Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

DA DUMI-DUMI: An Kama Mutumin Da Yai Barazanar Gayyato IPOB Lagos

An kama Eze Ndigbo na yankin Ajao Estate a Jihar Lagos, Fredrick Nwajagu.

Da yake magana a wani faifan bidiyo da ya yadu a Juma’ar nan, Nwajagu ya yi barzanar gayyato mambobin haramtacciyar kungiyar IPOB domin su kare dukiyoyin ‘yan kabilar Igbo a Jihar Lagos.

Ya ce, “IPOB, zamu gayyace su. Ba su da aikin yi. Duk ‘yan IPOB ne zasu kare mana shagunanmu. Sannan zamu biya su. Ya kamata mu tsara yin haka. Ya kamata mu yi hakan. Ya zama dole mu samu jami’an tsaronmu don su daina kai mana hari da tsakar dare, da safe, da kuma rana.

KARIN LABARI: Zamu Gayyaci IPOB Ta Zo Ta Kare Mu A Lagos – Shugabannin Igbo Na Kudu Maso Yamma

“Lokacin da suka gano cewa muna da jami’an tsaronmu kafin su zo, to dole su shirya. Ba wai ina fadin maganata ne don a boye ba. Bana boye magana ta, ina son maganar ta yadu. Dole ne Igbo su samu ‘yancinsu su kuma tsaya tsayin daka a Jihar Lagos,” in ji shi.

Wata majiya daga bangaren ‘yansanda wadda ta bukaci a sakaya sunanta, ta sanar da PUNCH cewar, jami’an ‘yansanda da na DSS sun kama shugaban na Igbo a safiyar yau Asabar.

“Tawagar ‘yansanda da DSS sun je gidansa to amma sun samu ya gudu. Daga bisani aka gano shi a wani otel da ke Ejigbo inda aka kama shi a can,” in ji majiyar.