Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

CIRE TALLAFI: Shawara Ga Gwamnan Jigawa, Namadi

Daga: Ahmed Ilallah

Koda yake, tun lokacin hawan wannan gwamnatin da shelar Shugaba Tinubu na kawo ƙarshen tallafin Man-Fetur a Nijeriya. Gwamantoci kama daga ta Tarayya da jihohi suke ta lissafin yadda zasu kawo wa al’umominsu sauƙin raɗaɗin da wannan cire tallafi ya jawo, duk da kasancewa ita kanta Gwamnatin Tarayyar ba ta fidda cikakkiyar matsaya kan yadda zata bayar da wannan tallafin ba, tun da ta fasa raba dubu takwas ga mataulatan magidanta don samun sauƙin wannan raɗaɗi.

Duk da kasancewar a makon da ya gabata a wajen rabon tattalin arziƙin ƙasa na wata-wata, an yi nuni da cewa, za a yi amafani da rijistar mabuƙata ta jihohi don bayar da tallafi, da kuma umartar gwamnoni da fito da tsare-tsaren kawo sauƙin raɗaɗi, ya haɗa da su biya basussukan ma’aikatansu da ƴan fansho na albashi, alawus da kuma garatuti duk dai don rage talaucin da al’uma suke ciki. Amma su kan su jihohin da yawa a cikinsu, ba su kai ga matsaya ba a kan wannan lamari, duk da cewa wasu sun rage ranakun aiki ga ma’aikata don rage kashe kuɗin mota zuwa wajen aiki, da kuma wasu alƙawuran ga mataulata da kuma, ma’aikata.

Shawara ga Maigirma Gwamna:

Noma Da Ƙamfar Talauci A Jigawa

Mu Jihar Jigawa dama tun kafin zuwan wannan ibtal’in, muna cikin jihohin da suka fi kowa fama da ƙamfar talauchi a wannan ƙasa. Sir, a ruhoton ƙiddiddiga a kan talauchi na Najeriya ta kwanan nan, Jigawa na cikin jihohi biyar da suka fi fama da talauchi a Nijeriya.

Sir, a cikin mazaɓun sanatoci (Senatorial Districts) 109 da ke Najeriya, santoriya ɗin Jigawa ta Arewa-maso-Yamma da Jigawa ta Arewa-Maso-Gabas suna da ga cikin sanatoriya goma (10) da suka fi kowa fama da talauci a Najeriya, wannan kaɗan kenan daga cikin yanayin da Jigawa ta ke ciki.

Duk da cewa wannan gwamnatin ta rage kuɗin takin zamani domin samun sauƙi ga manoma, wanda su ne suka fi yawa a Jihar Jigawa, amma fa Maigirma Gwamna, in har ana so a rage wannan raɗaɗi, sai an yi wa harkar noma duba na tsinaki da hankalta, domin akasarin manoman rani a Jigawa, sun dogara ne da man fetur domin yin ban ruwa, ga kuma halin da a ke ciki.

Tafiye-Tafiye Da Hawa Mota

Bayan yin dogon nazari, akasarin masu yin tafiye tafiye a hanyar mota musamman na dogon zango, ma’aikata ne da ƴan kasuwa, wanda su ma’aikata sukan yi tafiya ne da ga manyan biranen Jigawa, zuwa akasari Babban Birnin Jiha (Dutse). Ƴan kasuwa sukan yi tafiya ne, akasari da ga manyan Biranen Jigawa zuwa garin Kano domin yin sayayya da kasuwanci.

Zai yi kyau in har Jihar Jigawa zata rayo da tsohon tsarinta na sufuri kamar Jigawa Line ko wani abu makamancinsa, ta hanyar samar da dogayen motoci irin na zamani, masu amfanin da gas, don sanya su a wuraren da su ka dace, misali daga Dutse – Kazaure, Dutse – Hadejia, Dutse – Gumel, Babura da de sauran su, sannan a sanya mota daga waɗannan birane zuwa garin Kano.

In har aka samar da motocin cikin sauki, da kyakkyawan tsari na amana, tabbas zai rage raɗaɗin tsadar mota ga ɗinbin ƙananan ƴan kasuwa da ƙananan ma’aikata.

Ma’aikatan Jiha, Ƙananan Hukumomi Da Ƴan Fansho

Waɗannan suna da ga cikin mutanen da wannan yanayi ya jefa cikin ƙangin talauchi, domin abin da suke samu na albashi a yau, ba zai iya biyan buƙatarsu ta yau da kullum ba ga su da iyalansu, sannan su samu a sauƙe nauyin aikin gwamnatin da aka ɗora musu.

Sir musamman ma ƙananan ma’aikata da malaman makaranta, ma’aikatan asibitocinmu da zasu yi tafiya mai nisa kafin su isa wurin aiki.

Maigirma, Gwamna, ya kamata bayan biyan su haƙƙoƙinsu da wataƙila ba a biya ba, irin su promotion, ya kamata gwamnatin jiha ta yi tsarin ba su bashin da zasu biya a dogon lokaci domin su samu su fita daga cikin wannan ƙarnin.

Ƴan Fansho

Ya kamata a duk tsarin da gwamnati zata yi wajen tallafawa ma’aikata, ta tuna da dattijan ƴan fansho domin sun ma fi shiga yanayin wahala a irin wannan lokacin, domin shi fansho ba a ƙara shi kamar yadda ake ƙarawa masu albashi.

Waɗannan mutane suna buƙatar duk wani tallafi da za a bada, a ba musu kulawa ta mussamman.

alhajilallah@gmail.com