Sign in
Sign in
Recover your password.
A password will be e-mailed to you.
Browsing Category
Siyasa
Labaran siyasa daga Najeriya da ketare, tare da nazari, bayanai kan doka da tsarin mulki. Muna bin diddigin zabe, jam’iyyu da manufofi domin taimaka wa masu karatu su yanke shawara. Tattaunawa cikin natsuwa da gaskiya.
Kwankwaso Ya Zargi Gwamnatin Tinubu Da Nuna Wariya Ga Yankin Arewa
Tsohon gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da fifita yankin Kudu wajen rabon albarkatun ƙasa tare da barin Arewa cikin talauci da koma baya.
A wajen!-->!-->!-->…
APC Ta Naɗa Farfesa Nentawe Yilwatda A Matsayin Sabon Shugabanta Na Ƙasa
Jam’iyyar APC ta zaɓi Farfesa Nentawe Yilwatda a matsayin sabon shugaban jam’iyyar na ƙasa bayan murabus ɗin Abdullahi Ganduje saboda dalilan lafiya.
Yilwatda, wanda ke riƙe da muƙamin Ministan Harkokin Jin Ƙai, ya fito ne daga jihar!-->!-->!-->…
Har Yanzu Sanata Natasha Dakatacciya Ce – Majalissar Dattawa
Mai magana da yawun Majalisar Dattawa, Sanata Yemi Adaramodu, ya bayyana cewa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan za ta ci gaba da kasancewa cikin dakatarwar da aka yi mata har sai majalisar ta dawo daga hutun makonni biyu da take ciki.
!-->!-->!-->…
Makusantan Tinubu Na Ɓoye Masa Gaskiyar Abun Da Ke Faruwa A APC Da Najeriya – Adamu Garba
Ɗan jam’iyyar APC kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Adamu Garba, ya zargi wasu makusantan Shugaba Bola Tinubu da ɓoye masa gaskiyar halin da ƙasa da jam’iyyar ke ciki, yana mai cewa su na yaudararsa da cewa komai na tafiya lafiya.
!-->!-->!-->…
DA ƊUMI-ƊUMI: Sanata Natasha Ta Kutsa Cikin Zauren Majalisa Duk Da Yunƙurin Hanata Shiga
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta samu damar shiga harabar Majalisar Dattawa a Abuja bayan da tun farko aka hana ta shiga, duk da hukuncin kotu da ya buƙaci a dawo da ita.
Sanatar, wadda ke cikin dakatarwa na tsawon watanni shida daga!-->!-->!-->…
Ɗan Takara Daga Arewa Ne Kadai Zai Iya Kayar Da Tinubu A 2027, In Ji Wani Lauya Ɗan Kudu
Mai goyon bayan haɗaka kuma lauya Kenneth Okonkwo ya bayyana cewa tilas ne jam'iyyun adawa su tsayar da ɗan takara daga yankin Arewa idan har suna da niyyar kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
A hirar da ya yi a!-->!-->!-->…
ADC Na Ci Gaba Da Karɓar Jiga-Jigan PDP A Jihohin Arewa Maso Gabas
Rahotanni daga jihohin Adamawa, Yobe da Gombe na nuna cewa haɗakar jam’iyyar ADC ta ƴan hamayya na ci gaba da karɓe manyan mambobi daga jam’iyyar PDP, ciki har da shugabanni na ƙananan hukumomi da tsoffin masu riƙe da muƙamai a jihohi.
!-->!-->!-->…
Manyan Ƴan Siyasa Bakwai Ne Ke Zawarcin Kujerar Shugaban Ƙasa Daga Ɓangaren Haɗakar ADC
Tsohon shugaban jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Ralph Nwosu, ya bayyana cewa aƙalla mutane bakwai da suka fito daga babbar haɗakar ƴan adawa ne ake ƙwadaitar da su tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027 domin ƙalubalantar!-->…
NNPP Ta Ce Kwankwaso Ba Shi Da Damar Ƙara Yin Takara A Ƙarƙashinta
Jam’iyyar NNPP ta ce tsohon ɗan takararta na shugaban ƙasa a 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ba shi da hurumin sake amfani da jam’iyyar wajen tsayawa takarar shugabancin ƙasa a 2027.
Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Dr Agbo Major ne ya!-->!-->!-->…
CIKAKKEN LABARI: Batun Karɓa-Karɓa Zai Iya Zamewa ADC Alaƙaƙai, Yayin Da Atiku, Obi Da Amaechi Ke…
Sabon ƙawancen ƴan adawar Najeriya da ke burin kifar da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu a 2027 na ci gaba da ɗaukar hankulan ƴan siyasa da jama'a a faɗin ƙasar, inda jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta zama dandalin fafutukar.
