Sign in
Sign in
Recover your password.
A password will be e-mailed to you.
Browsing Category
Tsaro
Rahotanni kan tsaro: rundunonin tsaro, dokoki, dabaru da wayar da kai. Muna tattauna hanyoyin kare al’umma da inganta zaman lafiya. Rahotanni kan ’yan sandan Najeriya, sojoji, da sauran hukumomin tsaro.
Masu Fyaɗe 5 Sun Yi Lalata Da Ƙaramar Yarinya A Jigawa, Ɗaya A Cikinsu Yana Da Ƙanjamau
Jami’an ƴansanda a Jigawa sun cafke mutane biyar da ake zargi da yin lalata da ƴar ƙaramar yarinya ƴar shekara 14, inda aka samu ɗaya a cikinsu ɗauke da ciwon ƙanjamau.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar Ƴansandan Jihar Jigawa, DSP!-->!-->!-->…
‘Zai Iya Zamewa Yaƙi,’ Burkina Faso Da Mali Sun Goyi Bayan Sojojin Nijar Sun Kuma Gargaɗi ECOWAS
Sojojin da ke mulki a Burkina Faso da Mali sun yi gargaɗi kan yunƙurin amfani da ƙarfin soji a kan sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar, inda suka ce yin hakan tsokanar yaƙi ce a Afirka ta Yamma.
Gargaɗin wanda ya zo a wata sanarwar!-->!-->!-->…
Ƴansanda Sun Kama Ɓarayin Babura A Bauchi
Jami’an ƴansanda a Jihar Bauchi sun sami nasarar kama wasu mutane guda biyu waɗanda ake zargi da sun ƙware wajen ƙwatar babura daga masu su a yankin Gudum Hausawa da ke jihar.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar Ƴansandan Jihar Bauchi,!-->!-->!-->…
YANZU-YANZU: Gwamna Fintiri Ya Sanya Dokar Hana Fita A Jihar Adamawa
Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya ayyana dokar hana fita ta tsawon awanni 24 a jihar, biyo bayan hare-haren da ƴanbindiga suke kaiwa mutane a babban birnin jihar, Yola.
Gwamnan ya bayyana cewar, dokar ta fara aiki nan take!-->!-->!-->…
Ƴan Bindiga Sun Kashe Babban Malami, Manoma 5, Sun Yi Garkuwa Da Mutum 40 A Kaduna
Wasu ƴanbindiga sun kashe manoma aƙalla shida ciki har da Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Izala, Malam Yakubu Bugai a Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna.
Haka kuma, an rawaito cewa, ƴanbindigar sun kuma yi garkuwa da mutane!-->!-->!-->…
Hukumar Yaƙi Da Cin Hanci Ta Kano Ta Kama Mutane 8 Da Zargin Karkatar Da Naira Biliyan 4
Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafen Al’umma da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano ta tabbatar da cewar, ta kama mutane takwas da ake zargi da karkatar da kuɗaɗen da yawansu ya kai naira biliyan huɗu na Kamfanin Samar da Kayan Noma na!-->…
Ƴan Najeriya Miliyan 14.3 Ne Ke Ta’ammuli Da Miyagun Ƙawayoyi – NDLEA
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa, NDLEA ta ce, akwai aƙalla ƴan Najeriya miliyan 14 da dubu 300 da ke ta’ammuli da miyagun ƙwayoyi.
Kwamandar Hukumar ta Jihar Ogun, Ibiba Odili ce ta bayyana hakan lokacin ƙaddamar da!-->!-->!-->…
Ba Da Sani Na Na Ciri Kuɗi Har Sau 5 A Katin Kostoma Ba – Wani Ma’aikacin Banki
Wani tsohon ma’aikacin banki mai suna, Uchenna Emmanuel ya amsa laifin cewar ya yi amfani da katin kostoma wajen cirar kuɗi har sau biyar.
Wanda ake zargin, wanda tsohon mai biyan kuɗi a banki ne, ya amsa laifin nasa ne jiya Juma’a!-->!-->!-->…
An Damƙe Mai Yin Takin Zamanin Bogi, Yana Sawa A Buhun Takin Zamanin Gaske
Hukumar Kula da Ingancin Kayayyaki ta Najeriya, SON, a Jihar Bauchi ta ce, jami’anta sun damƙe wani mai sarrafa takin zamanin bogi a garin Chinade da ke Ƙaramar Hukumar Katagum ta jihar.
