Kamfanin Dangote Petroleum Refinery ya cimma gagarumar nasara ta hanyar fitar da manyan tankokin man jirgin sama guda biyu zuwa Saudi Aramco, babbar kamfanin mai a duniya.
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ne ya bayyana hakan yayin ziyarar da tawagar Nigerian Economic Summit Group (NESG) ta kai ga kamfanonin Dangote Fertiliser da Dangote Petroleum Refinery & Petrochemicals a Ibeju Lekki, Lagos.
Dangote ya bayyana cewa an samu wannan cigaba ne saboda ingancin matatar man sa da kuma amfani da sabbin fasahohi.
“Muna cimma manyan burikan da muka sa a gaba, kuma ina mai farin cikin sanar da cewa mun sayar da tankokin man jirgin sama guda biyu ga Saudi Aramco,” in ji shi.
Tun daga fara samar da mai a shekarar 2024, matatar Dangote ta karu da karfin aiki, inda yanzu tana tace gangar danyen mai har 550,000 a kowacce rana.
Shugaban NESG, Mista Niyi Yusuf, ya jaddada cewa Najeriya tana bukatar karin manyan hannayen jari irin wannan domin cimma burin tattalin arzikin dala tiriliyan daya da ta sa a gaba.
Yusuf ya yaba da jarumtar Dangote wajen gina masana’antu da za su taimaka wajen samar da ayyukan yi, rage dogaro da shigo da kaya daga waje, da kuma bunkasa tattalin arziki.
Dangote ya kara da cewa ya zama dole gwamnati ta kare masana’antun cikin gida kamar yadda manyan kasashe ke yi domin habaka ci gaba da samar da ayyukan yi.