Hukumar Shirya Jarabawa ta Afirka ta Yamma, WAEC, ta saki sakamakon jarabawar WASSCE ta ɗaliban sikandire ta shekarar 2023 a yau Litinin.
Shugaban Hukumar na Najeriya, Patrick Areghan ya ce, cikin ɗalibai miliyan 1,613,733 da suka rubuta jarabawar a bana, an riƙe sakamakon ɗalibai dubu 262,803 saboda zargin satar jarabawa.

Ya ce, an samu ci gaba wajen cin jarabawar a kan jarabawar da ta gabata, inda ɗalibai miliyan 1,361,608 waɗanda suka kai kwatankwacin kaso 84.38 cikin 100 na waɗanda suka rubuta jarabawar, sun sami credit zuwa sama a darussa biyar.
Haka kuma ya ce, ɗalibai miliyan 1,287,920 waɗanda yawansu ya kai kwatankwacin kaso 79.81 cikin 100 sun sami credit zuwa sama a darussa biyar ciki har da English da Mathematics.