Naira ta sake fuskantar zubewar daraja a kasuwar musayar kudade ta hukuma a ranar Jumma’a, inda ta faɗo zuwa N1,602.18 a kan kowace dala, wanda hakan ke nuni da faɗuwar N5.49 daga yadda take a baya.
Bayanai daga shafin yanar gizo na Babban Bankin Najeriya (CBN) sun nuna cewa wannan sauyin ya faru ne bayan hutun Ma’aikata na ranar Alhamis, 1 ga Mayu, wanda ya kawo tsaiko a kasuwanci na kwana ɗaya.
Wannan koma bayan darajar Naira ya kai kashi 0.34 cikin 100 idan aka kwatanta da N1,596.69 da aka rufe kasuwar a ranar Laraba, 30 ga Afrilu.
KARANTA WANNAN: RIKICIN SARAUTA: Sarki Sunusi Da Sarki Aminu Sun Naɗa Galidiman Kano Daban-Daban
A makon da ya gabata, Naira ta yi ƙarko na wasu kwanaki uku, inda ta kasance a tsakanin N1,599.95, N1,599.71 da kuma N1,596.69 a ranakun Litinin zuwa Laraba.
Duk da haka, ta buɗe makon da samun asara kaɗan ta kashi 0.02 cikin 100, alamar cewar matsin tattalin arziƙi da hauhawar farashin kaya na ci gaba da shafar darajar kuɗin ƙasar.
Wannan ci gaba na ƙara tayar da hankalin ƴan kasuwa da masu zuba jari da ke jiran ingantaccen sauyin manufofin kuɗi daga CBN.
Yayin da kasuwar dala ke ci gaba da fuskantar ƙalubale, masana tattalin arziki na ganin cewa akwai buƙatar gwamnatin tarayya ta ɗauki matakan gaggawa don daƙile taɓarɓarewar da Naira ke yi.