Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Dangote Ya Sake Rage Farashin Fetur Da Ake Sarowa Daga Matatarsa

Kamfanin Dangote Petroleum Refinery ya sanar da wani sabon sauƙe farashin sarar da fetur daga ₦840 zuwa ₦820 kan kowace lita, wanda hakan ke zama ragin ₦20 daga farashin da aka sanya mako guda da ya gabata.

Mai magana da yawun kamfanin, Tony Chiejina ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa ranar Talata, 8 ga Yuli, 2025, yana mai cewa sabon farashin ya fara aiki nan take.

Wannan matakin ya biyo bayan ragin farko da aka yi, daga ₦ 880 zuwa ₦840 a ranar 30 ga Yuni, 2025, wanda ya biyo bayan matakin sassauci da kamfanin ke ƙoƙarin samarwa ga ƴan kasuwa da masu amfani da man fetur a Najeriya.

WANI LABARIN: Ɗan Takara Daga Arewa Ne Kadai Zai Iya Kayar Da Tinubu A 2027, In Ji Wani Lauya Ɗan Kudu

A yanzu dai, kamfanoni masu dillancin fetur daga matatar, irin su MRS Oil & Gas, Ardova Plc, da Heyden da ke da yarjejeniyar musamman da Matatar Dangote na iya rage farashin sayarwa zuwa ƙasa da ₦880.

A ranar Lahadi 15 ga Yuni, kamfanin ya sanar da garaɓasar dakon fetur da dizal kyauta ga ƴan kasuwa da manyan masu amfani da waɗannan kayan a faɗin ƙasar.

Dangote ya kuma tabbatar da sayen sabbin manyan tankunan masu amfani da iskar gas (CNG) guda 4,000 da za su fara aiki daga 15 ga Agusta, 2025 domin wannan tsari.

Kamfanin ya kuma bayar da wani tsarin bashi ga masu siyan lita 500,000 zuwa sama, inda za su iya samun ƙarin lita 500,000 na fetur a matsayin bashi na makonni biyu bisa shaidar banki.

Duk da haka, wasu ƴan kasuwa da masu motocin haya sun nuna rashin jin daɗinsu, suna cewa wannan mataki zai takurawa kasuwarsu.

“Wannan tsarin na iya janyo mummunan tasiri ga masu rarraba mai da ƙananan ƴan kasuwa,” in ji wata ƙungiyar dillalan man fetur a Legas.