Tsagin jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, ƙarƙashin shugabancin Major Agbo ta kori ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen da ya gabata, Sanata Rabiu Kwankwaso saboda zargin aikata zagon ƙasa ga jam’iyyar da kuma badaƙalar kuɗaɗen kamfe na jam’iyyar.
Korar ta Kwankwaso dai ta bayyana ne a sanarwar da Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na NNPP, Abdulsalam Abdulrasaq ya saki yau a Abuja.
Wannan dai na zuwa ne kwanaki uku bayan shugabannin tsagin Agbo sun bayyana cewar za su binciki tsohon gwamnan Kanon da wasu makusantansa kan zargin badaƙala da kuɗin da ya haura naira biliyan ɗaya waɗanda aka tara yayin sayar da famafaman takara.
KARANTA WANNAN: NNPP Za Ta Binciki Kwankwaso Kan Zargin Badaƙalar Sama Da Naira Miliyan Dubu Na Jam’iyya
Abdulrasaq ya bayyana cewar, hukuncin korar Kwankwaso ba da ɓata lokaci ba ya faru ne bayan ya ƙi bayyana gaban kwamitin ladabtarwa domin ya kare kansa kan zargin da ake yi masa.
Ya ce, an bai wa Kwankwaso kwanaki biyar ne ya gurfana a gaban kwamitin amma ya gaza aiwatar da hakan.
Mai magana da yawun jam’iyyar ya ce, korar Kwankwason ta zo daidai da tanade-tanaden da ke kundin tsarin mulkin jam’iyyar wanda aka sabunta a shekarar 2022.
Da yake mayar da martani kan korar da aka yi wa Kwankwaso, Mai Binciken Kuɗi na Ƙasa na Jam’iyyar, Ladipo Johnson ya yi watsi da batun, inda ya ce, tsagin Agbo ba su da ƙarfin iya korar tsohon gwamna Kwankwaso.