Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

CIKAKKEN LABARI: Sauye-Sauyen Tsarin Mulki Da Majalisar Dattawa Ke Shirin Samarwa A Najeriya

Kwamitin Majalisar Dattawa kan Gyaran Kundin Tsarin Mulki ya karɓi buƙatu 31 na ƙirƙiro sabbin jihohi da wasu 18 na samar da ƙarin ƙananan hukumomi daga sassa daban-daban na Najeriya, kamar yadda Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar, Sanata Opeyemi Bamidele ya bayyana.

A cewar wata sanarwa daga ofishin yaɗa labaransa, an bayyana cewa za a gudanar da zaman sauraron ra’ayoyin jama’a daga ranar 4 zuwa 5 ga Yuli a jihohi shida da ke wakiltar kowanne yanki na siyasa a Najeriya.

Zaman na yankin Kudu maso Gabas zai gudana ne a jihar Enugu, sai Ikot Ekpene a Akwa Ibom a Kudu maso Kudu, sai Jos a Arewa ta Tsakiya, sai kuma Maiduguri a Arewa maso Gabas, yayin da Kano ke karɓar baƙuncin taron a Arewa maso Yamma – ko da yake an ɗage zaman Kanon domin girmama marigayi Aminu Dantata.

Kowanne yanki zai kasance ƙarƙashin jagorancin wani jigo daga majalisar, inda Sanata Akpabio zai kula da Kudu maso Kudu, Sanata Bamidele zai kula da Kudu maso Yamma, da dai sauransu.

Sanata Bamidele ya bayyana cewa “akwai buƙatu shida daga Arewa maso Yamma, takwas daga Arewa ta Tsakiya, biyar daga Kudu maso Gabas, shida daga Arewa maso Gabas, shida daga Kudu maso Kudu da hudu daga Kudu maso Yamma.”

Haka kuma, wasu jiga-jigan Abuja na neman a ba Babban Birnin Tarayya Abuja matsayin jiha.

WANI LABARIN: Kotu Ta Ba Wa Sanata Natasha Nasara Kan Akpabio, Ta Kuma Ci Tararta

Dangane da buƙatun ƙirƙiro ƙarin ƙananan hukumomi kuwa, akwai guda bakwai daga Arewa maso Yamma, guda biyar daga Arewa ta Tsakiya, guda ɗaya daga Arewa maso Gabas, uku daga Kudu maso Kudu da guda ɗaya daga Kudu maso Gabas da Kudu maso Yamma.

A cewar Bamidele, “kwamitin zai kuma duba buƙatun samar da ƴan sandan jihohi da kwamitocin tsaro na jihohi domin taimaka wa gwamnoni wajen yaƙi da matsalolin tsaro.”

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da matsalolin tsaro kamar garkuwa da mutane, fashi da makami da harin ƴan bindiga ke ƙara tsananta a faɗin kasar.

Kwamitin zai kuma tattauna kan batun bai wa gwamnoni dama su kafa dokoki kan harkar sufurin ruwa, ƙwadago da safarar kaya tsakanin jihohi ta hanyar canza wasu ɓangarori daga jerin ayyukan da gwamnatin tarayya kaɗai ke da iko a kai zuwa na haɗin gwiwa.

Bugu da ƙari, an gabatar da ƙudurin gyara dokar zaɓe domin bada damar tsayawa takara ba tare da jam’iyya ba da kuma kaɗa ƙuri’a daga ƙasashen waje domin shigar da ƴan Najeriya mazauna ƙasashen ƙetare cikin harkokin siyasa.

Sauran gyare-gyaren sun haɗa da ɗora wa shugabanni nauyin miƙa kasafin kuɗi kafin wani lokaci da kuma rage wa’adin da za a iya cire kuɗi daga asusun gwamnati ba tare da kasafin kuɗi ba daga watanni shida zuwa uku.

“Akwai kuma ƙudurin da ke neman duba tsarin rabon kuɗaɗen shiga don a haɗa da kuɗin da jihohi ke tarawa da kansu,” in ji Bamidele.

Bayan sauraron ra’ayoyin jama’a, kwamitin zai tattara duk abubuwan da aka gabatar, ya shirya shawarwari sannan ya fara aiwatar da tsarin canjin kundin tsarin mulkin.