Da sanyin safiyar yau Laraba, sojoji suka sanar da yin juyin mulki a ƙasa Gabon, inda suka ce, sun tunɓuke Shugaban Ƙasar Ali Bongo wanda ya ƙara lashe zaɓe a ranar Asabar da ta gabata.
Ali Bongo dai ya fara mulkin ƙasar Gabon ne a shekarar 2009 bayan rasuwar mahaifinsa, inda a Asabar ɗin da ta gabata ya ci zaɓe a karo na uku, zaɓen da ƴan adawa sukai matuƙar watsi da shi.
Kafar yaɗa labarai ta BBC ta rawaito cewar, sojojin sun bayyana a gidan talabijin na ƙasar Gabon, inda suka bayyana cewar sun ƙwace mulki.
Akwai rahotanni daga kamfanin dillancin labarai na AFP da Ruiters da ke nuni da cewar an ji harbe-harbe a babban birnin ƙasar Gabon a safiyar ta yau.
Waɗanda suka yi juyin mulkin sun kuma sanar da soke zaɓen ranar Asabar da ta gabata.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙoƙarin magance matsalar kawar da mulkin demokaraɗiyya da sojoji suka yi a Jamhuriyar Nijar.
Har kawo yanzu dai, Ƙungiyar Haɗin Kan Afirka, AU, da sauran ƙungiyoyin Afirka ba su magantu kan juyin mulkin da sojojin suka yi a Gabon ba.