Sign in
Sign in
Recover your password.
A password will be e-mailed to you.
Browsing Category
Siyasa
Labaran siyasa daga Najeriya da ketare, tare da nazari, bayanai kan doka da tsarin mulki. Muna bin diddigin zabe, jam’iyyu da manufofi domin taimaka wa masu karatu su yanke shawara. Tattaunawa cikin natsuwa da gaskiya.
NNPP Za Ta Fitar Da Matsaya Tsakanin Goyon Bayan Tinubu, Shiga Haɗaka Ko Ci Gaba A Haka
Gabanin zaɓen 2027, jam’iyyar NNPP ƙarƙashin jagorancin Rabiu Musa Kwankwaso ta saka ranar 28 ga Agusta don taron shugabanninta, NEC mai muhimmanci domin yanke matsayar dabarunta na siyasa, a cewar mai magana da yawunta, Ladipo Johnson.
!-->!-->!-->…
INEC Ta Bayyana Adadin Waɗanda Su Kai Rijistar Farko A Awanni 7 Bayan Fara Sabuwar Rijistar Katin…
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) ta bayyana cewa mutane 69,376 sun yi pre-registration a cikin awanni bakwai bayan buɗe shafin ci gaba da rajistar masu kaɗa ƙuri’a (CVR), inda Sam Olumekun ya ce “shafin ya fara aiki da 8:30 na safe ya!-->…
“Kwankwaso Ba Zai Taimaki Tinubu a 2027 Ba” — Buba Galadima
Buba Galadima, ɗaya daga cikin manyan shugabannin NNPP, ya ƙaryata gaba ɗaya zargin cewa Rabiu Kwankwaso zai shiga sahun Tinubu domin tallafa masa a zaɓen 2027, yana mai cewa irin mu'amalar gwamnatin tarayya da aka nuna wa Kano ba za ta!-->…
INEC Za Ta Fitar Da Sunayen Ƙungiyoyin Da Za Ai Wa Rijistar Zama Jam’iyyu Daga Buƙatu 151 Da Ta…
Hukumar Zabe ta Ƙasa, INEC, ta sanar da cewa tana kan kammala aikin gajarta sunayen ƙungiyoyin siyasa da suka nuna buƙatar zama jam’iyya, tare da shirin bayyana sunayen waɗanda suka cika sharuddan nan da nan bayan kammala zaɓen cike-gurbi.!-->…
PDP Ta Yi Watsi Da Sakamakon Zaɓen Babura/Garki, Ta Ce “An Yi Amfani Da Ƙarfin Gwamnati”
Jam’iyyar PDP ta ƙi sakamakon zaɓen cike-gurin Babura/Garki a Jigawa, tana zargin an samu maguɗi, tsoratar da masu zaɓe da kuma sayen ƙuri’u a lokacin gudanar da zaɓen.
Umar Kyari, kakakin PDP na jihar, ya bayyana wa manema labarai a!-->!-->!-->…
Zaɓen Cike-Gurbi: Rikici Ya Ɓarke Tsakanin APC Da Jam’iyyun Adawa
Zaɓen cike gurbi da aka gudanar a ranakun Asabar a yankuna 16 cikin jihohi 12 ya haifar da saɓani tsakanin manyan jam'iyyun Najeriya, inda APC ta lashe mafi yawan kujeru (12), PDP ta samu nasara a Ibadan da Adamawa, NNPP a Kano, APGA a!-->…
Dalilin Da Ya Sa Bai Kamata Goodluck Jonathan Ya Sake Takara A 2027 Ba
Daga: Kabiru Zubairu Birnin Kudu
Tsohon sanata Shehu Sani ya shawarci tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan da kada ya sake neman kujerar shugaban ƙasa a zaɓen 2027, a yayin wata tattaunawa a shirin Sunday Politics na Channels!-->!-->!-->…
Badaru Ya Ƙaryata Labarin Faɗuwar APC A Rumfarsa, Ya Ce “Tsagwaron Ƙaryace Da Yaudarar Masu Fitina”
Daga: Mika’il Tsoho, Dutse
Ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, ya fito da sanarwa yana ƙaryata rahotannin da ke cewa APC ta faɗi a akwatin zaɓensa na Babura Kofar Arewa Polling Unit 001 a zaɓen cike-gurbi na Garki/Babura.
A!-->!-->!-->!-->!-->…
ADC Ta Caccaki Zaɓen Cike Gurbi, Ta Ce “Rigingimu, Sayen Ƙuri’u Da Tsangwama Ne Suka Mamaye Komai”
Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta nuna damuwa matuƙa kan yadda aka gudanar da zaɓukan cike-gurbi na Asabar, 16 ga Agusta, a jihohi 12 da mazaɓu 16, tana mai cewa tsarin zaɓe ya ƙara lalacewa a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba!-->…
Tinubu Ya Yabi Nasarar Zaɓen Cike-Gurbi A Jihohi 12, Ya Godewa Ƴan Najeriya Bisa Nuna Yarda Da APC
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya murnar nasarar zaɓen cike-gurbi na Asabar, 16 ga Agusta, a mazaɓu 16 a jihohi 12, kamar yadda fadar shugaban ƙasa ta bayyana a sanarwar da ta fitar.
