Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta yi watsi da hukuncin da ya bai wa Musa Ilyasu Kwankwaso na Jam’iyyar All Progressives Congress, APC, nasara a zaɓen Ɗan Majalissar Tarayya mai Wakiltar Mazaɓar Kura/Madobi/Garun Malam tare da tabbatar da Yusuf Umar Datti a matsayin wanda ya ci zaɓe.
Alƙalai uku ƙarƙashin Alƙali Tunde Oyebamiji Awotoye ya karɓi ɗaukaka ƙarar da Yusuf Datti ya shigar tare da rushe hukuncin kotun sauraron ƙararraki zaɓe wadda ta ce, Datti bai shiga jam’iyyar da yai takara ba sai ranar zaɓen fidda gwani, abun da kotun ɗaukaka ƙarar ta ce babu wata kotu da ke da hurumi kan shiga jam’iyyar ɗantakara.