Sign in
Sign in
Recover your password.
A password will be e-mailed to you.
Browsing Category
Tattalin Arziki
IMF Ta Buƙaci Najeriya Ta Ƙarawa Ƴan Ƙasa Haraji, Ta Kuma Inganta Tsarin Kasafin Kuɗi Don Rage…
Hukumar IMF ta ce Najeriya tana buƙatar ƙara samun kuɗaɗen shiga daga cikin gida, da inganta tsarin kasafin kuɗi, tare da faɗaɗa tsarin tallafin kuɗi domin fitar da miliyoyin 'yan ƙasa daga kangin talauci, duk da cewa akwai alamun ci gaba!-->…
Yau Majalissar Dattawa Za Ta Yanke Hukuncin Ƙarshe Kan Ƙudirin Gyaran Haraji Da Ke Ci Gaba Da Jawo…
Shugabannin majalisar dattawa sun ɗage amincewa da ƙudurorin gyaran tsarin haraji da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tura zuwa yau Laraba domin samun cikakkiyar tantancewa da muhawara, in ji rahoton PUNCH.
Waɗannan ƙudurori guda huɗu da!-->!-->!-->…
Ƴan Birnin Na Ƙwace Gonakin Ƴan Ƙauye Yayin Da Tsanani Ke Sa Talakawa Ɗiban Guntun Injin Niƙa Don…
Talakawan karkara a faɗin Najeriya na ci gaba da fuskantar matsin rayuwa, inda rahoton Bankin Duniya na watan Afrilu 2025 ya bayyana cewa kashi 75.5 cikin 100 na mazauna karkara na rayuwa ƙasa da layin talauci, lamarin da ke haifar da!-->…
An Gano Fiye Da Naira Biliyan 80 A Asusun Wani Shugaban NNPC
Hukumar EFCC ta kama tsoffin shugabannin kamfanonin gyaran matatun mai na Port Harcourt, Warri da Kaduna tare da wasu manyan jami’an kamfanonin saboda zargin almundahana ta fiye da dala biliyan 2.9 da aka ware don gyaran matatun, yayin da!-->…
An Kafa Kwamitin Da Zai Jagoranci Tallafawa Matan Jigawa A Fannin Tattalin Arziƙi
Gwamnatin Jihar Jigawa ta ƙaddamar da wani kwamiti mai mahimmanci da ake kira Multi-Sectoral Coordination Steering Committee domin jagorantar aiwatar da shirin Nigeria for Women Programme (NFWP), wani haɗin gwiwa ne tsakanin Bankin Duniya!-->…
Darajar Naira Ta Ƙara Faɗuwa A Kasuwar Gwamnati
Naira ta sake fuskantar zubewar daraja a kasuwar musayar kudade ta hukuma a ranar Jumma’a, inda ta faɗo zuwa N1,602.18 a kan kowace dala, wanda hakan ke nuni da faɗuwar N5.49 daga yadda take a baya.
Bayanai daga shafin yanar gizo na!-->!-->!-->…
NG-CARES: Masu Cin Gajiyar Shirin Sun Sa Hannu Kan Yarjejeniyar Amfani da Tallafi a Jigawa
Daga Ibrahim Ibrahim
Masu cin gajiyar shirin Nigeria COVID-19 Action Recovery and Economic Stimulus (NG-CARES) Results Area II a Jihar Jigawa sun sa hannu kan wata yarjejeniyar amfani da tallafin don tabbatar da ingantaccen amfani da!-->!-->!-->…
Afirka Ta Kudu Ta Goyi Bayan Shirin Najeriya Na Shiga Ƙungiyar G20
Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya yi alƙawarin goyon bayan Najeriya wajen shiga cikin Ƙungiyar G20, yana bayyana ƙasar a matsayin “ƙasa ƴar’uwa mai daraja.”
Yayin ƙaddamar da jagorancinsa na G20 a Cape Town ranar Talata,!-->!-->!-->…
Majalisar Dattawa Ta Sanya Hukunci Kan Masu Fitar da Masara daga Najeriya
A ranar Laraba, Majalisar Dattawa ta amince da gyaran dokar da ta haramta fitar da masara da ba a sarrafa ba, inda ta tanadi hukuncin ɗaurin shekara guda ga waɗanda suka karya wannan doka.
Dokar, wadda ta samo asali daga Majalisar!-->!-->!-->…
Masana Sun Ce, Ƙaruwar GDP Ba Ta Wakilci Halin Ƙuncin Da Jama’a Ke Ciki Ba
Duk da ƙaruwar tattalin arziƙin Najeriya da kashi 3.46% a kwata ta uku ta 2024, masana tattalin arziƙi sun ce alƙaluman ba sa nuna matsalolin da al’umma ke fuskanta.
