Sign in
Sign in
Recover your password.
A password will be e-mailed to you.
Browsing Category
Tsaro
Rahotanni kan tsaro: rundunonin tsaro, dokoki, dabaru da wayar da kai. Muna tattauna hanyoyin kare al’umma da inganta zaman lafiya. Rahotanni kan ’yan sandan Najeriya, sojoji, da sauran hukumomin tsaro.
Jiragen Yaƙi Sun Tilasta Wa Ƴan Bindiga Tserewa, Yayinda Mutane 62 Da Aka Sace Suka Tsere Daga…
Sojojin sama da ƙasa sun yi wani gagarumin samame a yankin Danmusa na Jihar Katsina a ranar Asabar da misalin ƙarfe 5:10 na yamma, inda harbin jiragen sama ya tilastawa wasu ƴan bindiga dake da mafaka a wajen tserewa, kuma hakan ya baiwa!-->…
An Kama Ɗan Shugaban Boko Haram A Chadi, Ana Zargin Yana Jagorantar Ƙungiyar Ƴan Ta’adda
A Chadi, jami’an tsaro sun kama wani matashi da ake zargin ɗan marigayi Mohammed Yusuf ne mai suna Muslim Mohammed Yusuf, tare da wasu biyar da ake zargin su membobin wata ƙungiyar ƴan ta’adda ne a yankin Tafkin Chadi.
Wata majiyar!-->!-->!-->…
Ƴan Sanda Sun Cafke Wani Sufeta Ɗan’uwansu Da Wasu Fararen Hula Bisa Zargin Fashi Da Makami
Rundunar ƴan sanda ta Edo ta cafke wani jami’in ƴan sanda mai aiki tare da fararen hula uku bisa zargin azabtarwa, karɓar rashawa da kuma fashi da makami da ya addabi mazauna Benin.
Kakakin rundunar, Moses Yamu ne ya bayyana hakan a!-->!-->!-->…
Hukumar Ƴan Sanda Ta Samar Da Sabon Tsarin Ɗaukar Sabbin Jami’ai Da Ma’aikata
Hukumar Ƴan Sanda (Police Service Commission, PSC) ta sanar a shafinta ranar 15 ga Agusta, 2025 cewa ta sayi sabon portal na ɗaukar ma’aikata domin rarraba aikin ɗaukar ƴan sanda da tabbatar da gaskiya da adalci.
A sanarwar, hukumar ta!-->!-->!-->…
DSS Sun Yi Babban Kamu, Sun Kama Wani Ƙasurgumin Shugaban Ƴan Ta’adda
Daily Trust ta tabbatar da cewa Abubakar Abba, jagoran sabuwar ƙungiyar ta’addanci mai suna Mahmuda, yana hannun Hukumar Tsaro ta DSS bayan an cafke shi a Jihar Neja.
An gano cewa wannan shugaban ta’addanci, wanda jami’an sirri suka!-->!-->!-->…
Wata Kotu Ta Bayyana APC Da PDP A Matsayin Ƙaungiyoyin Ƴan Ta’adda Sai Dai PDP Ta Musanta
PDP ta ƙaryata rahotannin cewa wata Kotun Tarayya a Kanada ta ayyana PDP da APC a matsayin ƙungiyoyin ta’addanci, inda gwamnatin tarayya ke shirin fitar da martani a yau, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Mamba a Kwamitin Zartarwa,!-->!-->!-->…
Gwamnatin Tarayya Za ta Gina Tashoshin Mota A Jihohi 6 Kan Naira Biliyan 142
Gwamnatin Tarayya ta amince da gina sabbin tashoshin mota a kowane yanki shida na Najeriya, a kan kuɗi N142,028,576,008.17, wanda zai inganta sufuri da rage haɗura a kan manyan tituna.
Ministan Sufuri, Sanata Sa’idu Alkali, ya bayyana!-->!-->!-->…
Tsoron Boko Harama Ya Sa Ɗaruruwan Ƴan Najeriya Tafiya Kamaru Domin Kwana A Kan Tituna
Ɗaruruwan mazauna Kirawa a jihar Borno da Boko Haram suka raba da muhallansu sun koka kan halin ƙuncin rayuwa, inda suka bayyana cewa suna kwana a Kamaru cikin tsoron hare-haren mayaƙa sannan su dawo Najeriya da safe.
Sun bayyana wa!-->!-->!-->…
Jam’iyyu A Kano Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya Kafin Zaɓen Cike Gurbin Ranar Asabar
Shugabannin jam’iyyun siyasa a jihar Kano sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya domin tabbatar da gudanar da zaɓukan cike gurbi cikin lumana a ranar Asabar, 16 ga Agusta 2025.
