Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

CIKAKKEN SHARHI KAN TATTALIN ARZIƘI: Alƙaluma Masu Kyau Amma Ƴan Najeriya Na Cikin Ƙunci

Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta bayyana cewa tattalin arziƙin Najeriya ya ƙaru da kaso 3.13 cikin ɗari a wannan mako, yayin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ci gaba da riƙe kuɗin ruwa a kaso 27.5 cikin ɗari karo na uku a jere.

Duk da wannan sakamako na alƙaluman tattalin arziƙi da ke bayyana ci gaba, masana irinsu Bismarck Rewane sun yi gargaɗin cewa, in ba ƴan Najeriya sun fara jin sauyi a rayuwarsu ba, ba za a iya cewa an samu ci gaba ba.

“Abin da muke buƙata shi ne sauyi na zahiri da zai shafi rayuwar jama’a, ba wai kyawawan alƙaluma kawai ba,” in ji Rewane a wata hira da ya yi da Channels TV.

Ya bayyana cewa yanke shawarar da kwamitin kuɗi na CBN ya yi na ci gaba da riƙe kuɗin ruwa ya dace, ganin yadda hauhawar farashi ke ci gaba da zama barazana.

“An yi taro goma cikin shekaru biyu da suka gabata, an ƙara kuɗin ruwa sau shida, an bar shi yadda yake sau uku, yayin da sau ɗaya aka rage shi,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa duk da samun nasarar sauƙar da hauhawar farashi da ɗan ƙaruwar daraja da naira ta samu, akwai buƙatar hankali da kyakkyawan tsari domin guje wa girgizar kasuwa.

A cewarsa, “Farashin fetur ya ragu da kaso 4.4 cikin ɗari zuwa naira 865, naira ta ƙaru da kaso 6.6 cikin ɗari, amma wannan ba ya nufin mun samu isasshen ci gaba da za a yi shelar samun nasara.”

Rewane ya bayyana cewa tattalin arziƙin Najeriya yanzu yana da darajar kusan dala biliyan 250, kuma yana matsayi na huɗu a nahiyar Afirka bayan Afirka ta Kudu, Masar da Aljeriya.

Duk da wannan, ya jaddada cewa, “Idan har muna son kaiwa dala tiriliyan guda nan da shekarar 2030 kamar yanda gwamnati ke hasashe, muna buƙatar ci gaban tattalin arziƙi na kaso 15 cikin ɗari a shekara, amma yanzu muna da kaso 3.1 cikin ɗari.”

Ya koka da cewa samun kowanne ɗan Najeriya yana ƙasa da na yawancin ƙasashen da Najeriya ke fafatawa da su, inda ya ce: “Samun ɗan Najeriya yana $1,000 ne, yayin da na ɗan Afirka ta Kudu ya kai $5,000.”

WANI LABARIN: PDP Na Tuntunɓar Peter Obi Don Ya Dawo Cikinta Domin Yai Mata Takara A 2027

A ɓangaren hauhawar farashin kaya, ya bayyana cewa farashin buhun shinkafa ya ƙaru daga naira 84,000 zuwa naira 87,000, yayin da gero ya ragu daga naira 46,000 zuwa 33,000.

Haka kuma, farashin tumatir ya ƙaru da kaso 83 cikin ɗari, yayin da doya da ƙwai suka ƙaru da kaso 22 da 5.7 cikin ɗari bi da bi.

“Kayan abinci sun fi ƙaruwa fiye da yadda ake tsammani, kuma hakan yana shafar talaka kai tsaye,” in ji Rewane.

Ya kuma bayyana cewa bayan ƙaruwa a farashin mai, kuɗin mota daga Legas zuwa Benin yanzu ya kai naira 28,250, yayin da tikitin jirgi daga Legas zuwa Abuja ya kai naira 200,000.

Har ila yau, maganin Lonart syrup ya ƙaru da kaso 21 cikin ɗari, daga naira 3,800 zuwa 4,600, sai dai farashin gas ya ragu daga naira 15,060 zuwa 11,875.

Amma a cewarsa, “Me za ka dafa da gas idan babu abincin da za a dafa?”

Ya gargaɗi gwamnati da kada ta dogara da kyawawan alƙaluma kawai yayin da mutane ke cikin ƙunci.

“Abin da muke guje wa shi ne fararen alƙaluma da bakin cikin jama’a. Dole jama’a su ji daɗin rayuwa,” in ji shi.

Ya kammala da cewa dole ne gwamnati ta tabbatar da raba moriyar ci gaban tattalin arziƙi cikin adalci, domin rage talauci da samar da ayyukan yi ga al’umma.