Daga: Kabiru Zubairu Birnin Kudu
Tattalin arziƙi da mallakar dukiya a duniya na fuskantar matsaloli a ƴan shekarun nan saboda lalacewar tattalin arziƙin duniya. Masu arziƙi da dama sun yi asara, wasu ma sun karye. Mallakar dukiya a yanzu na rarrabuwa sosai saboda saboda mutuwa, hakan ta sa ba a cika samun damar gadar da ita a dunƙule ga ƴaƴa da jikoki ba. Haka su ma magadan ba su cika haɗa kai domin bunƙasa dukiyar da aka bar musu sai ƴan ƙalilan daga ciki.
Akwai mutanen da suka sami nasarar dasa ginshiƙin dukiya a danginsu bayan sun samu nasarar kasuwancin da suke yi. Irin waɗannan mutane sun mayar da danginsu, ƴaƴa, jikoki da tattaɓa kunne masu arziƙin da babu irinsu a duniya. A cikin wannan rubutu na tsakuro dangin goma da suka fi kowa arziƙin kuɗi a duniya domin nazarin mai karatu.
Dangin Walton

Tun a shekarar 1962 ne Sam da Bud Walton suka ƙirƙiri kasuwancinsu mai suna Walmart a Rogers da ke Arkansas ta Amurka, suka kuma sami nasarar zama masu saye da siyarwa mafiya ciniki a duniya. A yanzu haka Walmart ne ke gan gaba wajen hada-hadar siye da siyarwa duniya wajen samun kuɗaɗe.
A yanzu haka adadin kuɗin da Dangin Walton suka mallaka ya kai dalar Amurka biliyan 238.2 kwatankwacin naira tiriliyan 190.5 kuma sune dangi mafiya kuɗi a duniya.
Dangin Mars
Kamfanonin Milky Way, Twix, M&M’s, Snickers da Mars Bars kaɗan ne daga cikin kamfanonin da ke ƙarƙashin Mars Inc., sunan da ya samo asali daga dangin waɗanda tarin dukiyarsu ke da alaƙa da samar da sikari.
Mujallar Forbes ta bayyana cewa, ɗaiɗaikun mutane 6 na Dangin Mars waɗanda mazauna Virginia ne ta Amurka na cikin ɗaiɗaikun mutane mafiya kuɗi na duniya.
A yanzu haka, adadin yawan kuɗin da Dangin Mars suka mallaka ya kai dalar Amurka biliyan 124, kwatankwacin naira tiriliyan 99.2.
Dangin Koch

Bayan ƴan’uwansu biyu, Frederick da William sun bar kamfanin babansu, ƙannensu Charles da David Koch sun bunƙasa matatar man mahaifin nasu har ta girma sosai, wadda ake kira da Koch Industries.
A yanzu haka Dangin Koch suna mallakar dukiyar da kuɗinta ya kai dalar Amurka biliyan 124, kwatankwacin naira tiriliyan 99.2.
Dangin Dumas
Sana’ar da Dangin Dumas sukai shuhura da ita kuma sukai kuɗi da ita, ita ce samar da kayan ƙyale-ƙyale na sa wa da na kwalliyar gida. A yanzu haka yawan kudin da wannan dangin ke da shi ya kai dalar Amurka biliyan 112, kwatankwacin naira tiriliyan 89.6.
Dangin Sa’ud

Mujallar Bloomberg sun bayyana cewa, tarin arziƙin da Dangin Sa’ud suka tara na da alaƙa da kuɗaɗen da suke samu daga sarautar da suke ta Saudi Arabia wajen bayar da kwangiloli da kuma sanya hannun jarin da suka yi a arziƙin man ƙasar.
A yanzu haka an ƙiyasta yawan tarin kuɗin da Dangin Sa’ud suka mallaka da cewar ya kai dalar Amurka biliyan 100, kwatankwacin naira tiriliyan 80.