Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Dole Ne Sai Ɗalibi Ya Kai Shekaru 12 Kafin Ya Shiga Ƙaramar Sikandire A Najeriya

Ma’aikatar Ilimi ta Tarayyar Najeriya ta ƙaddamar da sabon tsarin da ya ƙayyade shekarun shiga makarantar Sikandire (JSS1) a makarantu masu zaman kansu zuwa 12 bayan kammala Firamare.

Wannan na cikin sabon tsarin makarantu masu zaman kansu da aka fitar, waɗanda suka haɗa da na addini, da na ƙungiyoyi da na kamfanoni masu zaman kansu.

Ma’aikatar ta bayyana cewa “kowane yaro zai fara Nursery yana da shekaru 3 sannan ya ci gaba da Pre-Primary a shekara ta 5,” kamar yadda NPE 2013 ta tanada.

WANI LABARIN: Ƴan Sanda Sun Cafke Wanda Ya Kashe Tsohuwar Matarsa Da Ɗan Fashi A Jigawa

Za a fara makarantar Firamare da shekaru 6 sannan a kammala cikin shekaru 6 kafin a shiga Sikandire a shekara 12.

Wannan dai na nufin ɗaliban za su kai kimanin shekaru 18 kafin su kai matakin shiga manyan makarantu ko jami’a.

A baya an samu saɓani tsakanin tsohon Minista Prof Tahir Mamman da sabon Minista Dr Tunji Alausa kan ƙayyade shekarun shiga jami’a tsakanin 18 ko 16.

Rahoton Nigeria Education Digest 2022 ya nuna cewa makarantu masu zaman kansu sun ƙaru a Najeriya da kashi 35.06% tsakanin 2017 da 2022 a matakin Sikandire, yayin da na gwamnati suka ƙaru da kashi 6.8% kacal.