Hukumar ta kuma ce, ta samu nasarar ƙwace aƙalla!-->!-->!-->…
Sojoji Sun Kashe Ƴanta’adda 59, Sun Kama 88
Rundunar Sojojin Najeriya ta tabbatar da kashe aƙalla ƴanta’adda 59 tare da kama wasu 88, sannan kuma sojojin sun samu nasarar kama masu garkuwa da mutane 10 da adadi mai yawa na masu satar ɗanyen mai.
Mai Magana da Yawan Rundunar!-->!-->!-->…
Wani Mutum Ya Mutu Yayinda Yake Gujewa Kare
Wani mutum da aka bayyana sunansa da Mohammed Faworaja ya gamu da ajalinsa a Ilorin, babban birnin Jihar Kwara a lokacin da yake gujewa kare.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa, lamarin ya faru ne a kusa Asa Dam da ke yankin Warah-Osin a!-->!-->!-->…
Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Ƴanmata Da Zawarawa 23 A Zamfara
Wasu ƴanbindiga da ake zargin ƴan ta’adda ne sun yi garkuwa da mata ashirin da uku a garin Damaga na Ƙaramar Hukumar Maradun a Jihar Zamfara.
Wani mazaunin yankin, Malam Ahmed Mohammed ne ya bayyana hakan a tattaunawarsa da DAILY POST!-->!-->!-->…
DA ƊUMI-ƊUMI: Kotu Ta Yi Watsi Da Buƙatar DSS Na Ci Gaba Da Tsare Emefiele
Babbar Kotu da ke Abuja ta yi watsi da buƙatar Hukumar Tsaro da Farin Kaya, DSS, ta ƙarin kwanaki 14 tana tsare da dakataccen Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele.
DSS dai ta gabatar da buƙatarta ga kotun ne a jiya Laraba,!-->!-->!-->…
Za A Ci Gaba Da Tsare Waɗanda Ake Zargi Da Ƙaryar KAROTA Su 25 A Kano
Wato Kutun Majistare a Kano jiya Talata, ta bayar da umarnin ci gaba da tsare wani da ake kira Aminu Salisu da wani Kamilu Yusuf da kuma wani Baba Jibril da sauran wasu mutane 22 waɗanda aka kama suna mallakar takardun bogi na Hukumar Kula!-->…
An Ƙara Kama Emefiele Kan Zargin Ta’addanci
An ƙara kama dakataccen Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele a ranar Talata bayan Babbar Kotun Tarayya da ke Lagos ta bayar da belinsa a kan kuɗi naira miliyan ashirin.
Jami’an Tsaro na Farin Kaya, DSS, ne suka kama shi!-->!-->!-->…
An Kama Ƴan Boko Haram Da Ke Kitsa Kai Hari Gidan Atiku
An kama wasu ƴan ƙungiyar Boko Haram da ake zargi da kitsa kai hari garin Yola, Jihar Adamawa gidan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar.
Wani wanda ake zargin mai shekaru 29 a duniya, Jubrila Mohammed, wanda ya amsa cewar!-->!-->!-->…
Ƴan Bindiga Sun Sace Wani Boka A Anambra
Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun yi garkuwa da wani shahararren boka ɗan asalin Jihar Anambra, mai suna Chinedu Nwangwu a ɗaya daga cikin otel ɗinsa da ke Ƙaramar Hukumar Idemili ta Arewa.
Bokan da aka fi sani da Akwa!-->!-->!-->…
Sojoji Sun Farmaki Ofishin KAEDCO Da Ke Kebbi, Sun Ci Zarafin Ma’aikata Saboda Rashin Wutar Lantarki
Sojoji dauke da makamai sun kai farmaki ofishin Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kaduna KAEDCO a jihar Kebbi tare da cin zarafin ma’aikatan da suka kasa samar musu da wutar lantarki a barikinsu.
Manajan kamfanin na jihar Kebbi,!-->!-->!-->…
‘Yan Sa-Kai Sun Kashe Makiyaya 12 A Sokoto
Kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetta Allah ta yi shelar cewar ‘Yan sa-kai a jihar Sokoto sun halaka mambobin ta 12 sakamakon wani farmakin da suka kai a matsugunansu da ke yankin Gwadabawa.
RFI Hausa ta rawaito cewa, shugaban kungiyar ta!-->!-->!-->…
NDLEA Ta Kara Wa’adin Daukar Sabbin Ma’aikatan Da Take Yi
Shugaban Hukumar Hana Sha da Fatucin Miyagun Kwayoyi, NDLEA, Buba Marwa, ya amince da kara wa’adin sati guda kafin a rufe shafin daukar sabbin ma’aikata na hukumar.
Buba Marwa ya bayyana hakan ne a sanarwar da Daraktan Yada Labarai da!-->!-->!-->…