Sign in
Sign in
Recover your password.
A password will be e-mailed to you.
Browsing Category
Mafi Shahara
Batun Sai Ɗalibai Sun Kai Shekaru 12 Zasu Shiga Ƙaramar Sikandire Ba Shi Da Tushe – Ma’aikatar Ilimi
Ma’aikatar Ilimi ta Tarayyar Najeriya ta ƙaryata rahotannin da ke cewa gwamnati ta sanya shekara 12 a matsayin mafi ƙarancin shekarun da ɗalibai za su iya fara ajin JSS1 a makarantu a faɗin ƙasar.
Cikin wata sanarwa da aka fitar ranar!-->!-->!-->…
Kotu Ta Tura Shahararren Ɗan TikTok Gidan Yari Bisa Yaɗa Ƙaryar Tinubu Ya Mutu
Wata kotun majistare a Abuja ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare wani mai amfani da kafar TikTok, Ghali Isma’il, a gidan gyaran hali na Keffi bisa zargin yada ƙaryar cewa Shugaba Bola Tinubu ya mutu.
An gurfanar da shi ne bayan!-->!-->!-->…
Rikicin SDP Ya Ƙara Ta’azzara: NEC Ta Rushe Shugabancin Jam’iyya, Ta Ce Ba Ta San El-Rufa’i A…
Jam’iyyar SDP ta sake fuskantar babban rikici yayin da kwamitin NEC na jam’iyyar ya rushe shugabancin Shehu Gabam, wanda ke a dakace, tare da naɗa sabbin shugabanni na wucin gadi domin ceto jam’iyyar.
Wannan mataki ya biyo bayan wani!-->!-->!-->…
ASUU Ta Yi Allah-wadai Da Sake Sunan Jami’ar Maiduguri, Ta Ce Za Ta Damfara Gwamnati A Kotu
Ƙungiyar malaman jami’a, ASUU reshen Jami’ar Maiduguri ta ce ta “ta matuƙar ƙin yarda kuma ta yi fatali” da matakin gwamnatin tarayya na sauya sunan jami’ar zuwa Muhammadu Buhari University, Maiduguri.
A wata sanarwa da shugaban!-->!-->!-->…
Majalisar Wakilai Zata Kama Gwamnan Babban Bankin Najeriya Bisa Saɓa Dokokin Kula Da Kuɗaɗe
Kwamitocin haɗaka na Majalisar Wakilai kan Lissafin Kuɗi da Kadarorin Jama’a sun yi barazanar bayar da sammacin kama Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Olayemi Michael Cardoso, saboda ƙin bayyana a gabansu duk da gayyatar da aka yi masa sau!-->…
Za A Fara Bayar Da Tallafin Naira Miliyan 50 Ga Ɗaliban Kimiyya Da Fasaha A Najeriya
Gwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na bayar da tallafin Naira miliyan 50 ga daliban da ke karatu a fannoni na kimiyya, fasaha, injiniya, lissafi da likitanci (STEMM) a manyan makarantu domin bunƙasa ƙirƙire-ƙirƙire da kasuwanci a!-->…
Kotu Ta Yankewa G-Fresh Hukuncin Ɗauri Bisa Cin Zarafin Naira
Wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta yanke wa wani shahararren mai amfani da TikTok, Abubakar Ibrahim, wanda aka fi sani da G-Fresh, hukuncin ɗauri na wata biyar bisa laifin cin mutuncin kuɗin Najeriya.
Mai shari’a Sale Musa Shuaibu!-->!-->!-->…
Gwamnatin Tinubu Ta Mayarwa Da Kwankwaso Martani Kan Zargin Nuna Wariya Ga Arewa
Fadar shugaban ƙasa ta musanta zargin da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 ƙarƙashin jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi na cewa, gwamnatin Tinubu na nuna wariya ga yankin Arewa.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a!-->!-->!-->…
PDP Ta Sanar Da Rana Da Wajen Zaɓen Sabbin Shugabanninta
Jam’iyyar PDP ta sanya ranakun 15 zuwa 16 ga watan Nuwamba, 2025 domin gudanar da babban taronta na ƙasa da zaɓen sabbin shugabanni a birnin Ibadan.
A cewar wata sanarwa daga taron NEC da aka gudanar a Abuja, an amince da jadawalin!-->!-->!-->…
JERIN SUNAYE: Lauyoyi 57 Da Suka Samu Ɗaukaka Zuwa Matsayin SAN A Najeriya
Kwamitin bayar da muƙamin SAN (LPPC) ya amince da ɗaukaka lauyoyi 57 zuwa matsayin Senior Advocate of Nigeria (SAN) a wani zama da aka gudanar a Abuja.