Kakakin rundunar ƴan sandan a jihar, SP Abdullahi!-->!-->!-->…
Ƙananan Yara Na Fuskantar Gargaɗin Ƴan Sanda A Kano Saboda Tuƙa Adaidaita Sahu
Rundunar Ƴan Sanda a Jihar Kano ta yi kira mai ƙarfi ga masu keke Napep, musamman ƙananan yara, da kuma direbobi masu karya dokar fitilun kan hanya.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce ana samun “tuƙin ganganci” daga!-->!-->!-->…
An Kama Wasu Masu Garkuwa Da Mutane Yayin Da Suke Raba Kuɗi
Rundunar Ƴan Sanda a Jihar Ondo ta cafke mutane uku da ake zargi da garkuwa da ma’aikatan Jami’ar Adekunle Ajasin, Akungba-Akoko.
Waɗanda aka sace sun haɗa da Omoniyi Eleyinmi, jami’in kula da harkokin gudanarwa na Kwalejin Ilimi, da!-->!-->!-->…
EFCC Ta Tsare Tsohon Gwamnan Sokoto Tambuwal Kan Zargin Cire Biliyoyin Nairori
Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya shiga hannun hukumar EFCC inda aka yi masa tambayoyi kan zargin cire kuɗaɗen gwamnati har Naira biliyan 189 a yanayin da ya saɓa da dokar hana safarar kuɗi ta 2022.
Rahotanni sun!-->!-->!-->…
Jihohi da Yawan Masu Nema: Masu Neman Aiki Miliyan 1.91 Na Rige-Rigen Samun Aikin Para-Military A…
Hukumar Civil Defence, Correctional, Fire and Immigration Services Board (CDCFIB) ta bayyana cewa sama da masu neman aiki miliyan 1.91 ne suka yi rajista don neman guraben aiki a hukumomin tsaro na para-military a wannan shekarar.
!-->!-->!-->…
Zargin Kisa: Wanda Ake Tuhuma Da Kashe Jami’in Civil Defense Ya Mutu Yayin Yunƙurin Tserewa
Daga: Mika'il Tsoho, Dutse
Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) ta bayyana kama wani mai suna Salisu Muhd mai shekaru 45, da ake zargi da hannu a kisan gilla da aka yi wa jami’insu, Bashir Adamu Jibrin, a kasuwar Shuwarin a!-->!-->!-->…
Ƴan Sanda Sun Musanta Azabtar da Sowore, Yayinda Ya Mayar Da Martani Mai Zafi
Rundunar ƴan sanda ta ƙasa ta fito da bayani mai tsawo don ƙaryata zargin cewa an azabtar da ɗan gwagwarmayar siyasa, Omoyele Sowore, yayin tsare shi bisa tuhume-tuhumen laifuka da suka haɗa da amfani da jabun takardu da amfani da yanar!-->…
ADC Ta Caccaki Gwamnatin Tinubu Kan Harajin Ƴan Bindiga da Ƙauyen da Aka Bar Shi a Kwara
Jam’iyyar ADC ta nuna takaici matuƙa kan rahoton karɓar haraji na naira miliyan 56 daga manoma a Jihar Zamfara da ƴan bindiga suka yi, tare da hoton faifan bidiyon wani ƙauye a Ifelodun Jihar Kwara, da ƴan ƙauyen suka fice baki ɗaya saboda!-->…
Zamfara: Ƴan Bindiga Sun Kashe Waɗanda Suka Kama Bayan Sun Karɓi Kuɗin Fansa Sama Da Naira Miliyan…
Al’umma a ƙauyen Banga da ke ƙaramar hukumar Kaura Namoda a Jihar Zamfara sun shiga cikin alhini bayan da aka kashe mutane 38 da aka sace musu, duk da cewa an biya ƴan bindigar sama da naira miliyan 50 a matsayin kuɗin fansa.
Shugaban!-->!-->!-->…
Niger: Haɗakar Rundunar Tsaro Ta Hallaka Ƴan Bindiga Da Dama A Ƙaramar Hukumar Shiroro, Ta Kuma Rasa…
A jihar Neja, sojojin Najeriya tare da haɗin gwiwar rundunar tsaro ta haɗaka da goyon bayan bayanan sirri daga hukumar DSS sun kashe aƙalla ƴan bindiga 45 a wani farmaki da suka kai a garin Iburu da ke ƙaramar hukumar Shiroro.
Rahotanni!-->!-->!-->…
Ƴan Sanda Sun Cafke Wanda Ya Kashe Tsohuwar Matarsa Da Ɗan Fashi A Jigawa
Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta cafke mutum biyu da ake zargi da hannu a kisan kai da fashi da makami a sassa daban-daban na jihar.
Kakakin rundunar, SP Shi’isu Adam, ya bayyana cewa Iliyasu Musa, mai shekaru 40 daga ƙauyen!-->!-->!-->…
An Bindige Jami’in NDLEA Har Lahira Yayin Da Yake Bakin Aiki
Wasu da ake zargin masu fataucin miyagun ƙwayoyi ne sun bindige wani jami’in hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), mai suna Jide, a wani samame da aka kai a unguwar Ita’nla da ke garin Ondo.
Rahotanni sun ce!-->!-->!-->…