Sign in
Sign in
Recover your password.
A password will be e-mailed to you.
Browsing Category
Siyasa
Labaran siyasa daga Najeriya da ketare, tare da nazari, bayanai kan doka da tsarin mulki. Muna bin diddigin zabe, jam’iyyu da manufofi domin taimaka wa masu karatu su yanke shawara. Tattaunawa cikin natsuwa da gaskiya.
Wani Gwamna Ya Musanta Jita-Jitar Komawarsa Jam’iyyar APC, Ya Ce “Ina Nan A PDP Har Abada”
Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya musanta raɗe-raɗin da ke yawo cewa yana shirin sauya sheƙa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa All Progressives Congress (APC), yana mai cewa “Ina nan a PDP har abada.”
A wata!-->!-->!-->…
Babu Abin Alkhairin Da Tinubu Zai Iya Yi Kafin 2027 – Salihu Lukman
Tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Salihu Lukman, ya bayyana cewa ya daina sa ran Shugaba Bola Tinubu zai kawo wani canji mai ma’ana a Najeriya kafin shekarar 2027.
Lukman ya bayyana haka ne yayin wata hira a shirin!-->!-->!-->…
Dukkan PDP A Delta Ta Koma APC A Wani Babban Taron Siyasa Tare Da Kashim Shettima Da Ganduje
Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori, da tsohon gwamnan jihar, Ifeanyi Okowa, sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC tare da manyan magoya bayansu a wani babban taro da aka gudanar a filin Cenotaph, Asaba, babban birnin jihar.
A wurin!-->!-->!-->…
El-Rufai Bai Isa Ya Sa Mu Bar PDP Ba – Sule Lamido
Tsohon gwamnan Jihar Jigawa, kuma jigo a jam’iyyar PDP, Sule Lamido, ya yi watsi da gayyatar da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi wa ‘yan adawa domin su koma jam’iyyar SDP.
El-Rufai, wanda kwanan nan ya sauya sheka daga APC!-->!-->!-->…
Sanata Natasha Ta Ce Ba Za Ta Ƙyale Hukuncin Da Majalissar Dattawa Tai Ma Ta Ba, Za Ta Ɗau Mataki
Sanata mai wakiltar yankin Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta ce za ta ƙalubalanci hukuncin dakatar da ita na tsawon wata shida a gaban kotu, bayan saɓanin da ta samu da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, kan wurin!-->…
PDP Ta Kira Ortom Da Anyanwu Gaban Kwamitin Ladabtarwa
Jam’iyyar PDP ta kira tsohon gwamnan Jihar Benue, Samuel Ortom, da sakatarenta na kasa mai matsala, Samuel Anyanwu, gaban kwamitin ladabi.
Shugaban kwamitin, Tom Ikimi, ya bayyana a wata sanarwa cewa, sun kira su ne sakamakon koke da!-->!-->!-->…
INEC Ta Ƙare Gabatar Da Kariya A Kotun Zaɓen Edo Ba Tare Da Gabatar Da Shaida Ba
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ƙare gabatar da kariya a gaban kotun sauraron ƙararraƙin zaɓen gwamnan Edo ba tare da gabatar da wata shaida ba.
A ranar Talata, lauyan INEC ya sanar da kotu cewa hukumar ba za ta gabatar da shaidu ba,!-->!-->!-->…
APC Ba Ta Cika Alkawuranta Ba – In Ji Wani Babba A APC
Tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya nemi afuwar ‘yan Najeriya kan gazawar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) wajen cika alkawurran da ta dauka tun bayan karbar mulki.
Fayemi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi!-->!-->!-->…
Jam’iyyun Adawa Sun Fara Shirye-Shiryen Samar Da Haɗaka Don Ƙalubalantar Tinubu A 2027
Wasu ƙungiyoyin siyasa na adawa sun fara ƙoƙarin kafa abin da suka kira "Haɗakar Ƴan Adawa Mafi Girma" don kifar da Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC a zaɓen 2027.