An samu lauyoyi 56 daga ɓangaren shari’a kai tsaye da guda ɗaya daga ɓangaren ilimi,!-->!-->!-->…
Dole Ne Sai Ɗalibi Ya Kai Shekaru 12 Kafin Ya Shiga Ƙaramar Sikandire A Najeriya
Ma’aikatar Ilimi ta Tarayyar Najeriya ta ƙaddamar da sabon tsarin da ya ƙayyade shekarun shiga makarantar Sikandire (JSS1) a makarantu masu zaman kansu zuwa 12 bayan kammala Firamare.
Wannan na cikin sabon tsarin makarantu masu zaman!-->!-->!-->…
Ƴan Sanda Sun Cafke Wanda Ya Kashe Tsohuwar Matarsa Da Ɗan Fashi A Jigawa
Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta cafke mutum biyu da ake zargi da hannu a kisan kai da fashi da makami a sassa daban-daban na jihar.
Kakakin rundunar, SP Shi’isu Adam, ya bayyana cewa Iliyasu Musa, mai shekaru 40 daga ƙauyen!-->!-->!-->…
Kwankwaso Ya Zargi Gwamnatin Tinubu Da Nuna Wariya Ga Yankin Arewa
Tsohon gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da fifita yankin Kudu wajen rabon albarkatun ƙasa tare da barin Arewa cikin talauci da koma baya.
A wajen!-->!-->!-->…
MATSALAR KARANCIN FANSHO: Ba Kawai Ƴan Sanda Ba, Dukkan Ma’aikata Ne
Daga: Ahmed Ilallah
Bayan ɗaukar kwanaki, tsaffin ƴan sanda suna nuna suke shan wahalar rayuwa bayan sun yi ritaya a kafafen yaɗa labarai a jiya suka ƙaddamar da zangazangarsu ta kwanaki uku don neman kawo ƙarshen matsalar da suke ciki.!-->!-->!-->…
Yadda Gwamna Namadi Ke Kiyaye Daidaito Tsakanin Masarautun Jigawa
Tun bayan ƙirƙirar jihar Jigawa daga tsohuwar jihar Kano a 1991, zaɓen Dutse a matsayin babban birni maimakon Hadejia ya janyo taƙaddama mai tsawo tsakanin masarautu.
Rikicin ya fito fili a zaɓen 2023 lokacin da APC ta zaɓi Umar Namadi!-->!-->!-->…
APC Ta Naɗa Farfesa Nentawe Yilwatda A Matsayin Sabon Shugabanta Na Ƙasa
Jam’iyyar APC ta zaɓi Farfesa Nentawe Yilwatda a matsayin sabon shugaban jam’iyyar na ƙasa bayan murabus ɗin Abdullahi Ganduje saboda dalilan lafiya.
Yilwatda, wanda ke riƙe da muƙamin Ministan Harkokin Jin Ƙai, ya fito ne daga jihar!-->!-->!-->…
Ƴan Jigawa Na Adawa Da Yunƙurin Gwamnati Na Gina Shaguna Kan Naira Biliyan 3.5 A Kano
Wasu ƴan jihar Jigawa sun bayyana damuwarsu dangane da amincewar majalisar zartarwar jihar na kashe naira biliyan 3.5 don gina shaguna a Kano da kuma ware naira miliyan 500 don masu ƙaro ilimi a jami’o’in ƙasashen waje.
A cikin wata!-->!-->!-->…
An Bindige Jami’in NDLEA Har Lahira Yayin Da Yake Bakin Aiki
Wasu da ake zargin masu fataucin miyagun ƙwayoyi ne sun bindige wani jami’in hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), mai suna Jide, a wani samame da aka kai a unguwar Ita’nla da ke garin Ondo.
Rahotanni sun ce!-->!-->!-->…
Har Yanzu Sanata Natasha Dakatacciya Ce – Majalissar Dattawa
Mai magana da yawun Majalisar Dattawa, Sanata Yemi Adaramodu, ya bayyana cewa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan za ta ci gaba da kasancewa cikin dakatarwar da aka yi mata har sai majalisar ta dawo daga hutun makonni biyu da take ciki.
!-->!-->!-->…
Makusantan Tinubu Na Ɓoye Masa Gaskiyar Abun Da Ke Faruwa A APC Da Najeriya – Adamu Garba
Ɗan jam’iyyar APC kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Adamu Garba, ya zargi wasu makusantan Shugaba Bola Tinubu da ɓoye masa gaskiyar halin da ƙasa da jam’iyyar ke ciki, yana mai cewa su na yaudararsa da cewa komai na tafiya lafiya.
!-->!-->!-->…