NSSEC, Farfesa Benjamin Abakpa saboda zargin badakalar kudade.
Dakatarwa ta bayyana ne a takardar da Babban Sakatare na Ma’aikatar Ilimi ta Kasa, Andrew David Adejo ya!-->!-->!-->…
Gwamnatin Tarayya, Jihohi Da Kananan Hukumomi Sun Raba Kudin Maris Naira Biliyan 714.629
Kwamitin Rarraba Kudaden Tarayya, FAAC, ya raba naira biliyan 714.629 ga rukunonin gwamnati uku na Najeriya jiya Laraba a Abuja a matsayin kudin watan Maris.
Wannan labari ya samu ne daga sanarwar bayan taro da aka saki a karshen zaman!-->!-->!-->…
Zazzabin Lassa Ya Watsu Cikin Jihohi 26 Na Najeriya, Ya Kashe Mutane 151
Mutuwa a sanadiyyar zazzabin Lassa a Najeriya ta karu a bana zuwa 151 daga 148, kamar yanda Hukumar Kare Yaduwar Cututtuka ta Najeriya, NCDC ta sanar.
A rahotonta na mako na 14, NCDC ta ce, an samu rahoton kamuwa da zazzabin Lassa 869!-->!-->!-->…
Buhari Ya Dawo Abuja Bayan Kwashe Kwanaki 8 A Saudiyya
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dawo Abuja bayan ziyarar kwanaki 8 a kasar Saudiyya, inda ya kuma gabatar da aikin Umara.
Shugaban na Najeriya ya bar Filin Jirgin King Abdulaziz da ke Jiddah a kasar Saudiyya a yau Laraba.
Kamfanin!-->!-->!-->!-->!-->…
Sabon Dan Majalissar Wakilai Ya Bayar Da Gudunmawar Shanu 59 Don Bikin Sallah A Mazabarsa
Sabon Dan Majalissar Wakilai mai jiran rantsuwa na Mazabar Gwamnatin Tarayya ta Maru/Bungudu a Jihar Zamfara, Abdulmalik Zubairu a jiya Talata, ya bayar da gudunmawar shanu 59 ga al’ummar mazabarsa domin gudanar da bikin karamar sallah.
!-->!-->!-->…
Binani Ta Musanta Zargin Cewa Ta Bayar Da Cinhancin Biliyan 2 Don Ta Ci Zabe
‘Yar takarar jam’iyyar APC a zaben gwamnan Jihar Adamawa da ya gabata, Sanata Aishatu Dahiru, wadda aka fi sani da Binani, ta musanta zarge-zargen da ake mata na cewa ta baiwa wasu jami’an Hukumar Zabe mai Zamanta Kanta ta Kasa, INEC, ciki!-->…
Fintiri Ya Lashe Zaben Gwamnan Adamawa
Hukumar zaɓe a Najeriya ta sanar da Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaɓen jihar Adamawa, wanda ya ƙare cikin taƙaddama.
Jami'in sanar da sakamakon zaɓen gwamna na Adamawa, Farfesa Mohammed Mele ya ce Ahmadu Fintiri!-->!-->!-->…
Za A Fara Duban Watan Karamar Sallah Ranar Alhamis
A daidai lokacin da watan Ramadan na shekarar Musulunci ta 1444 ke karewa, Majalissar Koli ta Al’amuran Addinin Musulunci a Najeriya, NSCIA, karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ta bukaci!-->…
INEC Ta Dakatar Da Kwamishinanta Da Ya Sanar Da Zaben Adamawa
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta umarci Kwamishinanta na Jihar Adamawa, Yunusa Ari da ya tsame kansa daga dukkan wasu aiyuka da suka shafi hukumar har zuwa umarni na gaba.
A wata wasika da aka sanyawa hannu ranar Litinin,!-->!-->!-->…
Me Yasa Wasu Ke Yawan Jin Bacci?
Daga: CRI HAUSA
Masu karatu, ko kuna jin bacci bai ishe ku ba duk da cewa kun dauki lokaci mai tsawo kuna yin baccin? Kwanan baya masanan kasar Jamus sun bayyana wasu dalilai guda 8 da kan sa wasu jin bacci ba ya isar su.
Da farko,!-->!-->!-->!-->!-->…
Jure Ƙishi Ba Juriya Ba Ce Gangancin Jefa Kai Cikin Matsalar Ƙoda Ne
Daga: Sama’ila Bature Jahun
Masana kiwon lafiyar ƙoda sun bayar da shawarar shan tsabtataccen ruwa aƙalla lita 2 zuwa 3 a kowace rana. Wato lita 2 (pure water 4) zuwa 3 (pure water 6) shi ne mafi ƙarancin ruwan da mutum ya kamata ya sha!-->!-->!-->…
Amfanin Zogale Ga Fatar Dan Adam
Daga: Hafsat Abubakar Sadiq
Wani lokaci abubuwa masu girma sukanzo a karamar suffa, kamar dai zogale, da ya kasance ƙananan ganye mai tarin albarka da kara lafiya. Kazalika ba kadai ganyen bane mai amfani, kowanne ɓangare na wannan!-->!-->!-->…
‘Yan Sa-Kai Sun Kashe Makiyaya 12 A Sokoto
Kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetta Allah ta yi shelar cewar ‘Yan sa-kai a jihar Sokoto sun halaka mambobin ta 12 sakamakon wani farmakin da suka kai a matsugunansu da ke yankin Gwadabawa.
RFI Hausa ta rawaito cewa, shugaban kungiyar ta!-->!-->!-->…
Yanda Za A Dakile Tare Da Kandagarkin Zazzabin Cizon Sauro A Duniya (I)
Ranar 25 ga watan Afrilu ta ko wace shekara, rana ce ta dakile da kandagarkin ciwon zazzabin sauro ta duniya.
Ciwon zazzabin cizon sauro, mummunan ciwo ne da ke yaduwa tsakanin mutane sakamakon samun kwarin plasmodium a jikin dan Adam.!-->!-->!-->…
Ko Akwai Bukatar A Riƙa Tantance Malamai Kafin Su Fara Wa’azi A Najeriya?
Sananniyar kafar yada labarai ta BBC ta yi bincike tare da jin ra’ayoyin malamai daban-daban kan ko akwai bukatar a dinga tantance malamai kafin a ba su dama su yi wa’azi ga al’umma.
Wannan ya samo asali ne saboda zargin sakin kalaman!-->!-->!-->…