Ya yabawa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) kan!-->!-->!-->…
SERAP Ta Nemi A Binciki Zargin Auyo Na Biyan Har Naira Miliyan 3 Don Gabatar Da Ƙudiri A Majalisa
Ƙungiyar SERAP ta yi kira ga EFCC da ICPC su binciki Majalisar Tarayya kan zargin cewa ƴan majalisa na “biyan daga naira miliyan 1 zuwa naira miliyan 3” domin su gabatar da ƙudiri, ko miƙa koke-koke.
Kiran ya biyo bayan zargin da ɗan!-->!-->!-->…
Zaɓen Cike Gurbin Kaura-Namoda Ta Kudu A Zamfara Bai Kammala Ba (Inconclusive), INEC Ta Faɗi Dalilai
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ayyana zaɓen cike-gurbin Kaura-Namoda ta Kudu a Zamfara a matsayin inconclusive bayan da tazarar ƙuri’u tsakanin manyan jam’iyyun ta gaza kai wa adadin PVCs da aka karɓa a rumfunan da aka soke.
Mai bayyana!-->!-->!-->…
SAKAMAKON ZAƁEN CIKE GURBI: Yanda Ta Kaya Tsakanin APC, PDP, APGA Da NNPP A Zaɓukan Da Aka Gudanar…
Daga: Kabiru Zubairu Birnin Kudu
Zaɓukan cike gurbi da aka gudanar a ranar Asabar sun haifar da manyan sauye-sauye a fagen siyasar Najeriya, inda jam’iyyun PDP, APC, APGA da NNPP suka yi takara a jihohin ƙasar, kuma sakamakon ya bayyana!-->!-->!-->…
GASKIYAR MAGANA: Ƙungiyar Good Governance Ta Kare Hon. Usman Kamfani Auyo “Bai Ce Majalisa Na Karɓar…
Ƙungiyar sa ido kan shugabanci ta Good Governance Advocates daga Jihar Jigawa ta fito fili ta kare Hon. Ibrahim Usman Kamfani Auyo, tana mai musunta rahotannin da suka bayyana a wasu kafafen yaɗa labarai cewa dan majalisar ya ce ana ba!-->…
‘Oyoyo Baba!’ – Badaru Ya Jawo Hankalin Dubban Magoya Baya A Babura, Yayin Da…
Dubban magoya baya sun taru a ranar Asabar don maraba da Ministan Tsaro, Badaru Abubakar, yayin zuwansa Jihar Jigawa domin zaɓen cike-gurbi na Babura/Garki a mazaɓarsa, abin da ya sa ake ganin an wanke jita-jitar cewa zai iya gujewa!-->…
PDP Ta Yi Alƙawarin Kare Ƙuri’unta A Zaɓen Jigawa Na Babura Da Garki
Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta yi gargaɗin cewa duk wani yunƙuri na karkatar da zaɓen cike-gurbi na Babura/Garki da aka gudanar a ranar Asabar, tana mai cewa magoya bayanta za su kasance masu lura sosai.
Umar Kyari,!-->!-->!-->…
APC Na Neman A Soke Zaɓe A Kano: Ƴan Jam’iyyar Sun Yi Ƙorafin Samun Tashin Hankali A…
Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta buƙaci hukumar INEC da ta soke zaɓen cike-gurbi na mazaɓar Shanono/Bagwai da kuma sabon zaɓen Ghari a Jihar Kano, ta na mai cewa an samu yamutsin tashin hankali a wuraren zaɓe.
A wata sanarwa!-->!-->!-->…
ZAƁEN CIKE GURBI: Ana Zargin Ma’aikatan INEC Da Wani Shugaban PDP Da Siyen Ƙuri’u, Yayin Da Zamfara…
Rundunar ƴan sanda ta kamo manyan PDP biyu ciki har da shugaban jam’iyyar a Iperu, Alhaji Abayomi Tella, tare da ma’aikatan INEC biyu da ake zarginsu ta tanadar kuɗi domin sayen ƙuri'a a zaɓen Remo Federal Constituency.
Wani rahoto ya!-->!-->!-->…
Zaɓen Cike-Gurbi a Jihohi 13: Takunkumin Zirga-Zirga, Dambarwar Jam’iyyu Da Alƙawarin Bayyana…
A yau Asabar, 16 ga Agusta 2025, miliyoyin masu kaɗa kuri’a a jihohi 13 sun yi jerin gwanon a rumfunan zaɓe domin cike guraben kujeru na Majalisar Dattawa, Majalisar Wakilai da majalisun jihohi, a jimillar zaɓuka 16 da suka shafi Jigawa,!-->…
Sai An Ba Da Cin Hanci Kafin A Karɓi Ƙudiri A Majalissa – Hon. Kamfani Auyo
Dan Majalisar Wakilai Hon Ibrahim Usman Auyo daga mazaɓar Hadejia/Auyo/Kafin Hausa a Jihar Jigawa ya yi zafafan tuhume-tuhume cikin wani bidiyo da ya yaɗu inda ya bayyana cewa wasu ƴan majalisa na karɓar kuɗi kafin su ɗauki nauyin gabatar!-->…