Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

DA ƊUMI-ƊUMI: Ƴan Ta’adda Sun Yi Garkuwa Da Ɗalibai Mata Na Jami’ar Dutsin-Ma

Wasu da ake zargin ƴan ta’adda ne sun kai mamaya tare da yin garkuwa da ɗalibai mata biyar na Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutsin-Ma a Jihar Katsina.

Wata ƴar’uawar ɗaya daga cikin ƴanmatan da lamarin ya rutsa da su mai suna Fatima Muhammad ƴar garin Lafiagi a Jihar Kwara, ta tabbatarwa da SaharaRepoters faruwar lamarin a safiyar yau Laraba.

Ta bayyana cewar, ƴan ta’addar da sanyin safiyar yau, sun kai mamaya wajen kwanan ɗalaibai mata na haya da ke kusa da makarantar Maryama Ajiri a Dutsin-Ma, inda suka tafi ɗalibai matan da ba su gaza biyar ba da ke zama a wannan yanki.

KARANTA WANNAN: Kano Ta Ɓullo Da Tsarin Bai Wa Ɗalibai Mata Tukuicin Naira 20,000 Don Bunƙasa Shigarsu Makarantu

SaharaReporters ta kuma gano cewar, uku daga cikin waɗanda aka yi garkuwar da su, sun fito ne daga Jihar Kwara, yayin da ɗaya ta fito daga Jihar Kano da kuma ɗaya ƴar Jihar Niger.

An bayyana ɗaliban da suka fito daga Jihar Kwara da suna Fatima Muhammad, Fatima Bello Zara da Rahmatullahi Adamu.

Ba a bayyana sunan sauran ƴanmata biyun da suka fito daga jihohin Kano da Niger ba a lokacin haɗa wannan rahoton.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki 12 bayan ƴan ta’adda sun kama gomman ɗalibai mata na Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Gusau a Jihar Zamfara da ke maƙwabtaka da Jihar Katsina.