Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

DA ƊUMI-ƊUMI: Sanata Natasha Ta Kutsa Cikin Zauren Majalisa Duk Da Yunƙurin Hanata Shiga

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta samu damar shiga harabar Majalisar Dattawa a Abuja bayan da tun farko aka hana ta shiga, duk da hukuncin kotu da ya buƙaci a dawo da ita.

Sanatar, wadda ke cikin dakatarwa na tsawon watanni shida daga majalisar, ta nace cewa za ta koma zauren majalisa bisa hukuncin kotu.

Lokacin da ta isa harabar majalisar, an dakatar da motarta daga shiga, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce daga mabiyanta.

Motar gabanta ma wadda ke ɗauke da ƴar gwagwarmaya Aisha Yesufu, ita ma an hana ta shiga.

Duk da haka, Natasha ta fito daga motarta kuma ta shiga harabar majalisar a ƙafa, tare da rakiyar wasu magoya bayanta.

WANI LABARIN: Jihohi 16 Da Suka Ƙi Aiwatar Da Dokar Ƙarin Shekarun Ritaya Ga Malaman Makaranta

Wannan mataki ya janyo hankalin jama’a da dama da ke ganin cewa majalisar ta yi watsi da doka da oda wadda kotu ta bayar.

Babu wata sanarwa daga shugabannin majalisar dangane da matakin hana ta shiga duk da umarnin kotun.

Ana gani Sanata Natasha dai a matsayin ɗaya daga cikin ƴan siyasar da ke fafutuka da kare haƙƙin mata da ƴan ƙasa.

Masana harkokin siyasa sun ce lamarin zai iya zama wata jarrabawa ga ikon doka a Najeriya.