Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Comrade Basirka Ya Musanta Samar Da Sabbin Shugabannin Haɗakar Ƙungiyoyin Jigawa

Shugaban Haɗakar Ƙungiyoyin Ci Gaban Al’umma ta Jigawa, Comrade Muhammad Musbahu Basirka ya musanta labarin da ke nuni da cewa, haɗakar ta sake zaɓar sabbin shugabanni, inda ya bayyana lamarin a matsayin wanda bai san da shi ba.

Basirka ya bayyana hakan ne a wata takarda da ya aikowa jaridar TASKAR YANCI a yau Laraba, yana bayyana cewa waɗanda sukai wancan yunƙuri mutane ne alamar tambaya a halayyarsu, fusatattun ƴan siyasa da ma’aikatan gwamnati waɗanda suke neman suna da ƙoƙarin ɗaukar fansa da sunan ƙungiyoyin ci gaban al’umma.

TASKAR YANCI dai ta rawaito cewa, Haɗakar Kungiyoyin Ci Gaban Al’umma ta Jigawa, NETJIC, ta ƙaddamar da sabbin shugabanninta waɗanda zasu jagorance ta wajen bayar da gudunmawar mutane a gwamnati da kuma yin buɗaɗɗiyar gwamnati a Jigawa.

Labari Mai Alaƙa: Haɗakar Kungiyoyin Ci Gaban Al’umma Ta Jigawa Ta Zabi Sabbin Shugabanni

NETJIC ta sami gudanar da zaɓen shugabannin ne a zaman da tai jiya Talata a Dutse, babban birnin Jihar Jigawa inda ta zaɓi Kwamared Mustapha Umar a matsayin shugaban haɗakar da kuma Farfesa Usman Haruna a matsayin Sakatare.

Sauran Shugabannin sune, Wada’u Muhd Jahun a matsayin Sakataren Kuɗi, sai kuma Ibrahim Isyaku a matsayin Mai Kula da Harkokin Sadarwa na Haɗakar da kuma Barrister Musa Abubakar Aliyu da Barrister Aisha Suleiman Jahun a matsayin Masu Bayar da Shawara kan Harkokin Shari’a na Haɗakar.

Haka kuma NETJIC ta bayyana sunaye wasu mutane sha tara a matsayin waɗanda zasu kula da muhimman ɓangarorin ci gaban al’umma na Jigawa, cikinsu kuwa har da Comrade Muhammad Musbahu Basirka a matsayin jami’in da zai jagoranci yaƙi da cin hanci da rashawa na haɗakar.

To sai dai kuma Basirka ya bayyana cewa shi ba a zaɓe shi ba kuma bai yarda da wannan naɗi ba domin abu ne da ba shi da tushe balle makama.

Basirka ya yi kira ga al’umma da kuma gwamnati da su yi watsi da haɗakar da abubuwan da faɗa, domin kuwa a cewarsa haɗakar ƙungiyoyi ɗaya ce a Jigawa wadda shi yake jagoranta.