Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Kafa Sabbin Jami’o’i Da Kwalejoji Na Shekaru Bakwai

Gwamnatin Tarayya ta sanar da dakatar da kafa sabbin jami’o’i, kwalejoji, da polytechnics na tsawon shekaru bakwai domin magance raguwar inganci da rashin kayan more rayuwa a ɓangaren ilimin manyan makarantu.

Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa ne ya bayyana hakan ga ƴan jarida a fadar shugaban ƙasa, inda ya ce wa’adin din zai taimaka wajen dakatar da sauye-sauye da ɓarnar kayan aiki, yayin da za a mayar da hankali wajen inganta cibiyoyin da ake da su a ƙasa.

Alausa ya ce matsalar shiga jami’a ba ta da wahala, amma yawan sabbin jami’o’in na haifar da raguwar ingancin digiri.

Ya ƙara da cewa, rashin ɗaukar mataki nan take zai ƙara yawan matasa marasa aikin yi saboda rashin ƙwarewa.

Ya bayyana misalin jami’a ɗaya da ke da ƙasa da ɗalibai 800 amma da ma’aikata 1,200 domin nuna rashin tsari da ɓata lokaci.

Ministan ya ce yanke wannan hukunci zai bai wa gwamnati damar gyara kayan aiki, da ɗaukar ma’aikata, da ƙara yawan ƙarfin cibiyoyin da ake da su.

Ya kuma bayyana cewa wasu jami’o’in tarayya a arewa na da ƙasa da ɗalibai 2,000.

Haka zalika, FEC ta amince da kafa jami’o’i masu zaman kansu guda tara da suka cika ka’idojin NUC.

Alausa ya ƙara da cewa nan gaba za a yi amfani da irin wannan matakin wajen dakatar da kafa wasu jami’o’i masu zaman kansu, polytechnic da kwalejoji domin tabbatar da inganci ba a wofantar da shi ba.