Farfesa Segun Ajibola, tsohon Shugaban Cibiyar Bankunan!-->!-->!-->…
Manyan Ƴan Kasuwa Sun Yi Tir Da Rahoton NBS Kan Cigaban Tattalin Arziƙin Najeriya
Rahoton Hukumar Ƙididdiga ta Kasa (NBS) wanda ya nuna ƙaruwar tattalin arziƙi da kashi 3.46% da kuma raguwar rashin aikin yi zuwa kashi 4.6% ya gamu da suka daga kungiyar ƴan kasuwa ta NACCIMA.
Shugaban NACCIMA, Dele Kelvin Oye,!-->!-->!-->…
Tinubu Ya Nuna Jin Daɗinsa Kan Cigaban Tattalin Arziƙin Najeriya, Ya Buƙaci A Cigaba Da Haƙuri
Shugaba Bola Tinubu ya nuna farin cikinsa kan ƙaruwar tattalin arziƙin Najeriya da ya kai kashi 3.46% a ƙarshen kwata ta uku ta 2024, yana mai danganta hakan da gyare-gyaren tattalin arziƙi da gwamnatinsa ta yi, amma ya ce akwai bukatar!-->…
Za A Cigaba Da Cin Bashi Wa Najeriya Duk da Yawan Kuɗaɗen Shigar Da Ake Samu — Ministan Kudi
Gwamnatin Najeriya za ta ci gaba da ciwo bashi don cike kasafin kuɗi, duk da cewa an zarce hasashen kuɗaɗen shigar da akai tsammani a wasu bangarori, in ji Ministan Kudi, Wale Edun.
Da yake magana a gaban kwamitin haɗin gwiwa na!-->!-->!-->…
Najeriya Da Brazil Sun Ƙulla Yarjejeniya Don Inganta Noma A Ƙananan Hukumomi 774
A cikin wani babban mataki na sauya fannin aikin gona a Najeriya, Gwamnatin Tarayya ta rattaba hannu kan yarjejeniya da Fundação Getulio Vargas (FGV) na Brazil don bunƙasa aikin gona ta hanyar haɗin gwiwar kamfanoni masu zaman kansu. !-->…
Majalisa Ta Amince Da Ciyo Bashin Sama da Naira Tiriliyan 2 Da Tinubu Ya Nema Duk Da Matsalolin…
Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na neman bashin sama da naira tiriliyan 2 (dala biliyan 2.2), bayan kaɗa ƙuri’ar amincewa ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau!-->…
IMF Ta Ce Sauye-sauyen Tattalin Arzikin Gwamnatin Tinubu Ba Sa Amfani
Wani sabon rahoton Asusun Bayar da Lamuni na Duniya (IMF) ya bayyana cewa manufofin tattalin arzikin da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta aiwatar cikin watanni 18 da suka gabata ba su haifar da sakamako mai ma’ana ba.
Rahoton, wanda!-->!-->!-->…
Gwamnatin Tarayya Ta Raba Kuɗin Tallafi ₦25,000 Ga Ƴan Najeriya Miliyan 25
Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa sama da ƴan Najeriya miliyan 25 ne suka ci gajiyar shirin raba kuɗin tallafi na ₦25,000 zuwa yanzu, abin da ke temakawa matuƙa yayin da ake aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki.
Ministan Kuɗi, Mista!-->!-->!-->…
Gwamnoni Sun Nemi A Janye Sabuwar Dokar Harajin Tinubu Saboda Damuwa Kan Yankin Arewa
Gwamnonin jihohi 36 na Najeriya sun haɗu don kiran a gaggauta janye sabuwar dokar haraji ta ƙasa, suna neman a nemi cikakkiyar shawarar juna kafin aiwatar da shirin shugaban ƙasa Tinubu na gyaran haraji.
Buƙatar gwamnonin, wadda aka!-->!-->!-->…
Gwamnoni Sun Amince Da Cewa Ana Fama Da Yunwa A Najeriya, Sun Kuma Yabi Tinubu
Gwamnonin Najeriya a karkashin inuwar Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) sun tabbatar da cewa ana fama da yunwa a ƙasar, sannan sun jinjina wa sauye-sauyen da Shugaba Bola Tinubu ya samar.
Sun bayyana hakan ne bayan wata doguwar ganawa!-->!-->!-->…
Fiye Da Mata 2,000 Sun Amfana da Tallafin Naira Miliyan 135 Daga Uwargidan Gwamnan Jigawa
Daga Mika’il Tsoho, Dutse
Fiye da mata 2,000 da marasa galihu a Jihar Jigawa sun amfana da tallafin Naira miliyan 135 daga uwargidan gwamnan jihar, Hajiya Hadiza Umar Namadi.
Shirin na nufin rage raɗaɗin da cire tallafin man fetur ya!-->!-->!-->!-->!-->…