Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

DA ƊUMI-ƊUMI: WAEC Ta Riƙe Sakamakon Jarabawar Jihohi 8

Ɗalibai daga jihohi takwas da West African Examinations Council, WAEC ke bin su bashi na aiyuka da dama ba za su sami damar karɓar sakamakon jarabawarsu ta shekarar 2023 ba.

WAEC ta bayyana haka ne ga manema labarai a yau Litinin a Ofishinta na Ƙasa da ke Yaba.

Hukumar ta yi ƙorafin cewa, rashin biyan kuɗaɗen aiyukan da ta yi, na jawo mata matuƙar matsala a aiyukanta na shirya jarabawa.

Da yake amsa tambayar manema labarai kan jihohin da suke bi bashi, Shugaban WAEC a Najeriya, Patrick Areghan ya ce, jihohi takwas ne su ke bi bashin, sai dai ba za su bayyana su duk ba, saboda akwai yunƙrin biya daga wasunsu.

Sai dai kuma ya bayyana Jihar Zamfara a matsayin wadda suka fi bi bashin, sannan kuma jihar ba ta shiga cikin waɗanda suka gabatar da ɗalibai domin rubuta jarabawar a bana ba.