!-->!-->!-->…
Wike Ya Ce Babu Wanda Ya Isa Ya Kore Shi Daga PDP, Yayin Da Kiraye-Kirayen Korarsa Ke Tayar Da Kura
Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya yi watsi da kiraye-kirayen da wasu ke yi na a kore shi daga jam’iyyar PDP, yana mai cewa ba wanda ya isa ya fitar da shi daga jam’iyyar da ya dade yana yi wa aiki da sadaukarwa.
A wata!-->!-->!-->…
APC na Ƙara Gagarar Ƴan’adawa, Yayin da Tinubu Ke Cika Shekaru 2 A Karagar Mulkin Najeriya
A yayin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke cika shekaru biyu a mulki a wannan watan Mayun, jam’iyyar APC na ƙara ƙarfafa mulkinta yayin da manyan ƴan siyasa daga jam’iyyun adawa ke cigaba da sauya sheƙa zuwa APC a shekarar 2025, matakin!-->…
Sule Lamido Zai Ƙaddamar Da Littafin Tarihin Rayuwarsa
Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya shirya ƙaddamar da littafin tarihin rayuwarsa da ya rubuta mai taken Being True to Myself (Faɗawa Kaina Gaskiya) a ranar Talata, 13 ga watan Mayu, a birnin tarayya Abuja, lamarin da ke janyo!-->…
Shugabannin CPC Sun Ce Suna Yin APC Ne Kawai Saboda Buhari, Duk Da Cewa An Mayar Da Su Saniyar Ware
A daidai lokacin da siyasa ke fara ɗaukar zafi gabanin zaɓen 2027, tsoffin shugabannin jihohi na jam’iyyar CPC da ta haɗu da wasu don kafa APC sun bayyana cewa sun ci gaba da kasancewa a jam’iyyar ne saboda biyayya ga tsohon shugaban ƙasa,!-->…
APC Ta Amince Da Gwamna Namadi A Matsayin Ɗan Takararta Tilo A Zaɓen Gwamnan Jigawa Na 2027
Jam’iyyar APC reshen Jihar Jigawa ta bayyana cikakken goyon bayanta ga Gwamna Umar Namadi tare da amincewa cewa ba za ta yarda wani ya tsaya takara da shi ba a zaɓen shekarar 2027, lamarin da ya sa ya zama ɗan takararta tilo a matakin!-->…
Ƴan Ƙwadago Zasu Jinkirta Yunƙurinsu Na Mamaye Ofisoshin Jam’iyyar Labour
Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) ta bayyana cewa sun dakatar da shirin mamaye ofisoshin jam’iyyar Labour Party (LP) a faɗin ƙasa ne domin ba hukumar zaɓe INEC damar nazarin hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara da ta yanke a watan jiya.
!-->!-->!-->…
Wasu Jigajigan PDP Na Zargin Atiku Da Dagula Lamuran Jam’iyyar
Wani mamba na kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na jam’iyyar PDP da tsohon mataimakin sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar, Diran Odeyemi, sun ɗora alhakin rikicin jam’iyyar kan tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, suna zarginsa!-->…
Gwamnonin PDP Sun Haɗa Kai Da Wike Don Samar Da Makomar Jam’iyyar Kafin 2027
Gwamnonin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, sun fara ƙoƙarin warware saɓanin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyar tun bayan zaɓen 2023, domin haɗa kai da farfaɗo da jam’iyyar!-->…
Tinubu Ya Lalata Tattalin Arzikin Najeriya Fiye Da Yanda Buhari Ya Lalata Shi – Hakeem Baba-Ahmed
Tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara a ofishin mataimakin shugaban ƙasa kan al’amuran siyasa, Dr Hakeem Baba-Ahmed, ya caccaki gwamnatin Tinubu, yana mai cewa tattalin arziƙin Najeriya ya taɓarɓare fiye da yadda Muhammadu Buhari ya bar shi.!-->…
Gwamna Abba Kabir Zai Samu Goyon Bayan Ma’aikatan Jihar Domin Yin Tazarce
Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya reshen Jihar Kano (NLC) ta bayyana goyon bayanta ga Gwamna Abba Kabir Yusuf domin ya ci gaba da mulki a karo na biyu, tana mai yabawa da kishinsa ga jin daɗin ma’aikata da ƴan ritaya a jihar.
Shugaban NLC na!-->!-->!-->…