Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

DA DUMI-DUMI: Tinubu Ya Sanya Hannu Kan Dokar Baiwa Dalibai Bashi

Shugaban Kasa Bola Tinubu ya sanya hannu a kan kudirin dokar baiwa dalibai bashi wanda hakan ya tabbatar da tsarin a matsayin doka.

Mai temakawa shugaban kasa, Dele Alake ne ya bayyana haka ga ‘yan jaridun Fadar Shugaban Kasa a yau Litinin da yamma.

Wannan doka dai zata baiwa dalibai ‘yan Najeriya damar cin bashin da bai da kudin ruwa domin gudanar da karatuttukansu.

Dokar dai ta yi nuni da cewa duk dalibin da ya gaza biyan bashin da ya ci bayan cikar wa’adin biyan za a ci tararsa ta naira 500,000 ko daurin shekara biyu ko kuma gaba daya.

Kudirin dokar da Shugaban Majalissar Wakilai mai barin gado, Femi Gbajabiamila ya gabatar a majalissar ya samu tsallake karatu na biyu ne a ranar 25 ga watan Mayu, 2023 a Majalissar Wakilai.