Hon. Ikenga Imo Ugochinyere, wanda ke wakiltar mazaɓar Ideato a!-->!-->!-->…
Najeriya Ta Fi Lagos Tsauri: Tinubu Ya Zama Dole Ya Fifita Ƴan Ƙasa Fiye da Ƴan Kungiyarsa – Farfesa…
Daga Kabiru Zubairu
A wata zuzzurfar hira da jaridar Daily Trust, Farfesa Kamilu Sani Fagge, masanin kimiyyar siyasa daga Jami’ar Bayero ta Kano, ya bayyana yadda wasu gungun mutane ke da tasiri mai ƙarfi a mulkin shugabannin Najeriya,!-->!-->!-->…
Badaru Abubakar: Jagoran Amana da Haɗin Kai, Inji Matasan APC
Ƙungiyar Wayar da Kan Matasa da Dalibai ta Jam’iyyar APC a Jihar Jigawa ta nuna cikakken goyon bayanta ga tsohon Gwamnan jihar kuma Ministan Tsaro na yanzu, Badaru Abubakar, tana mai yabawa da kyakkyawan shugabancinsa a matsayin “mutum mai!-->…
Ƙungiyar Jigawa Youth Agenda Ta Kare Minista Badaru Kan Zarge-Zarge Marasa Tushe
Ƙungiyar Jigawa Youth Agenda ta yi watsi da abin da ta kira zarge-zarge marasa tushe da wani rukunin matasa da ake zargin suna wakiltar APC a Jigawa suka yi wa Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar.
Sanarwar da Shugaban!-->!-->!-->…
Matasan APC a Jigawa Sun Nemi Shugaba Tinubu Ya Sauke Ministan Tsaro Badaru
Ƙungiyar Matasa ta Jam’iyyar APC a Jihar Jigawa ta yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya sake duba nadin da yai wa Ministan Tsaro, Badaru Abubakar, bisa rashin gamsuwa da aikinsa da kuma zargin rashin biyayya ga jam’iyyar.
!-->!-->!-->…
Wata Ƙungiya Mai Sanya Ido Kan Zaɓe Ta Tona Asirin Badaƙalar Zaɓen Jihar Edo
Kungiyar ci gaban al’umma ta Yiaga Africa ta caccaki sakamakon zaɓen gwamnan jihar Edo da aka gudanar a ranar Asabar, tana mai cewa zaɓen ya gaza cika ƙa’idar gaskiya da amana.
Cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Litinin, wadda!-->!-->!-->…
Fintiri Ya Yi Muhimmiyar Magana Kan Makomar Demokaraɗiyyar Najeriya
Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya nuna baƙin cikinsa kan sakamakon zaɓen gwamnan jihar Edo, inda ya bayyana cewa yana tausaya wa ga dimokaradiyyar Najeriya.
A ranar Lahadi ne hukumar zaɓe ta INEC ta bayyana Monday Okpebholo na!-->!-->!-->…
Babbar Kotun Tarayya Ta Yanke Hukunci Kan Makomar Ganduje A Shugabancin APC
Babbar Kotun Tarayya da ke a Abuja, a yau Litinin, ta ƙi amincewa da cire Dr. Abdullahi Umar Ganduje daga matsayin Shugaban Jam'iyyar APC na ƙasa.
A hukuncin da Mai Shari’a Inyang Ekwo ya yanke, kotun ta yi watsi da ƙarar da Ƙungiyar!-->!-->!-->…
Masu Zaɓe Sun Shiga Cikin Dukan Ruwan Sama Don Kaɗa Ƙuri’a A Zaɓen Gwamnan Edo
A yau Asabar, masu zaɓe da dama a yankin Tsakiyar Edo sun fito kwansu da kwarkwatarsu domin zaɓen gwamna duk da ruwan sama da aka tafka.
An fara kaɗa ƙuri’a da misalin ƙarfe 8:40 na safe a Makarantar Firamare ta Eguare, Ujiogba, Ƙaramar!-->!-->!-->…
Dole PDP Ta Yunƙura Yanzu, Ta Jurewa Wike Tsawon Lokaci, Inji Tsohon Shugaba A Jam’iyyar
Tsohon Mai Binciken Kudi na Ƙasa a jam’iyyar PDP, Barista Ray Nnaji, ya ce jam’iyyar ta daɗe tana haƙuri da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike.
Nnaji ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi, inda ya yi tsokaci kan!-->!-->!-->…
Jam’iyyar NNPP A Jigawa Ta Maka Hukumar Zaben Jihar A Kotu Kan Zaɓen Ƙananan Hukumomi
Jam'iyyar NNPP reshen Jihar Jigawa ta garzaya kotu domin neman bayani da amsoshi game da abubuwan da ta ce sun yi kama da kuskure a shirye-shiryen zaɓen ƙananan hukumomi da kansiloli da aka tsara gudanarwa ranar 5 ga watan Oktoba mai zuwa.!-->…
Jam’iyyar APC Ta Amince Cewa Gwamnatin Tinubu Ta Sanya Ƴan Najeriya A Wahala
Jam’iyyar APC mai mulki ta amince cewa manufofin da Shugaba Bola Tinubu ya ƙaddamar sun ƙara jefa ƴan Najeriya cikin wahalhalun tattalin arziƙi.
Wannan amincewar ta fito ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na jam’iyyar,!-->!-->!-->…