Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

DA ƊUMI-ƊUMI: NLC Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Matuƙar Aka Ƙara Kuɗin Mai

Ƙungiyar Ƙwadago, NLC, ta yi barazanar tsunduma yajin aikin sai-baba-ta-gani a duk faɗin Najeriya matuƙar aka ƙara kuɗin man fetur daga naira 617 da ake siyarwa a yanzu.

Ƙungiyar ta bayyana yunƙurin ƙarin da take ji ana yi a matsayin abun da ya saɓawa doka.

Shugaban NLC, Joe Ajaero ne ya sanar da matsayar ƙungiyar a yau Litinin, a wajen zaman Haɗakar Ƙungiyar Ƴan Kasuwa ta Afirka a Abuja.

KARANTA WANNAN: Tanaden-Tanaden Tinubu Na Sauƙaƙawa Ƴan Najeriya Ba Zasu Magance Komai Ba – Ƙungiyar Ƴan Kasuwa

TASKAR YANCI dai ta rawaito cewar, dillalan man fetur na ƙoƙarin ƙara farashin man daga naira 617 zuwa tsakanin naira 680 da 720 kan kowacce lita, saboda zubewar darajar naira, inda yanzu ake canjin dala ɗaya a kan naira 910 zuwa naira 950.

A baya-bayannan dai, ta janye shiga yajin aiki har sau biyu saboda samun daidaito da gwamnati kan buƙatunta da suke da alaƙa da janye tallafin man fetur da gwamnati ta yi.